Bazata...

1.4K 125 19
                                    

KUSKUREN IYAYENMU.

NA
U_F & Ashnur❤

®
NWA

7.
Gadanga........ Gusau..
Ali da ne ga Alh. Ahmad ana masa inkiya da Attajiri, sunan da ake kiransa kenan saboda arzikinshi, dan asalin Fanfo ne dake karkashin hukumar Bodinga dake Sokoto. Matarsa daya Haj. Asma'u, ita ce mahaifiyar Ali Gadanga, Ali ya samu sunan Gadanga ne daga kanen maihafinsa. Sai kanwarsa Amina, sai Sadiq sai auta Sagir.
Mahaifiyarsa asalin 'yar Gusau ce a jahar Zamfara, 'ya ce ga sarkin Katsinan Gusau. Ta hadu da Ahmad lokacin da ya zo Gusau ci rani, Allah ya hada su har suka kai ga aure. Ya dawo Gusau da zama saboda kasuwancinsa.
Tana zaune lafiya da mijinta da 'yan uwansa.
Ali mutum ne kyakkyawa mai kwarjini, ya ta so cikin gata ga iyayensa da kakaninsa na gefen uwa don koda ya waye kanshi bai tarda kakaninsa da uba raye ba, kasancewar shine jika na farko ga Sarki Muhammadu. Duk da haka gata baisa ya lalata tarbiyarsa ba, ya tsaya yayi karatu gefen boko da na Islamiyya.
Baya kula macce saboda ya tsani raini a rayuwarsa, shiyasa baya shiga duk wani abu da ya shafi macce(Soyayya). Ko kannensa tsoransa suke, zaa yi wasa da shi yanzu amma anjima ya rikida kamar ba shi ba, ga shi ya kware wurin basaja, idan ya canza maka zaka yi wahalar ganesa.
****

Sai karfe ukku na rana ya shigo Sokoto zai wuce kauyensu Fanfo, amma zai tsaya wurin abokinshi Kamal kafin ya karasa.
A shopping complex ya tsaya yayi sayayyan kayan chocolate don kaima 'yar abokinsa.

Kwanar zuru road ya shiga, dai-dai kofar wani gida ya tsaya. Horn yayi Maigadi ya bude masa, dama ya kira Kamal a waya ya shaida masa zuwansa.
Tarba mai kyau ya samu a gidan, don matar Kamal na da mutunci sosai, 'yarsa ma harda oyoyo tayi masa, mika mata chocolate din yayi cike da murna ta karba, mamarta tayi godiya suka wuce daka don basu guri su zanta.

Cike da zolaya Kamal ya ce
"Azumi mai zuwa har Gusau zani na yi ma wakar gwauro! Gwauro! Gwauro! Gadanga tashi gari ya waye! Gwauro!".
Ali yayi dariya tareda kurbar lemun dake gabansa.
"Allah Sarki Babana. Da zarar an ce Gadanga sai ya fado man a rai, tamkar ga bakinsa sunan nan aka zana shi".
"Daddy?".
Cewar Kamal yana gyara zamansa
"Idan ka ji na ce Babana toh Baba Iro. nake nufi, ni har yaushe nasan Daddy shine mahaifina?. Baka ga da Aliyu Ibrahim nake amfani ba Aliyu Ahmad ba? Ai da Baban Basiru Ibrahim da Daddy uwa daya uba daya suke ".
   "Oh! Haka fa. Toh me yasa kake amfani da sunansa?".
"Ai tun ina karami aka ce idan aka zo sallah Fanfo toh har ban son dawowa Gusau saboda soyayyar dake tsakanina da shi, mugun so na yake tamkar dansa Basiru koma in ce fin haka, Haj. (Mahaifiyata) ta ce watarana da kuka ake dawowa dani saboda makaranta, idan kuma ana hutu ne can ake baro ni wurinsa.Tun da Daddy ya saka mu makaranta ni da Basiru da sunan Baba Iro. ya bada, kai da an ce waye Babana shi ne nake cewa, kuma shine ya rada man Gadanga, tunda aka haife ni aka ce an radamin suna Aliyu ya ce an samu Gadanga, shike nan fa sunan nan ya zauna bakinsa, a kauyenmu ma wasu Baban Gadanga suke kiransa.
Yanzu ma can zan karasa don na dade ban zo ba saboda karatu, na ce bari mu gaisa sai in karasa wurinsa".
   "Allah Sarki! Haba ka bari sai gobe mana mu sha firar yaushe gamo".
"Inaaa ko giwa da hadeye ni yanzu sai ta amaye ne garin Fanfo. Na jima fa tun hutuna na farko a makaranta da na zo a lokacin amaryarsa ta haihu mun zo barka da Haj. Ban sake dawowa ba sai dai in yi waya da shi".
    "Kai! Kai! Lallai ka Dade".
"Da a kasar nan nayi karatu me zai sa na jima haka? Ai nayi kewar Babana. Uhummm! Ka ga tafiyata".
Ya tashi tsaye. Kamal bai so ba amma ya ya iya. Haka ya rakosa har mota.


