1. JIDDA

4.9K 292 33
                                    

KUSKUREN IYAYENMU

Na
U_F & Ashnur pyaar
®NWA

1.
Haj. Rahma ce tareda classmates dinta guda ukku, kawaye ne tun a makaranta da suke ma juna lakabi da (4stars). Yau fira suke cike da raha don an dade baa hadu haka ba. Dayar ce tayi gud'a ta ce
"Kai! Mun yi saa yar mu zata fada a babban gida, gidan ma na mai(petrol), kai lallai yarinya tayi goshi".
Suka tabe da dayar dake kusa gareta suna shewa. Dayar ta ce
"Ai dole ga bikin Jidda ayi biki na kece raini Larai, wanda sai ya kaure duniya, don dole a nunama duniya an tara kuma an je".
Dayar ta karba da cewa
"Yo in naira bata kuka me aka yi Halima? Yanzu ne fa su Rahma zasu fara aurarwa, lallai tabbas naira dole ta koka, Dan mai da 'yar mai kudi. Uhumm!".
Suka tabe dukkansu, Haj. Rahma kan wannan magana tasu ita kadai tasan yadda take ji don dadi, sai murmushi jin dadi take. ta ce
"Ai ku bari kawai, don auren Jidda shine babban buri agaremu, gashi shima a gidansu shine wanda zasu fara aurarwa".
Haba nan fa suka guda 'yarsu tayi goshi. A haka suka ci gaba da firarsu.
*****

Abba ne ya sauko daga sama izuwa dakin baki dake kasa sakamakon bakon da aka ce ya zo tuntuni yana dakin baki yana jiransa.
Dama tun zuwan bakon Haj. Rahma tuni tasa an aika masa da abinci, lemu da ruwa har ma dangin kayan itatuwa. Shigowar Abba yasa bakon sauka daga kan kujera ya durkusa kasa cike da girmamawa, ba don Abba ya girme masa ba aa saboda zamowar Abba mai abun duniya ne.
Bayan sun gaisa ne Abba yayi mashi nuni da ya zauna kan kujerarsa sannan  ya ce masa
"Malam a gafarce ni, ina wani uzuri ne?.
Cikin fara'a Malam ya ce
"Ai ranka ya dade ba komai".
Sai kuma yayi shiru yana durba-durba da alamu dai da magana a bakinshi sai dai ya rasa ta inda zai fara.
"Malam na ce ko da wata matsala ne dangane da ginin masallacin ne?"
"Aa. Dama.... Dama yaron nan ne Imrana dan makwabcina ya ga Hauwa'u Jidda ya na so shine ya ke so in mai iso sannan a bashi dama da ya turo iyayensa ayi magana, na ce Inshaa Allah zan yi ma magana duba da yadda nake da kusanci da gidan nan".
"Waye ubansa a kasar nan? Wane matsayi ne da shi? Me ya aje? Me yake da? ".
Abba ya jefi Malam da wannan tambayoyin. Jikin Malam ya yi sanyi ya ce
"D'a ne ga Alh. Bala ma'aikacin gwamnati ne a da amma yanzu yayi ritaya, sai shi yaron ya kammala makarantar koyarwa ta kwalejin Shehu Shagari, yanzu haka yana da shagon dunki, aiki ne ake nema......".
Bai karasa maganarsa ba  Abba yayi murmushi hadi da dariya ya ce
"Kai! Kai! Yaro yaro ne. Wannan ai shirme ne. Ina shi ina Jidda? Ai Jidda ba ajinsa ba ne Sam! A kudin dukin ne yake tunanin tunkarar neman auren yarinyata? Yarinyar dake gudanar da rayuwar cikin tsadaddar rayuwa, abincinta, abin shanta, suturarta, abun hawanta, muhallinta, da sauran bukatun rayuwarta duk a tsadance wanda ko gidan ubansa aka sai da ba zasu iya daukarta ba, har nawa yake samu? Nawa ubansa ya tara ya aje? Da zai yi tunanin iya tunkarar aje Jidda a matsayin mata?. Wadda ko ciwon da bai kai ya kawo ba sai na fidda ita waje don ta samo nagartacciyar lafiya, ko ba don ciwo ba na kan fita da ita kasashe bude ido.
Ka ga Malam ko a matsayin karatu ta sha gabansa, wadda ta digirgire a jami'ar dake Cyprus, ka ga ka gargade  shi da ya gargadi zuciyarsa da ta daina gwada masa ire-iren shirmen nan, don ni a shirme na daukesa. Kuma ma Jidda na da tsayayyen miji".
Ya ida maganarsa yana yunkurin tashi. Dama yaron Abba dan daman hannunsa Tijjani ya shigo a lokacin da suke tattaunawa.
Abba ya kai dubansa ga Tijjani ya ce
"Ka sallami Malam".
Tijjani ya gane ko wace sallama Abba ke nufi, don da ya ce a sallame ka toh Allah ya ci da kai don kuwa kudi ne zaa baka.
Ran Malam ya sosu kam maganganun da Abba yayi amma tunda ya ce a sallame shi ya ji ai komai ya wanke, a wani bangaren zuciyar Malam  ta bashi ai toh Abba da gaskiyarsa don ba wanda sai so ya saida Akuya ta dawo tana ci masa danga.

