KUSKUREN IYAYENMU
Na
U_F & Ashnur pyar
®NWA2.
Wayarta kirar Nokia karama mai tocila(touch light) wadda hausawa ke kira da (rakani bayi) ta d'auko ta mik'awa Hameed tace
"Ungo Hameedu latsomin d'annan (Abba), dole in fad'a masa Hauwa'u ta shigo mai da d'an iska cikin gida". Ta sake rushewa da kuka had'i da fyace majina, ta cigaba da magana
"Inyin.... A ce tsofai-tsofai dani a ce za'a lalata min rayuwa....inyun.......".
Ta k'ara fyace majina, Hameed kam sai dariya yake yi ciki-ciki ba tareda ya bari ta gane dariyar yake yi ba, don in har ya sake tayi arba da shi yana dariyan to ko tabbas fad'an kanshi zai komo.
"Ungo nace ko baka jini ne inyin?... Ka wani tsaya min wani sandan da kai kamar tsanin gyara wuta".
Ta k'arasa maganar tana mik'a masa wayar dake hannunta
"Maza ka latsomin shi(Abbansu), don yau sai na fad'a masa lalacin da yaron nan ya min, iskanci karara, ai ni bakomai yafi b'atamin rai ba irin kirana da yayi da sunan kafirai... Oh! Ni jikanyar Tumba!".
Hannu yasa ya karb'i wayarta, wacce ita kanta wayar sai da aka sha fama da ita kafin ta amshi irinta, dan lokacin da aka fara bata waya fad'a ta rik'ayi me zai sa a had'ata da kayan Aljanu, takance ku dai da ku ka ga zaku iya ku je can ku yi tayi, amma ni kubar ni na sha ruwa. In ance mata Inna ba Aljanu ba ne ta kan ce
"Yo Aljanu ne mana, in ba haka ba ta yaya zaka kira wani dake can wani guri daban sannan ku yi magana?, Wannan ai sai aikin jinnu, su kad'ai ka wannan aikin".
To sai da k'yar da lallami fa aka samu ta amshi waya a hannunta, anan ma tace bata iya rik'e babbar waya gara k'arama wacce jinnun cikinta ba suyi k'wari ba.
Ko da ya kira nomban Abba bai shiga ba, don dama yayi tafiya tun cikin satin can.
"Inna ina tunanin fa Abba yana wani uzurin ne domin wayarsa a kashe take".
"Kai dai kawai ka ce ba zaka kira min shi ba, tsoronta( Jidda) ka ke ji ko?, ta ya za ace be shiga ba bacin an ce kowa ne lokaci za ka iya magana da mutum?. Bani kayana".
Ta fad'a yayinda ta mik'a mai hannunta, sa' ilin ya sanya mata wayar cikin hannunta sai faman kunshe dariyarsa yake.
Data lura da dariyar da Hameed ke yi, sai ta wawuro sanda tana fad'in
"Kai ma zo ka fice min daga nan ko in mangare ka da wannan sandar." Da sauri Hameed yayi waje yana dariya.
****
DANKANE GUEST INN.
Zaune suke cikin hall d'in, wanda yasha decoration da nau'i daban-daban na fulawoyi, ga balobalo ta ko'ina a jikin bango a mammanna, ta gefen baloons din kuma doom light ne ke kawowa suna daukewa, daga can kan stage din M.C ne rik'eda microphone yana jawabi.
Jidda da Sajid zaune suke a kan kujeru masu matatukar kyau, suna fuskantar juna, wankan(Dressing) da suka yi ne yasa kowa a cikin hall din su yake kallo domin sun tafi da zuciyoyin jama'a, don a b.u.g clothing suka yi ordering.
M.C ya buk'aci Sajid daya fito ya ce wani abu a matsayinsa na fiance din celebrity. Yana mik'ewa tsaye mutanen dake cikin hall din aka d'au tabi.
Tunda Sajid ya haukan stage mata suka fara santin kyawonsa da had'ewarsa, don tabbas duk inda ake kiran mai kyau toh tabbas Sajid ya kai.
Cikin harshen nasara yake jawabinsa har yayi ya gama tareda yiwa Jidda fatan wasu shekarun masu albarka. gaba d'aya ya tafi da zuciyoyin 'yan matan dake gurin, bare kuma b'angaren Jidda da ta ji sonshi ya karu har cikin ranta, ita dai tana son wayayyen mutum dan gayu mai aji.
