KUSKUREN IYAYENMU
Na
U_F & Ashnur❤®
NWA8.
Minti talatin ya kaisa cikin garin Fanfo, kai tsaye shagon Babansa Mal. Iro ya zarce.Murna gun Mal. Iro baa magana da ya ga Ali, baki har baka, lallai Allah ne ke saka so, shi kam ya saka masa son Ali fiye da zaton mutum.
Sai ina ya kan aza da shi haka yake ta rawar jiki da shi.
Suka gaisa Mal. Iro ya tambayesa lafiyar kannensa da iyayensa, Ali ya shaida mashi dukkansu lafiya kalau suke.
Fira sosai suka yi. Kiran sallar magrib ce ta katse firarsu, suka yi alwala, Mal. Ya rufe shagonsa, suka wuce masallaci domin yin sallah.Bayan fitowarshi masallaci suka wuce gidan Mal. A kofar gida suka yi karo da Basiru, cikin murna suka yi musabiha, daga nan suka shiga cikin gida shi kuwa Basiru ya wuce wani guri da zai kai sako.
"A'i! A'i! Fito ga Dana nan ya zo".
Cewar Mal. Yana shinfida masa tabarma da ya gani tsakar gida.
Ali ya zauna dauke da fara'a a fuskarsa, shi kam yana jin dadin yadda Babansa ke rawar kafa da shi, shiyasa yake kara sonsa."Ah ah ah! Kai marhabin lale lale, yau mutanen turai ne a garin namu?".
A'i ta fada tana fitowa daga daki. Ali dariya yayi ya shiga gaisheta, Mal. Ya karba da cewa
"Kawo masa abinci ya ci kafin ya isa masaukinsa".
Ta amsa da toh ta tashi. Mal. Ya shiga kiran Nasiru ya zo ya sawo masa lemun kwalba.Fadima ce dauke da tiren abinci ta aje gaban Ali, kuloli biyu ne ta abinci da ta miya sai kofin silba dauke da ruwan sha ciki.
"Gashi matar Yaya ta ce akawo wa Ya Gadanga. Gata nan ma zuwa".
"Toh madallah".
Cewar Mal. tareda fuskantar Ali, ya kara da cewa
"Kana can aka yi auren Zali da dan uwanka gashi yanzu harda karuwa an samu, sunansa Abdullahi ya ci sunan mahaifinmu shine ake kiransa Bayero".
"Kai masha Allahu. Ai a lokacin auren na kirasa na masa Allah sanya alkhairi, haihuwar ce ban jiba, kila Daddy ya manta ne".
"Toh kasan abubuwan ba kadan ba......".
Matar Basiru Aina'u ta katse su da gaishesu, Ali ya amsa a fara'ance, ya tambayi Bayero ta shaida masa yana bacci.Bayan ya kammala cin abinci suka wuce masallaci sallar isha, bayan sun dawo kuma ya shigar da tsarabar da ya zo masu da ita, dangin kayan abinci ne.
Gidansu dake nesa kadan dana Mal. Iro ya wuce, Daddinsa ya gina shine saboda in sun zo sallah ko wani abu ya kawo su Fanfo, sai dai ba wani kayan alatu bane sosai aka zuba cikinsa ba, dai-dai misali aka kawata gidan.
****Firgigit ta tashi daga baccin da take sakamakon ruwan sanyi da taji a jikinta. A hankali ta tadda kanta sama ta kai kallo ga wacce tasan ita ce kawai wacce zatai mata haka.
Cikin Gadara Jidda ta ce
"Tun ina can nake kiranki amma inaa kina nan kin wani habbare baki kina bacci sai ka ce wata jaka, ko da yake mece ce ke?".
Ta ya mutsa fuska sannan ta cigaba da magana
"Ai jakar ce, zan fita ki gyara min daki kafin na dawo".
Ta juya ta wuce. Inda sabo ai ta saba da irin cin kashin da take fuskanta wurin Jidda.
Cikin mintuna kalilan ta je ta gyara ko ina na dakin tareda feshe shi da turaren daki.
Sannan tayo kitchen din dake baya ta samu Izzatu, zaunawa tayi kasancewar ta tarar da ita da tana fige alayyahu.
"Har kin tashi daga baccin?".
Izzatu ta tambayeta tana kai duba gareta
"Eh".
Tana bata amsa bayan tasa hannunwanta biyu ta matse jikinta da su alamun sanyi take ji, nan take jikinta ya hau bari, cikin azama Izzatu ta saki wukar dake hannunta ta riko Meramu
"Subhanalillahi. Baki lafiya ne?".
Meramu ta girgiza kanta alamun eh. Sakinta tayi ta je gate da sauri tana kwala ma Mani direba kira, shima da sauri ya fito daga dakin maigadi jin kiran da ake masa.
"Lafiya Izzatu?".
Ya ida tambayar yana saka talkamansa.
"Ina fa lafiya, Meramu ce ba lafiya jikinta sai bari yake hakoranta na gabgabgab".
"Ashsha. Toh rikota mu kaita kemis".
Ta koma da sauri ta dauko mata hijabi a dakinsu ta saka mata, kana ta riko ta suka yo gate.A mota Mani ya kaisu Binji pharmacy, aka rubuta magani da allura, ba kudi a hannunsu hakan yasa Mani ya kira Tijjani yaron Abba, don komai na hannunsa, saboda Haj. da Abba sun yi tafiya, shiyasa aka hannunta ma Tijjani komai a hannunsa.
