KUSKUREN IYAYENMU
Na
U_F & Ashnur❤®
NWA10.
Washegari ko da ta je ta isko dukansu ma'aikatan gidan bakin dakin maigadi, ciki harda Izzatu, suna fira cike da raha, cikin girmamawa ta gaishe su, nan Izzatu ta ce
"Umm bari ki ga in je in karbuwa Inna katin waya kafin ta neme ni. Wai kin san dake yau Jidda zata fita siyayya kuwa?".
"Ni?".
Meramu ta tambaya tana zaro ido
"Eh ke fa. Zaki raka ta sayayya gobe su Haj. da Alh. za su dawo daga kasar ingila, in dai kin shiga Jidda za tai maki bayani".
Mani ya karba da cewa
"Ni ma dai bari na tashi, wankin motan Jidda fa zan yi na shiririce a nan".
Nan gungu ya watse kowa ya kama gabansa.Sai da ta je gun Inna ta gaisheta sannan ta karasa daga ciki. Kicibus suka yi bakin kofa, hakan yasa Meramu ta dawo tareda nusar da kai kasa
"Ina kwana?".
Ta gaisheta.
"Lafiya".
Shiru ya gifta can kuma ta ce
"Ki biyo ni".
Tana ida maganarta ta wuce, a sanyaye ta biyo bayanta don tana mugun tsoron cin mutuncin Jidda, Jidda bata ganin kowa da gashi, ta kan iya ma mutum rashin mutunci, wulakanci, zagin kaskanci sai ta mashi, barinma kana ci karkashinsu.Wurin ma'adinar motoci ta tsaya cak, motarta ta kalla da kyau tana ya mutsa fuska, cike da bacin rai ta kira sunan Mani, cikin sauri ya karaso wurinta, kallon wulakanci ta wulga masa sannan ta ce
"Ashe baka wanke man motata ba? A haka kake son na fita da ita duk datti?".
"Ya hakuri ranki ya dade, na zata ba yanzu zaki fita ba?".
"Dalla yi man shiru matsiyaci dan talaka wawan banza kawai, in bancin dakikanci in ce maka 10am zan fita kake kira man baka zata ba, don dakikanci da jahilci. Mtsw".
Ta ja tsaki ta koma cikin gida. In ranshi yayi dubu ya baci, sai dai ya zai yi nan yake samun abunda yake kaima iyalinsa.
Bokitayya ta dauko, daya ya hada ruwan kunfa, sauran kuma ruwan da zai daurayeta ne.
Cikin zafin nama ya shiga wanke motar, kofi ya ciko da ruwa da nufin watsawa saman motar, yayi rashin saa sai ga jikin Jidda, ita kuma komawar da tayi mukulin motar Haj. ta dauko. Bai an karaba ya ji saukan mari tas a kuncinsa
"Ni zaka watsa ma ruwa? Wai kai wani irin dakikin mutun ne? Mtsww ".
Ta juya da nufin komawa cikin gida.
Sai da ya fidda kwallan bakin ciki, a haife zai haife ta, yana tsaran ubanta amma harta iya daga hannu ta marinsa.
"Duniyan nan baka yi ba tayi maka bare ka yi, da sannu zaki girbi abunda kika shuka".
Ya furta a hankali kana ya cigaba da aikinshi.Bayan mintuna kadan sai gata ta sake fitowa ta tsantsara ado cikin wani dankararen uban lesi green mai ratsin orange dauke da adon stones.
Cikin takun isa da gadara har ta kai ga motar da zata fita da ita kirar Mercedes benz.
Gaba Meramu ta bude ta shiga ta zauna cikin dari-dari.
"Fita joor, ji wata kodaddiyar atamfa da kika sa, in na fita dake ai sai ki rage man gp(aji), dallah fita!".
Ta idar maganar cikin tsawa. A sanyaye Meramu ta fito cikin motar ta koma cikin gida da gudu-gudu tana kwalla.
*****Ranar da ya koma Gusau washegarin ranar ya koma sake dawowa Sokoto kasancewar Basiru ya shaida masa Babansa ba lafiya yana fama da matsanancin ciwon kai.