Shigar doguwar riga tayi baka mai jajayen dowatsu, ta yarfa gyalen rigar a kafada, ta saka space a idonta, tayi kwalliya dai-dai misali, sai talkaman da tasa mai tsini.
A hankali take saukowa daga sama cikin kasaita da gadara.
Kawayenta biyu a falon kasa suna jiranta zasu fita tare, yayinda Meramu ke ta goge-gogenta a falon.
"Wow! Wow! Kai Jidda kin hadu fa. Kina wuta wallahi".
Cewar daya daga cikin kawayenta, Meramu ta kai dubanta ga Jidda suka yi ido hudu da ita. Bata an kara ba sai ta ji rankwashi a kai tareda fadin
"Kin saki baki galalala kina kallona, bakauyar banza kawai".
   "Baki da sauki fa".
"Hahahaha na kai ku?".
Suka tabe suka fita.
Meramu harda digin hawaye saboda ciwon da ta ji.

A wani masallacin dake cikin wani gidan mai ya tsaya don sallar laasar. Fitowarsa kenan ya yi tozali da 'yan matan dake cikin mota, Irin tsofafin nan mabarata daya daga cikinsu ya karaso gaban motar yana
"A taimaka fisabillilahi. A taimaka don Allah".
Ko kallon banza bai isa Jidda ba sai cin cingom take kas kas. Da mai tatsar mai ya mata alamun an  zuba yasa ta sauke glass don basa kudinsa, hakan yasa tsohon kara karasowa gefenta, hannunsa ya aza kan murfin motar. Cikin ko ina kula ta tada gilashin motar hakan ya dan jima tsohon ga yatsu, kara sauke glass din tayi ta wulga masa dubu daya tareda fadin
"Sorry".
Ta ja motar. Duk wannan abun kan idon Ali aka yi. Ranshi ya sosu, cikin sauri ya kai ga tsohon ya bashi hakuri tareda bashi wasu kudin. Tsohon yasa masa albarka sosai, nan mai tatsar mai ya ce
"Ai in dai yarinyar nan ce kadan ma ga gani Maigida, yar wulakanci ce ta karshe, akwaita da wulakanta talaka, a wurinsu talaka ba a bakin komai yake ba".
Ali bai ce komai ba ya koma motarsa ya shiga ya kama hanya zuwa Fanfo, ziciyarsa na kona.
Tuki yake sai jan tsaki yake yana fadin
"Shiyasa naki yarda Daddy yaba su Amina dama irin haka. Ina amfanin wannan?".
Ya kuma sakin tsaki.
'Ko waye ubanta da take wulakanta jamaa haka?'
Wata zuciyar ta tambaya.

 KUSKUREN IYAYEN MUWhere stories live. Discover now