Tijjani ya shaida masa ga inda yake ya je ya karba, nan ya barsu Izzatu kemis ya tafi ya karbo. Biyan kudin Mani yayi aka bata magani sannan akai mata allura suka yo gida.Dakinsu dake baya ta shiga ta kwanta kan katifa. Take bacci yayi awon gaba da ita.
Izzatu ta koma kan aikinta, nan sai ga Inna dingis-dingis tana bombami
"Wai ni me Hauwa'u ta dauke ni ne? Iyinnn... Shi kenan sai ta dinga fita bata sanar da ni ba, wato ni kenan ko oho ce gareta, toh wai ma meye amfanin yan siful sifet(civil defence)? Din da ba zasu hana ta fita ba.... Anya yarinyar nan na so ta ga hawa kuwa?".
"Sai hakuri Inna. Ai kurciya ce".
"Barni da yar banza zata dawo ta same ni. Wai ni kam ina Meramu? Yar albarka yarinyar kirki".
Izzatu dariya tayi ta ce
"Mu kenan bana kirki ba ne Inna?".
"Ta dai fi ku".
"Tana can tana kwana, bamu dade da dawowa kemis ba an mata allura".
"Kai kai kai ashsha! Subhanalillahi. Me ke damunta?".
"Maleriya ce Inna".
"Allah Ya bata lafiya".
Izzatu ta amsa da Amin.A can bangaren Ali kuwa ya shirya tsaf cikin manyan kayansa, shadda ce blue da tasha aiki mai kyau, sai hula kalar shaddarsa sai talkamansa baki da suke sheki da man gyaransu, sai a gogan hannu dake kan wutsiyar hannunshi, sajen fuskarshi luf a kwance, ya yi kyau sosai.
Dama sha biyun rana yake son tafiya, yana fitowa gidansu shagon Mal. Ya wuce kai tsaye.A can ya tarar da Basiru, don wani lokaci su biyu suke tsare shagon, sai dai Mal. ba kowane lokaci yake zama ba.
Bayan sun gama gaishe-gaishensu yake shaida masu zai tafi saboda wani uzuri da ya gifta mashi. Dai-dai lokacin wayar Basiru tayi kara alamun kira ya shigo. Bai dauka ba ya ce da Mal.
"Baba Inyamurin nan ne mai takalma ya kira, zan fada masa jibi zan zo na karba, sai dai Baba wallahi kudin da yasa ma talkamansa sun yi tsada".
"Toh ka fada mashi mana, ai sai ya rage".
Basiru ya dauki wayar ya fara magana
"Kuda aftanen".
Inyamuri ya ce
"Afternoon How are you?".
"Fine sir. Am going to com tomorrow tomorrow to collect za shoes, but gaskiya u hav to sizors d money bcos is to higher cos".
"Ok till you come. Thanks".
"Ehen bye".
Ya katse wayar. Dariya kamar kamar zata kashe Ali, amma ya cije ta kada ta fito su ga ya yi cin fuska.
Sallama yayi masu ya wuce tareda yi ma Basiru alkhairi.A mota sai dariya yake, shi turancin yafi bashi dariya, toh ina amfani kin yi karatu? An saka su tare amma shi yasa tsabar wasa, gashi makarantar basa wasa in yaro bai karatu repeating ake mai, idan aka mai sau biyu na ukku korarshi ake, toh haka ta kasance da Basiru.
Wayarsa ya dauko ya kira Kamal yana son ya fada masa zai zo, ringin biyu ukku ya dauka, yana dauka Ali ya ce mashi
"Am going to com now now".
Yana dariya, shima Kamal dariya yayi ya ce
"What?".
Bai ce masa komai ba ya katse kiran, yana dariyarsa shi kadai.A wurin aikinsa ya iske sa, suka gaisa, Ali ya tambayesa lafiyan iyalinsa, Kamal ya shaida mashi kalau suke tareda cewa
"Wai kasan tunda muka gama waya dariya an nan ina yi, nayi dariya sosai don ka tuno man da Sani uwayen Luv".
"Haba. Hahahah nima dariyar kenan nake yi".
"Ai Sani uwayen Luv wato saboda soyayyar da yake ma budurwarshi, watarana ya je wurinta, tayi ado ta burgeshi, ya rasa wace kalma zai yi amfani da ita ya nuna mata ta yi, sai kawai ya ce kinyi kyau Lobin, kai gaskiya u r za fish in my whole stomach".
Haba mai Ali zai yi in ba dariya, yayi dariya iya dariya, Kamal ya kara da cewa
"Ai in kana zaune da shi cikinka sai ya fashe don dariya".
Cikin dariya Ali ya ce
"Wato Loving shine Lobin?".
"Eh".
Suka sake darawa, Kamal ya kara da cewa
"Ai wurinshi zan kai ka ya koya ma Luv da kalamansa".
"Hahahahha. Ai kam zan so ganin wannan Sani uwayen Luv, kai ko ba komai ai na dau wannan u r za fish in my whole stomach, na samu abun fada ma matata watarana".
Kamal yayi dariya, nan Ali ya bashi labarin wayar Basiru, Kamal yayi dariya sosai ya ce
"Wallahi ilimi da dadi yake bare in ka hada biyu wato boko da na islama, kai gaskiya Basiru bai kyauta ma kanshi ba da yaki yin karatu".
"Bari kawai".

KAMU SEDANG MEMBACA
KUSKUREN IYAYEN MU
Misteri / ThrillerKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...