Babi Na Talatin Da Biyu

1.7K 177 66
                                    

* * * * *
Ibrahim ya yi wata sassanyar sallama sannan ya shiga Ofishin Malik. Shi kuwa ya na zaune ne a makekiyar kujerar sa ta alfarma, ya na jujjuya ta a yayin da kwakwalwar sa ke juyawa tamkar kujerar. Kusan ya na zaune ne cikin duhu, sai da Ibrahim ya saka hannu ya kunna wuta tukunna wuri ya dau haske. Agogon bango ya buga tare da na hannun Malik, karfe goma sha daya na dare dai-dai.

Ibrahim ya yi kyakyawar nisawa da ya ga halin da dan uwan sa ke ciki. Zuciyar sa ta sosu ainun. Ya nufi wurin da ya ke zaune, yatsun sa suna sarkafe da juna, ya dora su bisa cikin sa, kan sa ya na kallon silin din dakin. Ya san tunanin sa bai wuce kan abu daya, wato Hindu!

“Malik….Malik…ka zo mu je gida. Hajiya ta damu da rashin ganin ka.”

Malik ya dago ya dubi Ibrahim. Idanun sa cike da kunci. A yau sati biyu ke nan da batar Hindu, gaba daya ya fita daga kamannin sa, ya dawo tamkar wani marar lafiya. 

Ya warware yatsun sa, ya mayar da hannayen sa gefen sa, su na lilo, ya ce,”Gida? Me zan je na yi a gidan Ibrahim? Me zan je na yi bayan ba bu Hindu?” Sai kawai idanun sa su ka yi rau-rau, suka cike kwalla.

Ibrahim ya kara tausaya masa,amma kuma har yaushe zai ci gaba da zama haka? Ya matsa dab da shi, ya sauke muryar sa cikin tausayawa, “Na san ka shiga cikin wani mawuyacin hali a yanzu, amma kar ka mance da nauyin da ya rataya a wuyan ka. Kar ka mance da cewa mutane da dama su na bakin cikin ganin ka a irin wannan hali. Shin kai ba ka damu da irin yadda su ke ji ba ne?”

Malik ya zauna da kyau, ya na iya fuskantar sa sosai, “Ban san yadda su ke ji ba Ibrahim. Na dai san ba zan iya rayuwa ba bu Hindu ba.” Ya na fadin haka ya sa hannu ya dauko wani abin ajiye hoto mai dauke da hoton Hindun, wanda a ka dauka lokacin auren su da shi.

Ba ya cikin hoton, amma albom guda a ka yi a ka adana saboda tarihi. Ya kalli hoton sannan ya rungume a kirjin sa tare da lumshe idanun sa, hawaye na zuba.

Ibrahim ya matse kwallar da ke neman fita daga nasa idanun. Ya ce, “Me za mu iya yi ne fiye da wanda mu ka yi? Mun yi cikiyar har mun gaji. Mun kai rahoto ofishin ‘yan sanda, mun bayar da sanarwa a gidan  rediyo, sannan mun hada da rokon Allah. Me ka ke son kuma mu yi?”

Irin kallon ta Malik ke ma san a rashin fahimtar kalaman say a sa shi jin kamar ya ja shi ya jijjiga shi har sai sun nutse cikin kan sa tukunna. Amma ya san hakan ba zai yi tasiri ba a lokacin. Ya yanke shawarar ci gaba da lallaba shi, kamar yadda ya rika yi tsawon sati biyu.

“Malik, don Allah, ka daure mu jira lokacin da Allah zai karkato mana da hankalin ta zuwa nan. Amma kafin nan mu na bukatar zama da karfin mu, cikin koshin lafiya. Wannan hanya da ka dauko Malik ba alheri ba ne. Ka kauracewa abinci, sai an tilasta ma ka kafin ka ci. Ba ka barci sai ya zama dole, aiki ya gagare ka yi….shin ya ya ka ke zaton mu na kusa da kai za mu ji? Ita Gwoggo idan ta na ganin ka a irin wannan halin, ya ya za ta ji?”

Malik ya hadiye yawu da kyar, daci ya cike makogwaron sa. “Ji za ta yi ta bani amana, amma na gaza rikewa.” Wata iska mai zafi tayi barazanar shake shi. ya tsinci kan sa cikin tari mai tsanani, kirjin say a shiga zafi da kuna. Ya kasa bambance ciwon zuciya ce ta kawo hakan, ko kuma radadin rashin Hindu ne.

“Don Allah Malik ka bar yi wa kan ka haka. Babu wanda zai baka laifi don saboda kun samu sabani kai da matar ka. Ina ne ka taba jin ba a fada tsakanin miji da mata?” Ka yi hakuri, ka saka dauriya a cikin wannan al’amari. Akwai wadanda zukatan su za su raunana ainun idan ka ci gaba da kasancewa cikin hali irin haka.” Ya dan dafa kafadar sa, ya dora da, “Please, be courageous, be strong.”

Malik ya nisa sannan ya goge fuskar sa. Ya ja hoton Hindu ya kura ma ta idanu. Ya sake nisawa, ya ce, “Ibrahim na yi kokarin ganin na daure, amma abin ya gagare ni.” Kamar yadda dariya ya gagari kare.

..... Tun Ran Zane Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu