🌟。*。💗~ xXx
。💚。* 。🌟
🌟 _*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟_GODIA_
DOKKAN GODIA DA YABO SUN TABBASA GA ALLLAH MADAUKA KIN SARKI ME SAMA DA KASA WANDA YA KAGI KOMAIWANNAN LBR KIRKIRA NE BANYISHI DANCIN ZARAFIN KOWABA, NAYINE DAN NISHADANTAR DA MAKARANTA, INA ROKAN ALLAH YABANI IKON FARAWA TARE DA KAMMALAWA LFY...ASHA KARATU LFY
*HASKE WRITERS ASSO..* 💡
_*Story and written by*_
_*Asy khaleel....✍*__The Whole Book is Dedicated to_
_*Jiddah Ja'o*
_Book din tukwici ne gareki *Baby Afreen*
بسم الله الرحمن الرجيم1⃣
Ah ah wayyo Allah na cikina, Jiddah ce ke wannan maganar yayinda take chunkushe a cikin bayi se uban nishi take ba kaukautawa, Jiddah lafiyar ki kuwa irin wannan nishi haka kamar wadda take nakuda, Cikin hassala goggo ke wannan maganr, yarinya se uban ciye ciye komai kika gani se kinkai cikinki, oh ni Hamsatu yaxanyi da wagga yarinya? "wayyo Goggo ki taimakamin"
Wangale baki goggo tayi Tace " Au! Ji jairar yarinya ,tsabar iskanci ni Zan taimaka miki kiyi ba haya? Wannan yarinya yaushe zakiyi hankali ne ? Wlhy Albasa batayi halin ruwa ba, sokon ci sekace y'ar fari?"
A hankali Jiddah ta bud'e kyauren bayin ta fito a sunkuye rik'e da cikin ta , ba tare da ta kalli inda goggo ke tsaye ba tayi wurgi da butar ta koma cikin band'akin da gudu ,goggo ta rik'e hab'a 🤔baki duk goro tace " Allah ya shirya ! Yanzu Jiddah butar kuma da kika wurgar wa zai d'auko miki?"Daga cikin bayin tace " Ai ba se ki d'auko ba goggo ni Zan d'auko kayana " kai kawai goggo ta girgiza tace hakan zaki tashi da kazantar?" Ita dai Jddodo ko a jikin ta se tafka uban nishi take goggo dake hura wuta tace " Nidai kiyi ki fito ki zagaya wajen Malam labaran mai kayan Miya ki siyo min kabewa da yakuwa kar dare yayi" tana rufe baki Jiddah ta fito tana Sosa kai kamar me kwarkwata ta d'au butar zata wajen Randa , da sauri goggo ta taso ta wafce butar " Bani nan! Wannan wani sabon Kazanta ne ? Ja baya ni in d'eba miki ruwan ,yarinya se rigimar tsiya ? "
Ita dai bata ce komai ba se washe hak'ora take tana Sosa kai 'kafar nan fursu fursu 😃 ko takalmi babu ,goggo ta mik'a Mata butar ta juya da tsallen ta takoma cikin bayin ,nan ma saida taci wasanta kafin ta fito .
A tsakar gidan ta iske goggo dake tsaye hannu a kunkumi tace " Laaah!! Yanzu dambe zakiyi goggo?" Uwaki Zan yi! Nace Uwaki Zan yi ,tsarkin ne har ya d'auke ki dogon lokaci? Ungo amshi kud'in nan ki siyo kabewa na ashirin da yakuwa na talatin idan kin je kuma ki zauna se kinga damar dawowa , in kinga dama ki tafi wasan ki har dare Yayi!"Washe hak'ora Jiddodo tayi tace " Toh goggo nagode! " ta fice da gudu goggo ta girgiza kai tace " Ko me dalilin godiyar nata oho ? Ta juya taci gaba da iza wuta tana ta surutai.................. _*READ MORE*_
_*ASY KHALEEL TA KOWA*_

ESTÁS LEYENDO
KURUCIYAR JIDDAH
Historia CortaLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.