babi na sha d'aya...

1K 112 8
                                    

  KUSKUREN IYAYENMU.

Na
U_F & Ashnur❤

®
NWA

11.
       BAYAN KWANA BIYU.
Cikin azarbabe Izzatu ke kiran sunan Meramu dauke da fara'a a fuskarta, jin haka Meramu ta saki wankin inner wears din Jidda da take wankewa a bakin famfo sakamakon rashin son wankin washing machine din da Jidda take yanzu.
"Kin ga tsarabar da Haj. ta bani, ta ce ki je ki zabi naki".
Cewar Izzatu tana nuna mata. Jallabiya ce kalar brown mai kyan gaske, cikin taya Izzatu murna ta ce
"Kai wallahi rigar  nan tayi kyau sosai. Allah Yasa a kashe lafiya Amin".
    "Amin nagode. Ki tafi tana falonta tana jiranki".

A falonta ta tarar da ita kan kujera, rusunawa tayi cike da ladabi ta ce
"Haj. gani Izzatu ta ce kina kira na".
    "Dama tsarabarki ce zan baki".
Sai ta jawo doguwar riga daya da swiss atampa biyu, doguwar rigar baka ce, irinta Izzatu sai dai dukkansu adonsu daya. Haj. Rahma ta ce
"Ki dauki wacce ki ke so cikin ukkun nan, wa'anda kika bari sai a ba Mani da Sule su bama matansu".
Cikin murna ta dauki bakar rigar don ta ji tafi son ta. Can ta ji Jidda na cewa
"Ina ke ina bakin abu ga ki bakar macce ai bakin abu sai mu fararen fata".
Haj. dariya tayi ganin Meramu ta aje rigar a sanyaye, sai ga Inna na karasowa dingis-dingis cikin falon, maganar Jidda tayi karaf ga kunnenta ta ce
"Kyaleta Meramu dauki wacce ki ke so kiyi tafiyarki, ko da kike bakar kin fita kyau sosai wallahi, kin ji din ke ba fara ba ce amma koma ai ba zaa ce dake baka ba, wallahi kin fita kyau, ita har wani kyau ne da ita? Dauki ki tafiyarki 'yar albarka".
Cikin kukan shagwaba Jidda ta fada jikin Haj. Rahma, ganin haka Meramu ta fita a sulale, dai-dai nan Abba ya shigo yana tambayar meke faruwa, Haj. Rahma ta yi karab ta ce
"Inna baki dai son yarinyar nan, yau harda fifita bare a kanta?".
Inna ta ce
"Ba sonta ne bana yi ba halinta ne bana so, yaron nan ga diba irin cin fuska da tayi ma Meramu, uwarta na ji maimakon ta tsawata mata sai ma dariya take, duk kun lalata yariya bata ganin kowa da daraja".
Cikin daurewar fuska Haj. Rahma ta ce
"Ba wani nan Inna ke dai ba tun yanzu ba kin tsani Jidda baki dai sonta, na rasa sanin dalili".
Abba bai bi takan Inna ba ya shiga lallashin Jidda yana shafar bayanta tareda gogen hawayenta, daga bisani ya ce
"Sorry dear, ki bar saurin fidda hawayenki bana son ganinsu, in bamu baki gata ba waye zai baki? Shalelena me ki ke son in baki, iyee 'yar gatan mamanta da babanta?".
Murmushi tayi tana dubansa ta ce
"Dad sub din wayana ya kare da na dstvn dakina dazu ina cikin kallo".
"Ok. Ki tafi bedroom dina, cikin bedside drawer akwai bandir din dubu-dubu a ciki ki dauki daya, ai 100k sun isa ayi sub din ko?"
Cike da farin ciki ta girgiza mashi alamun sun isa, ta wuce da nufin zuwa dakin Abba.

Inna kam kasa furta komai tayi baki a sake tana kallonsu, Abba ya karasa wurinta ya ce
"Inna ki bar ma Jidda haka, yarinya ce kurciya ke cinta, duka-duka nawa take? 20+ fa, don Allah Inna ke bar matsama yarinyar nan"
   "An matsa mata, na ce an matsa mata".
Inna ta fita tana bombami tareda tirr da wannan abu.

