KUSKUREN IYAYENMU
Na
U_F & Ashnur❤9.
Sai bayan azahar Meramu ta tashi daga bacci. Tafe take tana dafe bango saboda jirin da take ji, ta fito daki ne da niyar zuwa baya wurin Izzatu. Da kyar ta iya kaiwa.
Da sauri Izzatu ta kamota ta zaunar tareda fadin
"Sannu Meramu. Har yanzu jikin ko?".
Meramu ta girgiza kai alamar eh
"Bari na kawo maki abinci ki ci sai ki sha magani sai ki yi sallah. Allah Ya kara sauki. Sannu kin ji".
Cikin kankanin lokaci da kawo mata dafadukar shinkafa da alayyahu cikin plate, sai pure water da ledar magungunnanta.
A hankali ta fara ci har ta cinye, ruwa ta sha ta kora magani. Ta dau mintota zaune daga bisani ta je tayi sallah.Tana ida sallah ta sake komawa ta kwanta, wannan karon ba bacci take ba kwance kawai take.
Bub aka bugo kofa, wani abu sai Jidda. Kafa tasa ta fara bubbugar kafafunta tana cewa
"Ke matsiyaciya ina wallet din da kika dauka a dakina?".
Da kyar ta yunkura ta tashi saboda azababben ciwon kan da take ji, cikin marairaicewa Meramu ta ce
"Wallahi ban dauka ba".
Dai-dai nan Inna ta shigo, ta zo duba jikin Meramu.
"Lafiya Hauwa'u?"
Ina ta tambaya ganin cika da batsewar da take
"Ina fa lafiya, daga zan fita na barta ta gyara min daki yanzu na dawo zan ba Mani ya anso man kati na duba banga wallet din na ba, wannan matsiyaciyar yarinyar nan ta sace. Daga gyara min daki fa?".
"Wallahi Inna ban dauka ba".
"Ina shedarki Meramu".
"Kamar ya kina shedarta? Karya zan mata ne? Ki bari bana son haka Inna, kada ki sa ta raina ni".
Sai ga Izzatu ta shigo, miko wallet tayi ta ce
"Ranki ya dade dazu Sule Maigadi ya kawo ya ce a aje maki kin yarda kasa a lokacin da kika shiga mota.
"Oh!".
Ta ce ta karba, ta fita ko kunya. Meramu tuni hawaye sun wanke mata fuska, wannan abu har ina, yau wai ita ce aka ma kazafin sata, kawai sai ta fashe da kuka.
Inna ma habar dan kwalinta tasa tana matsar ido tana fadin
"Duk ku ka ga na fadi toh bakin cikin Hauwa'u ne ya man yawa ya kada ni"
"Ya hakuri Inna, watarana ko an ce tayi ma ba zata yi ba".
Cewar Izzatu.
Inna bata ce komai ba ta juya ta fita.Izzatu ne da Meramu bakin titi ta zo ta sama mata napep ta tafi gida tunda bata jin dadi. Nan take ta bata hakuri kan abubuwan da Jidda ke mata, ta kara da cewa
"Idan kasan halin mutum sai kai ta takatsantsan da shi, kafin zuwanki ni kadai nake ta shan walakanci, amma wallahi kanenta Hameed ya fita mutunci nesa ba kusa ba, kin zo a lokacin da yana can waje wurin karatu. Kiyi hakuri kin ji?".
"Bakomai"
"Bari na tafi na baro abu kan wuta, Allah Ya kara lafiya, a gaida Umma".
"Amin nagode. Umma zata ji".
Izzatu ta wuce tareda mika mata dari biyu na napep.Ta yi kusan minti goma bata samu napep din da zata dauketa daga Kalambaina road zuwa Tudun wada ita kadai ba, kuma bata son hawan mashin a yanayin da take.
Juwa sai dibanta take, tana rangaji kan titi, horn taji ana danna mata kwarai, hakan yasa ta rude ta rasa ta wani gefe zata.
Kit ya ci je birki, harda a jiyar zuciya yayi, Ali ya fito ya ce
"Malama ba kya gani ne? Kan hanya fa kike. Don Allah ki kiyaye".
Hakan da ya ce ta ji dadi, tasan a dokance ita ce me laifi amma yake bata hakuri, juyowa tayi suka yi ido hudu da shi ta ce
"Kai ma don Allah ka yi hakuri, wallahi ba dagangan ba".
Ta koma daga can gefe tana jiran napep, cikin saa kuwa ta samu wani ya dauko mata biyu, ta gaya masa unguwar da zata, ya ce ta shiga don Sokoto cinema zai kai wa'ennan.Sai marece Ali ya bar garin Sokoto ya kama hanya zuwa Gusau ta Sambo.
Awa biyu da mintota ya isa garin Gusau da gidansu dake Gada biyu."Oyoyo Ya Ali"
Cewar Sagir da gudunshi, shima Sadiq karasowa yayi yana masa sannu da zuwa, dama kwallo suke bugawa a harabar gate. Cikin gida suka karasa, a kitchen suka tarar Haj. Asma'u tareda mai aikinta suna girkin dare, don bata barin mai aiki ita kadai tayi aikin abinci, idan ma ranar weekend ne harda Amina ake shiga.
A ladabce ya gaida ta, ta tambayesa lafiyan Babansa, har take zolayansa yayi giba ya kurbo ruwan garinsu, dariya yayi ya ce
"Haj. ai Baba ya iya kiyo".
Sadiq ya ce
"Ai in mutum na Fanfo komai ma zai yi don Baba Iro ba wasa".
Suka dara baki daya.Da daddare ya iske Babansa a dakinshi yana karatun jarida. Daddy ya aje ta gefe, shima zolayarsa ya shiga yi
"Ya Babanka? Dafatar duk suna lafita? Allah dai yasa na samu suruka wannan zuwan".
Kansa ya sosa kana ya ce
"Duk suna lafiya, sun ce a gaishe ku. Ai da saura Daddy".
"Me ne adda saura Aliyu? Ina ce karatu an gama? Aiki kuwa Inshaa Allahu ka kusa farawa, toh me ne da saura? Toh ko auren anka tashi kai zaka yi ma kanka komai ne? Diba dan uwanka har da su d'a kai ko baka ma sa niyar aure ba".
"Inshaa Allah Daddy lokaci ya kusa".
"Toh Allah Yasa".
Ya kara gyara zamansa tareda cire gilashin idonsa, ya kwantar da murya ya ce
"Ni ko Aliyu na ce me zai hana ka diba mata cikin 'ya'yan Babanka wato Iro, ni dai ina maka sha'awar auren 'yarsa ko Fadima ko Meramu, ka ga zaka kara dankon zumunci a tsakani, sannan Babanka zai yi farin cikin haka. Amma in har kana da wacce kake so toh baida damuwa, dama banyi magana da kowa ba a cikin raina nake ta nazarin da shaawar haka".
Ali yayi jim, yayi shiru.
"Ka ga ba abun tilastawa kai ne ba, shawara dai ce Aliyu".
"Daddy wace kuma Meramu".
"'Yarsa mana, diyar amaryarsa Sahiya. Baka ganta ba ne?".
"Eh. Kuma kaman an dinke man baki wallahi ban tambaya ba".
"Kila ko ta je wani guri ne kasan mata da son zuwa biki ko da na barin gari ne".
ESTÁS LEYENDO
KUSKUREN IYAYEN MU
Misterio / SuspensoKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...