Yana isa Fanfo wannan karon gidan Mal. ya wuce yasan ba abunda zai zaunar da shi shago tunda bai jin dadi. Bai tsaya wata-wata ba ya ce da shi ya zo ya kai shi asibiti a duba lafiyansa, harda Mal. ya kiya Ali ya tursasa sai dai sun je asibiti.A uduth suka je, basu wani shan wahalan ganin likita ba saboda Kamal dake aiki a asibitin. Magungunna aka rubuta masa, Ali ya tsaya gawon nama don ya saya. Ya shiga pharmacy din kenan, shi kuma Mal. Iro ya ga wani mai baro na saida d'wata da yalo, sai ya fito motar da nufin sanyen d'wata, dama gurin akwai masu saida abubuwa ciki harda masu saida lemona da ayba. Fitowarshi mota takun da zai yi dayan biyu sai yaji ya zame luuuuu sai jikin wata budurwa, (hakan da zan yi ni U_F sai naga ashe Jidda ce. Tab Na kalli Ashnur muka jinjina kai).
Hannu biyu-biyu tasa ta turesa kansa ya bugi booth din mota, cikin bacin rai take magana
"Ji min tsoho banza, ai wannan iskanci ne, toh me ka ji yanzu a jikina? Tsohon banza dan iska, ko dan iskan ma lamba daya".
Nan wani saurayi ya ce
"Ke dalla Malama baki ga abunda ya taka ba ne?".
"Ina ruwana ko uwarsa da ubansa ya taka, shege dan shishshigi".
Tana gama fadin haka ta koma cikin mota, ta fiddo space (no respect) cikin jikarta ta maka a fuskarta, ta tada mota.Tun fitowarsa shago yake jin maganarta don da karfi take magana, sai dai bai san da waye ta kema wannan kaskancin ba, kan ya karaso har ta shige mota ta fara ja, ya ga fuskarta sarai ya kuma tuna the same girl din da ta jima tsohun nan a yatsu ranar a gidan mai.
Da sauri ya karasa bayan motorshi ganin Mal. zube a kasa, ga jini a goshinshi
"Babana me ya same ka?".
Nan wani saurayi dake gurin, da abun ya faru gabanshi ya ce
"Wallahi wannan tsinanniyar yarinyar ce ta turesa da karfe ya buge kanshi ga motarka. Ka ga fa kwalfar ayba ya taka sulbi ya ja shi cikin rashin saa ya kai gareta shine ta mai haka ta zazzage shi. Kai yarinyar nan bata da mutunci wallahi".
Gab ya bugi mota cikin konan zuciya, take idanunshi suka rikida, har an haifi yarinyar da zata ci ma Babansa mutunci ya kyale
"Never!".
Ya furta da karfi.Kai shi yayi akai ma gurin dressing sannan suka wuce zuwa Fanfo.
Tuki yake ranshi a jagule yake, shi kam Mal. ko mai kasa furtawa yayi, shima kanshi ranshi a bace yake, tunda Allah ya halacci shi baa taba masa irin cin zarafi haka ba sai yau, wai harma a kirasa dan iska
'Tsohon banza, dan iska'.
Kalaman nan suka sake dawowa a kanshi, zirrrrr sai hawaye suka yi zarya a kuncinsa, yayi saurin gogewa kada Ali ya gani, sai da kash tuni Ali ya ga fitowarsu. Har suka isa ba wanda ya ce da kowa uffan, Mal. na shiga gida, Ali ya wuce na su gidan.Komai kasa yi yayi saboda zuciyarsa da take zugi har wani radadin bakin ciki yake ji, shi kam yana ganin faruwan wannan abu tamkar kaddara ce da zai shiga rayuwarta don gyarata.
'Ina son in kaskanta yarinyar nan in nakassa rayuwarta, in hana rayuwarta walwala, in jefa rayuwarta cikin bakin ciki, in ganta tana zubda hawaye koyaushe'.
Wata zuciyar ta ce da shi kasa a sace ta ka yaga rigar mutuncinta
"Aa!".
Ya kuma fadi da karfin gaske.
"Ina so in kaskantata when she is under my control".
Ya sake furtawa. Zirga-zirga yake tayi yana sake-sake a zuciyarshi.
ESTÁS LEYENDO
KUSKUREN IYAYEN MU
Misterio / SuspensoKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...