Agaggauce ta gama wankinta ta ida sauran aikin da zata yi, ko sallama kasa zuwa tayi ma Haj. ta yi saboda fargabar haduwarta da Jidda, ina lafiyar kura bare an taba ta. Gidansu Habiba ta je inda ake ma Inna dakan kumbar kunu, da suka kulla kawance tsakaninsu.
Cikin 'yan mintota ta isa gidan kasancewar bayan gidansu Jidda gidansu yake, don na su Jidda a bakin titi yake, na su na daga ciki lungu. Ko da ta je ta tarar tana wanke-wanke, da murna Habiba ta saki kofin dake hannunta ta rungumo Meramu tareda fadin
"Oyoyo Meramu".
  "Ah! Zaki balla ni fa".
"Hahahha duk cikin murnar zuwanki ne".
Suka dara
"Ina Mama?".
Cewar Meramu tana kai kallo ga kofar dakin da take fuskantarta.
  "Ta fita amma ba nesa ta je ba".
"Allah sarki. Bari na taya ki".
   "Aa ai nama kusa kammalawa, har kin tashi aiki?"
"Eh".
Ta bada amsa tana sake zuba wasu ruwan dwauraya. Habiba ta jinjina
   "Yau kam kin yi sauri tashi aiki, da wuri zaki koma gida yau don hudu saura yanzu".
Nan Meramu ta bata labarin abunda ya faru har ta nuna mata tsarabar, mere baki Habiba tayi ta ce
"Ai dai kin kusa hutawa in ta koma makaranta".
   "Haka na ji, ashe ma shekarar karshe take a jami'ar dake sifuros(Cyprus) din".

Haka dai suka cigaba da fira suna aikinsu har suka kammala wanke-wanken harma da sharan tsakar gida dai-dai lokacin ana kiraye-kirayen sallar la'asar. Sallah Meramu ta ida ta ce ma Habiba dake dannar waya
"Ki zo ki yi sallah ni kam ki rakani in tafi gida".
   "Hutu nake mu tafi kawai".
Da ida maganarta tana jawo hijabinta dake sargahe kan taga.

Suka tafi bayan Habiba ta rufe gida. A hanya Meramu ke ce mata
"Hahaha kin san da kika ce kina hutu sai na tuno da jini na na farko. Ban mantawa na tashi baccin rana da matsanancin ciwon mara, na dinga juye-juye ina kuka, tashin da zanyi naga jini ya zaryo a kafata, na yi saurin komawa kwance. Kuka nasaka da karfin gaske ganin jini ya zubo min, saboda rashin sanin daga ina jinin ke fitowa don a sanina ban fadi ba kuma ban yanke ba. Na shiga fadin wayyo ni Umma zan mutu! Wayyo mutuwa zan yi! Da karfi fa nake kuka, sai gata da gudu tayo kaina, na ce mata na bani mutuwa zan yi, shikenan yau tawa ta kare, Umma jini yana fitowa kuma bansan ta yaya ba, ina fadin haka, ta dago ni sai naga tana dariya, sai na kara saka kuka, nan ta lallashe ni ta duraman ruwan zafi nayi wanka, na gyara jikina, ta yaga zaninta taman kunzuku, nan ta shiga yi min bayanin wai girma ne ya zo man, ta shiga yi min nasiha tsare sallah da guje ma namiji indai ba muharramina ba ne, da dai sauran nasihohi. Bayan zuwanmu ma garin nan nayi Umma Ladidi ta bani kunzugu na zamani(pad) gaskiya birni akwai cigaba".
Habiba dariya ta yi sosai sannan ta ce
"Kai kowa dai da yadda yake, ni kam koda ya zo man nasan komene ne don an muna bayaninshi a makarantar islamiyya".
   "Mu ma an fada sai dai bai muna bayani yadda ya kamata ba, ina aji biyu na furamari na fara".
"Aji biyu fa kika ce?"
    "Eh. Sai da muka shekara goma aka samu boko, na kare a shekara sha shidda, yanzu kuma ina cikin ta sha bakwai, sai dai a iya furamari na tsaya, amma islamiyya kam tun muna 'yan dugaduggai ake samu, shiyassa kam ta fanin muhammadiyya kam Alhmadullilah".
"Ashe shekarun mu daya".

Fira suke har suka isa kan titi suna jiran abun hawa, Habiba ta dafa kafadarta ta ce
"Kin ga har zan manta, an kawo man I see I love?".
Ta ida maganarta tana rufe fuskarta da tafukan hannunta
   "Me ye kuma hakan?".
Meramu ta tambaya tana fuskantarta
"An ganni ana so, a al'adar garin idan saurayi ya ga yarinya yana so, duka bangare biyu suka aminta, shine ake kawo dangin alawa(minti), goro da dai sauransu, iya dai karfin mutum. Baa raba ba da kin ga naki kason".
Murna sosai Meramu ta tayata tareda sanya alkhairi. Fuskarta dauke da rashin walwala ta ce Habiba
"Wai ni kam mummuna ce?".
"In ji wa? Ai ni da ina da kyanki da anga abu wai shi jan aji. Wane munafinkin ne ya ce haka?".
  "Toh naga duk sa'anina suna da mashinshini a garinmu ma wasu har sun yi aure, ni kam wani bai taba furta kalmar so gare ni ba, kila ko don ni din mummunace a nawa zato".
Ta ida maganarta cike da damuwa, jikin Habiba yayi sanyi, ta tausayawa Meramu, ashe abun na damunta.
"Komai lokaci ne, wani jingirin alkhairi ne".
Nan dai ta cigaba da sanyaya mata rai har ta samu mashin ta hau.

Vote👌 and comments

 KUSKUREN IYAYEN MUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora