tsuntsun daya ja ruwa..

1.1K 124 50
                                    

KUSKUREN IYAYENMU.

Na
U_F & Ashnur❤

®
NWA

14.
*Sha biyun dare*
Sai a sannan jidda ke sallar ishaa cikin kankanin lokaci tayi ta, dama haka Jidda ke sallah koyaushe, sharp sharp ko raka'a nawa ce kuwa.
Ta kuma cikin bargo ta kankame jikinta, jin cikinta sai kukan yunwa yake don haka ta sauko da zumman zuwa kitchen.
Tea ta hada ta barshi nan kan loka ta nufi firiza dauko swan, ko da ta juyo daukar tea babu tea babu mafarin shi, firgici da ban mamaki hadi da tsoro ya kamata, ta duba gefe da gefe bata ga inda ya zube ba. Da sauri ta kai dubanta ga windo dake bub-bub-bub da karfi da karfi, lokaci guda kuma drawers na kitchen na bude kansu suna rufewa da sauri-sauri, kwas-kwas ta ji takun tafiya daga cikin falo, cikin tsoro tayo falon, kalle-kalle take gaba da baya bata ga mutum ba, tsoro ya cika ta. Can ta ji takun tafiyar a matattakala, ta bi sahun takun cikin sand'a. Takun take bi har ta isa cikin dakinta, tana shiga taji kofar ta shiga lock, ta ja ta ja murfin kofar amma sam ta kasa budewa.
Ji ta yi an makalo hannu kan kafadarta, ta juyo da sauri nan ma bata ga mutum ba amma tana jin nauyin hannun a kafadarta, kuka wiwi Jidda ta shiga yi. Aka dauke hannun. Can kuma daga gefen gadonta ta ji sautin kuka na fita, ta karaso ganin me ke kuka, sifar macce karama ta gani cikin fararen kaya, ta soka kanta cikin cinyoyinta sai faman kuka take da karfin gaske, nan ta fara sheshshekar kuka da kuwa mai kara, take komai na dakin Jidda ya fara rawa.
Zirrrrr ta saki fitsari a wando ga hawaye shabe-shabe a fuska.
Ta yo kofa da sauri da nufin fita, ta yi rashin saa kofan a kulle take har yanzu. Dafe kuncinta ta yi sakamakon wawan marin da aka saukar mata
"Na shiga ukku, wayyo Allah".
Ta fadi tana kuka
"Hahahhahahhahaha".
Can aka soma dariya kala-kala.

"Iskanci banza iskancin wofi, sai na ci kaniyar habiba gobe, bama aljannu ba ajunnunno. Mtsw".
Ita kadai ke bombaminta yayinda ta cire kaya da nufin wanka kan ta isko Abba a dakinshi.
Zaune ta yi bakin gado tana latsa wayarta(wacce zata shiga wanka ta bingire ga latsan waya). Ji tai ruwa na zuba cikin baye shaaaaaa, ta aje wayarta ta shiga ta kashe famfon ta dawo cikin daki, zaunawarta kenan ta sake ji ta je ta kashe, ta dawo zata zauna kenan ta kuma jin zubarsu, ta yi tsaki ta je ta kashe fanfon, tsaye ta ji kan fanfon dake kan zinc ta tsaya ta gani me ke kunnasa, zarrrrr taji abu na zarya a fuskarta, tasa hannu ta kakkabe, ta sake ji ta kuma kakkabewa. Ta nufi madubi ta zumman duba mene ne. Me zata gani? Mussa(mage) baka kirin a bayanta, cikin firgici ta juyo bayanta, wayam bata ga komai, ta sake kallon madubin ta gansu, wannan karon biyu ta gani, da gudu ta fito bayen har towel din dake jikinta na neman sabule mata. Dakin Abba ta je, ta tarar ya kwanta ya ja bargo izuwa wuyanshi, haye gadon ta yi ta kankamo shi gam, fadin take
"Alh. aljannu sun dira a gidan nan".
Juyowar da zai yi ta ga mutum ya washe baki yana dariya da hakoranshi zagam-zagam, idanuwanshi jajaye, ta sake shi tareda watsa kuwa mai karfi, bat aljanin ya bace, zirrrrr Haj. Rahma ta saki fitsari, tareda kankame kanta. Abba ya shigo dakin yana waya, bayan ya kare ya ga Haj. kwance, tayi rufa da bargo. Bargon ya yaye yana fadin
"Har kin kwanta, gaskiya ki tashi don hakkina na zaki bani".
Hannunsa da zai kai jikinta ya ji jikinta da sanyin ruwa, ya kai idonshi kan katifar ya ga tayi jagam, sai mamaki ya cika shi ta ina ruwa suka fito, zaunawa yayi kusa gareta, sai ya ji zarnin fitsari na tashi
"Subhanalillahi! Fitsarin kwance kika yi godai-godai dake Rahma?".
Ya bubbugeta a hankali da ta tashi bacci, bai san idanunta biyu ba tsoro ne yasa ta rufe idanunta.

Ganin ya matsa mata da ta tashi, yasa ta tashi zaune, amma idanunta a rufe
"Wai meye haka ne?".
Tsaki ya ja ya koma kan wardrobe, jallabiyarsa ya ciro da zumman sawa, nan ta bude idanunta a hankali.

Mata biyu ta gani cikin fararen kaya gashin nan nasu har baya, cikin sifar dodanni, matan babba da karama, karamar sai kuka take tana fidda hawayen jini, yarinyar na nuni da inda Haj. take, hakan yasa babbar nufo inda Haj. take zaune, Haj. ta tashi da gudu tayi wurin Abba ta kankame shi, towel din ma can kan gadon ta barshi sakamakon sabule mata da yayi, ran Abba ya baci, cikin fada ya fara magana
"Wai me ke damunki ne Rahma? Tumbur fa kike? Ni dai cika ni".
Ya zame jikinshi da nufin dauko mata, kasa cewa komai ta yi sai kuka da take. Kara kai dubanta tayi ga inda suke, matar ta gani ta dauki towel din ta share ma karamar hawaye da shi, sai kuma suka bace bat
"Alh. Kada ka taba towel din nan!".
Ta fada da karfi yayinda zai dauko mata, cak Abba ya tsaya cikin mamaki, jin an kwan kwasa kofa yasa ta yi sauri ta zira jallabiyar Abba.
Zai bude ta yi saurin rike hannunshi, kwace hannunshi ya yi cikin bacin rai. Bude kofar yayi bai ga kowa ba, fitowa yayi yana dube-dube, can kuma ya ji ana bubbugar kofa daga cikin dakin Jidda.

Tafe yake Haj. na bin bayanshi, murda kofar dakin ya yi ya bude, dakin a hargitse, duk abunda ke gilashi a watse yake
"Jidda! Jidda!".
Abba ya shiga kiranta sakamakon ganinta da bai yi ba. Butbuttutut.... Ya ji alamun ana gudanawa a baye, kafin ya yi yunkurin zuwa bayen sai ga Jidda ta fito a rarrafe. Karfinta ya har kare saboda gudawa, kumatunta sun kumbura saboda marurrukan da tasha.

*needs more vote*

 KUSKUREN IYAYEN MUWhere stories live. Discover now