Mutuwa mai yanka kauna......

1.9K 102 28
                                    


KUSKUREN IYAYENMU.

Na
U_F & Ashnur❤

®
NWA

Shafin naku ne Nty Maijidda Musa, Nty YBK, Nty Sady Jegal, da sauran yan MU SHA KARATU.

17.
Tari take sosai, yi take tayi har sa'anda Likiita ya zo ya saka wasu ruwan allurai cikin drip dake bi ta hanyar jijiyoyin jikinta, sannu a hankali ta daina har ta samu bacci cikin iyawar Allah. Likita ya neme da Baba ya biyo shi ofishinsa, tareda Kamal suka je Likita ya mika mashi takardu ya ce
"Baba ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai zo da sauki, a saye wa'ennan magungun nan da allurai da aka rubuta, sannan zaa yi foto da kafarta da ta jimu don gano tabbatacen jimuwar gurin".
   "Toh Likita. Mun gode".
Cewar Baba yana share zufan fuskarsa ta hannayensa.

Bayan sun fito ofis din suka karasa inda Ali yake tsaye.
"Baba da sauki ko?".
Ya fada cikin nuna damuwarsa.
   "Eh toh da sauki zaa ce".
Baba ya idasa maganarsa ya jingina kansa ga bango.
"Baba addu'a zamu yi, don Allah kada ka daga hankalinka".
   "Gadanga idan ban damu ba ya zan yi?, Allah ne kadai masanin yadda nake ji a raina, zuciyata kamar zata tarwatse saboda kuncin da nake ji, na cuci Sahiya, na wofintar da ita da 'yarta, ni yanzu har me zan ce ma Meramu? Da wane ido zan kalle ta Gadanga?".
Zarrrr kwalla suka gangaro masa ya yi saurin gogewa. Iya raunana zuciyar Ali ta raunana, haka yake da saurin rauni kamar macce. Baba ya dafa kafadarsa ya ce
"Ina fatar Meramu bata san komai ba?".
Ya girgiza kansa alamar eh
"Yauwa. Kada a sanar da ita, kada hankalinta ya tashi gata ba lafiya ba, An shi kai takardar gwajin, sai dai duk ta yayyage amma dai akai haka Likita ya gani, ni ma zan zo dubinta idan Ya Amadu ya zo".

Ali ya amsa ya wucewarsa shi da Kamal. Lokacin sallar laasar yayi don haka suka fara wucewa masallaci suka yi sallah.

Sun tarda Matar Kamal ta zuba mata abinci tareda tsiyaya mata lemu a cup.
"Yauwa Aliyu gara da ka zo, may be ko don ganinka yasa ta ci, bata son cin abinci, toh taya zata samu karfin jiki da yunwa?".
Ta ida maganar tana sake mika ma Meramu abincin.
  "Toh ai yanzu tunda gashi ya zo sai ta ci. Ni nama gano ciwon nan......".
Kamal ya fada cikin zolaya
   "Uhummm! Ka fada kaima, yarinya har tasan ciwon so, kwana biyun da bata ganni ba shine harda su zazzabi, oh ni! daga gasa fa Mom Ilham shikenan ta kai son Aliyu har cikin balgon zuciyarta tun kan na ce ina son ki, toh ina ga na dube ta na ce ina son ki".
Ya yi maganar shima cikin zolaya yana kallonta. Kasan hijab dinta tasa ta rufe fuskarta saboda tsabar kunyar da taji. Ita kam ba ciwon so ba ne, sai dai ita kanta ta san tana jinshi a ranta ba tareda tasan akwai kyakkyawar yan uwantaka a tsakaninsu ba, kwarai ta na jin wani abu daban dagane da shi
"Maryam ki ci, ko bakya son jallof da hadin koslo ne? Ko a zuba maki ita kadai ba tareda koslo ba?".
Cewar Matar Kamal.
   "Bar ni da ita, na iya dore ma".
Ta yi saurin kallonsa tana zaro ido, shima kallonta yake cike da tsananin tausayinta. Jin haka yasa ta karbi plate din sai dai bata soma ci ba, sai juya spoon din da take. Ta rasa dalilin faduwar gabanta akai-akai, fatanta daya Allah Yasa dai lafiya.
A hankali ta soma ci cikin natsuwa. Ci take ba don dadi ba sai dai yunwar da take ji, sai son ganin Ummanta da take.

Takarda gwajin ya bada a lokacin da Likita ya zo, ya tabbatar masu da malaria ce, sannan ya rubuta wasu allura.

Sai bayan Magrib Daddy da Mamy suka iso, ta hanyar wayar da su da Mal. yasa suka isa inda suke.
Da ka ga Mal. kasan yana cikin halin damuwa. Daddy yayi ta bashi magana masu kwantar da hankali, Kamal yasa yayi mashi jagoranci zuwa ga Likitan dake duty a lokacin. Bayani sosai Likita yayi mashi da gwaje-gwajen da aka bada ayi, bayan fitowar Daddy daga ofis din Likita suka je dakin da aka kwantar da Umma. Komai na jikinta ya saki, gaban Mal. ya fadi ganin idonta kafe suna kallon sama
"Innalillahi wa'inna ilaihin rajiun".
Haka Daddy ya furta. Likita yayi sauri ya dubata, tabbas rai yayi halinsa, shafe idanunta yayi ya jawo zanen dake rufe ga jikinta izuwa fuskarta.
"Allah yayi nasa iko".
Cewar Likita yana dubansu.  Mal. sai da ya fadi zaune dirshin yana kuka, Mamy ma kukan ta soma.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 17, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

 KUSKUREN IYAYEN MUWhere stories live. Discover now