Babi Na Ashirin Da Uku

2.1K 198 316
                                    

Hindu ta kasance cikin jin dadin da ba ta san za ta same shi ban a tsawon lokaci. Ta fada soyayyar wanda ya fito karara ya bayyana mata kaunar sag are ta.

Rayuwar da ta juya ma ta baya ta dawo ma ta sabuwa fil. Wurin da ta rasa na iyaye, ta samu wajen su Hajiya Lauratu, sannan ga su Baba Lanti da Gwaggo. Kannen ta kuwa sun kasance cikin cikakken kulawa a wajen Alhaji Maigari. Me ya fi wannan dadi?

Sai dai duk da hakan ta gagara sakewa, musamman da Malik. Gani take yi idan ta yi hakan komai zai iya subucewa, ta koma gidan jiya. Abu ne da take ganin idan farin ciki ya ma ta yawa, to wani abu zai sa hannu ya kwace mata.

Farko iyayen ta, wadan da suka kasance duniyar ta a lokacin suna raye. Tashi guda su ka mace su ka bar ta cikin kunci da kadaici. Na biyu Baba Alhaji ya kara matsawa kusa da rayuwar ta, ya miye ma ta gurbin su Abba, shi ma kuma ga yadda ya kasance. Sai kuma Sadiq, wanda ya hadu da mummunar hatsari, sai Gwaggo….

Ko dan zaman da ta yi da su Auwal sai da ya kai ga rabuwa da abubuwan sa ma su muhimmanci saboda su. Ta nisa, a’a, bai dace ta ci gaba da yaudarar kanta ba. Ba ta san yadda za ta bayyana ba, amma ta san ba za ta bari wani abu ya samu Malik ko iyalin gidan sa ba.

A hankali ta ji an rungumo ta ta baya, kan sa a kan ta yana shaker kamshin gashin ta lokacin da take tsaye jikin wadurof din dakin, ta na kokarin fidda kayan da za ta saka don zuwa wajen Gwaggo. A ranar ne suke shirin tafiya Abuja dukan su tare da Baba Lanti. Duk jikin ta ya dauki zogi, ya fara yamutsin jin dadi a yayin da karar bugun zuciyar ta ke cike ma ta kunne.

“Auren mu rubutaccen ala’amari ne daga Allah, tun ran gini ran zane.”
Kalaman san a daren jiya suka rika kararrawa cikin kunnuwan ta. A jiyan tun daga hanyar komawar su daga gidan gona ta yanke shawarar kaucewa hanyar sa, don haka sai da ta bari daidai lokacin barci tukunna ta koma dakin.

A tunanin ta, za ta tarar ya yi barci, ko kuma ma, zuwa kawai za ta yi ta fada kan kujerar ta tare da juya bayan ta ta yadda ba zai iya yi ma ta magana ba. idan ta yi sa’a ma, ba zai lura da it aba musamman idan ya na danne-dannen komfutar sa.

Sai dai da komawar ta dakin ta tarar ya na jiran ta, sannan ko da ta lura babu kujera ko daya a dakin, zuciyar ta ta shiga rudani. Nan ta kalli wurin da yake, suka hada idanu, ya taso ya nufo ta. Kowane takun sa daya ya na kara wa zuciyar ta bugu da tsalle, sannan idanuwan sa sun rike na ta.

A gaban ta ya tsaya, daga shi sai dogon wando da singilet, numfashin sa da nata suka gewaye su hade da kamshin da dukan su ke yi. Ba ta iya fahimtar komai sai zogi da radadin da zuciyar ta ke yi a lokaci guda, a yayin da numfashin ta yayi barazanar daukewa. A lokacin ne yayi abin da bata yi tsammani ba.

Ya ja ta zuwa jikin sa a hankali, sannan ya dauke ta zuwa duniyar da ba ta san da it aba balle dadin ta. Da farko, ta shiga kaduwa sannan rudani. Sunan ta kawai ta ji ya furta, sauran bayani kuma ba ta fahimci komai ba. Sumbartarta yake yi kamar ba gobe, ya na aika mata sakon da kwanyar ta ba ta iya fahimta, sai zuciyar ta.

A lokacin ta narke kamar kankarar da a ka dora bisa wuta, ta yi ninkaya ta nitse cikin kogin kaunar sa. Ba za ta iya fassara yadda ta jib a a lokacin, kawai mayar ma sa da martanin sumbar ta samu kan ta ta ke yi.

Har sai da ta ji ya sake bude bakin say a furta ma ta kalaman da ba ta taba jin sun kwanta ma ta a rai ba sai a lokacin. “Ina kaunar ki Hindu….”

Duniyar ta ta tsaya cik, ba ta iya jin komai sai karar bugun zuciyar sa, wanda ke tafiya tare da na ta, da kuma yadda hannayen sa ke gewaye da ita gaba daya, ta zama wata kankanuwa a cikin babban jikin sa gaba daya.

Za ta iya sabawa da hakan, za ta iya kasancewa cikin wannan yanayi tsawon rayuwar ta ba tare da ta gaji ba. Ashe haka so ya ke dama? Haka ya ke dagargaza zuciyar mai yin sa, ya yi majajjawa da mai shi cikin duniyar gajimare ya na shawagi da shi cikin nishadi da annashuwa?

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now