Babi Na Ashirin

2.1K 189 134
                                    

Alhaji Bilya ya dade a ofishin sa, ya na nazarin abubuwa. A ranar ya hana kowa shiga wajen sa, domin ba ya jin son ganin kowa. Ya ja kwalin sigarin sa ya zare kara na tara a wannan safiya sannan ya kunna ya na zuka tare da fitar da hayakin ta hanci da baki.

A lokacin Hindu ta cika sati shida ke nan a gidan Malik, yanzu ne ya kamata ya motsa don cika burin sa. Da ma ya bari ta zauna tsawon lokaci a gidan ne ba tare da ya yi motsi ba saboda ta saba da mutanen gidan gaba daya, ta kuma ta sake das u sosai ta yadda za ta san tattari duk wani sirrin gidan gaba daya.

Tsoron sa daya; Allah Ya sa Hindu ba ta amince ta bar Malik ya taba ta ba,don ya san Malik wajen narkar da zukatan ‘yan mata.

A yadda abubuwa su ke tafiya, komai dai-dai ne da yadda ya tsara ya kuma shirya. Yanzu saura mataki na karshe da zai dauka a kan kudirin sa game da Malik.

Ya yi murmushi a lokacin da ya karkade tokar tabar sa, ya sake zukar hayakin ya busa. Ya riga ya gama da Malik, domin ya na da makamai biyu a hannun sa ma su zafi. Daya Hindu ce, dayar kuma a hankali zai bayyana. Malik ba zai san abin da ya same shi ba sai ya gan shi a kasa. A wannan lokaci ne shi kuma zai yi murnar nasarar sa.

Ya fadada murmushin sa tare da jujuyawa a kan kujerar sa ta alfarma, wacce ke gaban makeken teburin da ke ofishin sa. Kwarai, Malik ya gama yawo.

Ya ja kan wayar tarho din sa, wata farar takardar da ke shimfide a kasar sa ke tunasar da shi cewar ya kamata ya biya kudin wayar na watan da ya wuce. In bah aka ba kuwa za a iya katse ma sa layin a kowane lokaci.

Ba zai yi karya ba, a ‘yan watannin nan abubuwa bas a uwa ma sa da sauki. Ya bugar da kadarorin san a karshe ne don ya samu kudin da y aba wa Hindu. A yanzu ba ya da komai sai gidan da yake cikin ta, da motar da yake hawa.

Cefanen gidan sa ma Allah Ya sa matar sa mutuniyar arziki ce, ta sayar da gwalagwalen ta ta saya mu su hatsi. Ya kuma yi alkawarin sai ya mayar mata duk abin da ta rasa, da ninkin irin sa goma.

Hakika, lokaci kara kurewa yak e yi, don haka ya latsa lamba a wayar sannan ya jira. Lokacin da ya ji wayar ta amsa a daya bangaren,sai ya yi sauri ya kashe tabar. Bayan bugawa sau uku, sai ya ji an dauka.

“Assalamu Alaikum”.

“Wa alaikumus-s-salaam.” A lokacin da ya gane muryar da ta kwararo daga daya bangaren.

                 *                                    *                                           *                                        

Tun da wayewar gari Hindu ta tashi da tsananin zazzabi mai hade da ciwon kai. Ba ta ko iya tashi daga wajen da take kwance. Da kyar ta iya tashi ta yi sallar subh, bayan nan kuma sai karkarwa ta rika yi cikin jin sanyi.

Ba ta san lokacin da a ka kashe iyakwandishan din dakin ba, sai muryar Malik ta ji a gefen ta, ya na tambayar ta ko lafiya. Gyada kai kawai ta iya yi ma sa, amma lebban ta karawa su ke da juna tsabar jin sanyi.

Ji ta yi ya daga ta, dumin jikin sa ya lullube nata, zuciyar ta na bugu a cikin kunnuwan ta. Ko zuciyar ta ce?

Don ji ta yi kan ta na juyawa a lokacin da hannayen ta suka nemi madafa a saman wuyan sa. ta yi hakan ne don kar ta fadi, ta raya wa kan ta. Amma abin da ya razana ta, shi ne yin hakan da ta yi kamar wacce ta saba yin sa kullum.

Kan gadon barcin sa ya ajiye sannan ya lullube ta da bargon sa. ta lumshe idanun ta, don ba ta kaunar dadin dumin da ya mamaye ta a lokacin, ko ma na kamshin turaren sa. Ta na iya jin lokacin da ya ke latsa lambobi jikin tarho din dakin. Kan ta ya 

Misalin karfe tara da rabi na safe ne Dokta Zainab ta isa sannan ta duba ta. Dokta ta dan yi tambaoyin ta sannan ta rubuta wasu magungunan da za a saya don su taimaka mata wajen saukar da zazzabin.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now