Bayan ya koma dakinsa ya tarar da Haj. Rahma na feshe dakinsa da turarukka kasancewar gyaran dakin da aka sake yi. Nan Abba ke gaya mata batun da Malam ya zo mashi da ita. Wani wawan tsaki taja cikin takaici ta ce
"Kaji wani rainin wayo! Ai da nasan da shashashar maganar da ya zo kenan da ko damar ganinka bai samu yi ba. Mutane da jaye-jayen abunda yafi karfinsu suke, in baccin da rashin tunani wa shi wa Jidda? Mtsww! Kai! Talaka da jawo makansa abunda yafi karfinsa yake, ko baida labarin Jidda na da tsayayyan miji?".
Abba ya amsa kiran wayar da ya shigo masa. Ai kuwa yinin ranar Haj. Rahma bambamin da tayi-tayi kenan. Ita da burinta ya kare kan auran Jidda da mijin da Jidda zata aura a ce Malam ya zo nema wa madinki auren 'yarta, har alfahari take tana shaidawa kawayenta lokacin bikin 'yarta zaa yi biki na ji da fada wanda sai ya kaure ko'ina. (Har watarana kawarta Haj. Amina ke fada mata cewa kanwarta kuwa ta bude catering sch. Ko Jidda zata shiga, budewar bakin Haj. Rahma ta ce  Inaa.... Yarinyar da zaa zube mata kuku har wani abinci zata koyo? Kin manta gidan da zata yi aure ne? Ko kin manta dan waye?). Wani kyacci ta kuma saki, lallai Malam ya kuru don da gabanta ne yake fadi sai yaji ba dadi.

A BANGAREN JIDDA kuwa. Ta je bikin yayar kawarta da ake yi a Abuja, tareda direba da 'yar aiki Izzatu da aka hada ta da ita don zata yi kwana biyu a can kuma ita bata yiwa kanta komai, komai kankatar abu sai dai tasa yan aiki suyi mata shiyasa da zata zo bikin Haj. Rahma ta hada ta da mai aiki.

A gajiyace ta fada kan gado sakamakon dawowarta dinner kenan don bata jira an karasa da ita ba, a can ma ta baro kawarta Saleema. Duba agogon hannunta tayi ta ga biyu da rabi na dare.

"Assalamu Alaikum".
Ta sake furtawa, karo na ukku kenan tun shigowar ta cikin dakin take sallama a bakin kofa amma bata ji an amsa ba.
Koyaushe tana mamakin irin wannan hali na Jidda, sai da tayi har sau hudu kamar yanda ta saba kullum, sai a dai-dai wannan lokaci ne ta tsinkayi amsan sallamarta daga can k'asan mak'oshinta.

Tsugunawa tayi har k'asa ta gaishe ta, don dama ba da ita aka je dinner ba, a cewar Jidda a wurin nan ire-irensu basu da muhalli.
Kamar ba da mai rai tayi magana ba, bata karaya ba ta sake maimata abinda ta fad'i wannan karonma kamar ba zata tanka ta ba, can kuma sai ta nisa ta ce
"Ki cire man talkaman dake kafafuna ki kaisu a ma'ajiyarsu, sannan ki bude trolley ki fidda man da Rigar bacci ki fisheta da turarukka ki a zaman gefen gado, bayan nan ki koma toilet ki hada man ruwan dumi".
Cikin 'yan mintuna da gudanar da komai da aka umurceta. Cikin girmamawa ta ce
"Ranki ya dade an yi yadda kika ce".
Ba tareda ta kai kallo wurinta ba ta ce
"Ga koriyar jaka can ki dauka da duk abun cikinta".
Izzatu tayi godiya sosai ta dauka ta fita tana murna tayi sashen yan aikin gidan.
Washegari yinin biki, ita kuma ba mai son haniya ba ce don haka ta dawo gida.
*****

BAYAN SATI DAYA a cikin satin Abba yayi tafiya.
A tarihin gidan ya dade bai samu gyara irin na yau ba, gyara abunda ar gyara, komai tas ko ina tas ko wane sako da lungu na gidan yana fidda kamshi, wannan gyara kuma ba komai bane face zaa gudanar da bikin zagayowar haihuwar Jidda bisa cika shekara ashirin da ukku a duniya kuma tayi gayatar manyan kawayenta gashi dan Ministan mai shine babban bako. Yau hadda 'yan aikin gida sun shaida haka saboda fara'ar dake dauke da ita tunda safiyar Allah ta waye.
A jiyan kafin yau saurayinta wanda take so yake sonta wanda iyayenta ke burin ta aura kasancewarsa dan Minista ya iso kan bikin zagayowar ranar haihuwarta.
A jiyan ba cimmar da baa jera masa, sai dai iya coffee kawai ya sha don shi irin masu rayuwar turawan nan ne don ko a cikin maganarsa hausansa kwara-kwara ce a ciki. Bayan ya gaida Haj. Rahma, aka Jidda tayi masa iso ya gaida Inna (Mahaifiyar Abba), ba don ta so ba saboda sanin halin Inna don sam basu jittuwa da ita, Inna tafi shiri da Hameed kananta.

Fura take sha tana sauraren rediyo suka shigo sagale da hannu, shigarsu kenan Sajid ya zame hannunsa yayi hugging Inna tareda fadin
"Ina wuninki Granny? How are you?".
Jidda tayi murmushi, ita dai Sajid na burgeta haka komai nasa na burgeta, yasan rayuwa kuma ya iya tafiyar da ita, a rayuwarta tana son harkar wayewa. Wayarsa ce ta yi ruri hakan ya dawo da ita daga tunanin da ta lula a ciki.
Yana fita ta biyo bayanshi  yayin da Inna ta zauna kamar komai an zare daga jikinta.

Koda Hameed ya shigo ya tarar da Inna na kuka ga hawaye shabe-shabe a fuskarta harda su fyace majina.

Don't forget to vote pls

 KUSKUREN IYAYEN MUWhere stories live. Discover now