Bayan babbar kawarta Saleema ta fito ta ce wani abu, nan Dj ya saki sauti, aka dan cashe, inda daga bisani Mc ya bada yan mintuna don aci asha, sanna. ya bukaci tashin Jidda tsaye don fara mika mata birthday gift. Sajid ne ya fara fitowa da yaransa guda biyu masu take mai baya, d'ayan na rik'e da wani d'an karamin box.
Sai da suka karaso gunta ya amshi dan karamin box din, sannan ya ciro d'an mukullin mota a aljihunsa ya mik'a mata, raf..raf...raf...wurin ya dau tafi baki d'aya cameraman beyi wata-wata ba ya dauke su hoto.Haka sauran friends suka mika ta su, kowa da irin tashi bajintar, domin kowane kyauta ta ji da fadi ya kawo. Kafin ta koma mazauninta kenan sai ga wani saurayi ya fito, fitarsa kenan wurin ya kaure da dariya irin shigarsa da yayi. Wandon jeans a jikinsa sai polo shirt sannan ya makalo necktie, yasa talkamansa half cover. Kara kallon adonsa yayi tsaf amma ya rasa abunda suke ma dariya, don shi a iya wanka toh ya wanku, don duk randa yayi irin wankan nan a kauyensu rikici yake hadawa tsakanin yan mata.
Ledar viva baka ya mika ma Jidda dauke da murmushi a fuskarsa. Jidda kam kasa daka hannunta tayi saboda dariyar da take yi.
'Wannan kuma daga ina?'.
Wata zuciyar ta tambaya. Tayi mamakin yadda aka bari ya shigo nan.
Bata an kara ba ne ta ji Mc na fadin
"Toh fa wannan kuma daga ina?"
Saurayin ya ce
"Daga Fanfo karkashin karamar hukumar Bodinga".
Mc ya bushe da dariya
"Fanfo!....".
Mc ya sake maimaita sunan garin, ai ko kowa dariya yake.
"Ranki ya dade ko ba a bude kyautar kowa ba, ya kamata a bude na shi domin mu ga bajintar dan Fanfo".
Gurin ya kaure da
"Yes so......!".
Cikin dariya Jidda ta ce
"Go ahead".
A hankali Mc ya fara bude ledar. A cikin ledar greeting cards ne guda biyu sai turaren emergency da farar takarda, Mc ya bude greeting cards din ya nuna ma kowa, a cikin cards ne duka birthday wishes sai 4rm edge 2 edge an rubuta da biro 4rm Gadanga 2 u Lobin dina, Mc ya karanta abunda ke ciki, ai fa kowa me zai yi in ba dariya ba a zamanin nan yaushe rabo. Sai ya walwale farar takardar, tun kafin ya karanta bayyane yake dariya harda rike cikinsa. Ga abinda takardar ta kunsa.
"Assalamu Alaikum yake zunzurutun mazurar azurfar rayuwata.
Lobin dina! Wannan sammacin soyayyata ne domin ina cikin jabarawar begenki, ina ma a ce ki zamo guga in zamo igiya mu taru mu janyo ruwan soyayya, domin duk lokacin da naga fotonki sai in ji fure ta cikin jikina, hakan yasa a garinmu ake mani dayiya amma hakan bai dame ni ba. Ina sonki! Ina sonki! Zan aure ki! Don ina cikin wani matsanancin tsagwaron laulayin azabebben zazzabin zazzafan sonki".
Hall din ga baki daya ya kaure da kuwa, kowa sai dariya yake, saurayin dai gefe ya koma, yana mamakin su don shi sam bai ga abun dariya ba don kwan cikinsa ne ya amayar. Tuni Jidda ta koma mazauninta.
Dai-dai kunnen Jidda Mc ke fada mata
"Ranki ya dade idan kin bamu dama zamu kara nishadantuwa da Dan Fanfo, kin san yau 31st March ne daren April ne sai mu yi wasan April fool da shi".
Jidda bata musa ba, hakan yasa Mc sake gayatar Dan Fanfo a fili.Vote
And
Comments
ВЫ ЧИТАЕТЕ
KUSKUREN IYAYEN MU
Детектив / ТриллерKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...