Daga wasa......

1.4K 145 42
                                    

KUSKUREN  IYAYENMU

NA
U_F aur Ashnur pyar

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.

Dedicated to miemiebee,mrspurple,fatyjum are,zainab yunus

3.

Bayan Gadanga Dan Fanfo ya sake fitowa tsakiyar fili sai MC yake tambayarsa
"Idan da princess Jidda zata baka dama guda d'aya tak, mece ce bukatar ka a gare ta?".
Bud'an bakin Gadanga sai cewa yayi
"Ni inda a ce Lobin dina zata ban dama d'aya tak! Bukata ta bata wuce kawai in aure ta ba".
Gaba d'aya hall d'in aka kece da dariya, banda Sajid wanda gaba d'aya hankalinsa baya ga abinda ake yi, hankalinsa na can kan iphone din dake hannunsa sai faman latse-latse yake yi, kuma dama shi bai fiye son hayaniya ba, shiyasa tun bayan mikawa fiance sa kyauta da yayi ya koma kan wayarsa, be kuma ta komawa kan abinda ke wakana a cikin hall din ba, in banda dalili ma irin wannan ba abinda zai kawo Sajid
wannan guri.

A tunanin Mc Gadanga   bai wuci yace soyayyar Jidda yake nema ba, sai gashi shi mai gaba d'aya  yace aurenta yake so aba shi, lallai wannan wautarsa ta kai wauta.
Bayan hall din ya dan lafa daga dariyar mutane  cikin gatse Mc ya cigaba da magana da cewa
"So fans lets play April fool to this guy and see his reaction".
" Yes soooo!........" Mutanen hall din suka sake amsawa.

"To yanzu Gadanga idan princess ta amince da aurenka mai zaka bata a matsayin sadaki, kasan dai aure bashi yuyuwa dole sai da sadaki ko?".
Cikin jin dadi gameda k'ombo irin na samarin k'auye yace
"Yo kwarai kuwa na sani, amma in har Lobin zata yarda ni yanzu haka naira dubu d'aya da d'ari biyar gare ni, suke nan gaba d'aya kudina, sai wanann zobunan azurfa dake hannu na, daya zai kai kimanin dubu hudu, dayan kuma zai kai dubu shidda, idan ta amince sai na bata su a matsayin sadakinta".
Cikin muryar dariya Mc yace
"Princess Jidda kin ji fa mutumin naki, kin amince?".
Cikin dariya Jidda ta  d'aga Kai alamun amincewa, ita gaba d'aya saurayin dariya yake bata, lallai ta kara tabbatar da dan kauye cikakken hamago ne.
"He is so funny indeed".
Ta furta a hankalihankali. Mc yace
"Ki amsa da baki mu ji ko Gadanga zai ji dad'i".
Ba tareda tunanin komai ba Jidda tace
"Eh na amince".
Nan fa Ali Gadanga ya rasa ta inda zai sa kansa don dadi, shi kam dadi zai ballasa gaba-gaba, yau Lobin dinsa zata zama mallakinsa, yayinda wasu ke dariya don mafi yawa a gurin daukar bai da cikkaken hankali, baccin haka wa shi wa Jidda.

Gadanga ya ciro kudin  dake aljihunsa yana kaud'i, 'yan d'ari-d'ari ya k'irga guda goma, sai dari biyar da ta kunshi su dari yan hamsin har ashirin akwai ciki, ya mikawa Mc hadi da zobunan. Gun ya sake daukan tafi raf!...raf!..raf!.. Domin  a sake nishadantuwa Mc ya fara k'irgen kudin.
Jin hayaniyar ta su tayi yawa yasa Sajid mikewa tareda fad'in
"Excuse me"
Yace da Jidda yana kokarin mikewa
"Ok dear"
Ta amsa shi ba tareda ta lura ma da yanayin fuskarsa ba, ita gaba daya comedyn Ali ya tafi da ita dan ya iya bada dariya, yau ya nishad'antar da ita sosai.
"Dubu da dari hudu da hamsin.... Dubu da dari biyar.....yeeeeeee!". aka dau sowa, kudi sun cika cif!. Mc ya mika ma Jidda kudi da zobuna ta karba tana fidda murmushi.
Gadanga har ya jawo abokansa su biyu cikin azarbabe, ya ce cikin muryar sauri
"Ga Falalu da Ummaru abokaina ne kuma yan uwana, na wakiltasu a matsayin waliyai na, saura Lobin ta fadi nata waliyai".
Wata dariya Jidda tayi
"Wai Lobin".
Ta furta a hankali, lallai duniya akwai gaulaye. Sai da tayi dariyarta mai isarta sannan ta ce
"Hameed da Uncle Zaks su ne waleyaina".
Gurin ya kaure da hayaniya. Uncle Zaks ya ce
"Ni Zaks na bada auren Jidda bisa sadaki dubu da dari biyar da zobuna da suka yi kimanin dubu goma, don haka na mallaka maka ita, cinta, shanta, suturarta, muhallinta, addininta, kun karba?"
Ummaru ya ce
"Eh mun karba kuma mun amince"
Zaks ya ce
"Jamaa kun shaida"
Sai mutanen hall ya dau cewa
"Eh mun shaida".
"Toh ayi salati".
Daga karshe kamar hadin baki mutanen gurin suka ce
"April fool!".
Dama 12am na dare ya guta, Mc ya dafa kafadar Gadanga cikin dariya ya ce
"Ali Gadanga zaka iya koma wurin zamanka, an kammala wasan kwaikwayo".
Jiki ba kwari Gadanga ya fita hall din saboda zuciyarsa dake kona irin rena masa wayo da sukai.
"Wai me yasa wasu masu kudin ke ma talaka yadda suka so?"
Wata zuciyar tasa ta tambaya....✍🏻

Toh makaranta meye ra'ayoyinku kan auren wasan nan? Shin kuna ganin auren ya dauru ko bai dauru ba?.

Vote
And comments pls 

 KUSKUREN IYAYEN MUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora