KUSKUREN IYAYENMU
NA
U_F & Ashnur4.
"Abba jiya wallahi baka ga wani bagidaje ba abun ban dariya, ba zaka kosa da kallon abin dariyarsa ba, wallahi he is so funny, shiyasa na bata lokaci wajen taya su sashi abin dariya, shi wai agun babu wanda yake so sama da ni, ni mamakin ma inda ya samu gate pass da abokansa har suka samu shigowa wurin nake yi".
Nan dai ta cigaba da ba iyayenta labarin abubuwan da suka wakana su kuma sai dariya suke yi. Dama iyayen Jidda kansu ba wai ilmin addini ya wadace su ba, sunfi sha'awar rayuwar nasara, to haka Jidda itama ta taso.
Koda take karama Inna ce kadai ke matsa mata zuwa islamiyya inka ga Jidda taje islamiyya sai Inna ta korata da bulala, tunda ta girma kuma saita botsare tsoron Inna da take yi da saita daina, shiyasa sam! Basa shiri. Inna ta tsani tsarin rayuwar da Abba ya daukanma kansa gaba daya rayuwarsa ta canja daga tarbiyan data bashi, tunda ya ga ya fara samun abin duniya, tunda ya fara hulda da masu jajayen kunne (cewar Inna). K'ari da kuma matar banza daya samu. Shiyasa koda aka haifi Hameed Inna ita ta daukeshi ta rikeshi tareda gina masa rayuwa bisa tarbiya me kyau.
Halin Hameed shi kwata-kwata ba iri d'aya bane dana Jidda shi yana son talakawa akasin Jidda da iyayenta wa inda suka dauki talaka wawan mutum ne mara yanci, zaka iya takasa a duk lokacin daka so ana su fad'in. Inna nason Hameed sosai dukda bayan ya girma an turashi makaranta waje amma Hakan besa halayyarsa sun canza ba, ya riga ya sami tarbiya daga tushe!. _Dama kyakkyawan tarbiya ko mummuna tana samuwa ne tun fil'azal
Tarbiyan yaro tana farawa ne tun daga ciki, zuwa haihuwarsa har girmansa, amma iyaye dayawa basu san haka. ba. Kana fara koyawa yaro ya san yi ya san bari tun daga lokacin da yake shan momma, tun kafin ya fara magana, amma KUSKUREN IYAYENMU musamman mata sai ka ji yaro yayi abu ace wai baza a kwabe shi ba sai ya girma, ai beyi wayo ba, yara na fara koyan rashin ji ne tun daga barna yaro yayi barna baza ace bari ba, yayi tsokana baza ace meyasa ba, to shi yaro da duk abinda ka koyamai dashi yake tashi.
In ya san muryar bari lokacin da yake barna to fa ya rike inko be sani ba ba zai taba sani ba, tarbiyar yaro tamkar zane ne akan dutse kaman yadda yazo cikin wani hadisi (karatun yaro karami tamkar zane ne akan dutse, shi kuma babba tamkar yin zane ne asaman ruwa)_Su na cikin fira sai ga Hameed ya shigo, friut din da aka jera cikin plate din dake centre table ya dau apple, sai da ya gutsira sannan ya dubi Jidda ya ce
"Sis ga fa mutumin nan na jiya ya zo".
"Sure?"
"Yeah"
Rufe bakinta kenan shigowar Inna. Dingyil-dingyil tana fada
"Ina sam! wannan tsari ba na son shi, a ce in mutum ya zo gidan nan sai yan siful sifen(civil defence) su hana shi shigowa. Tir! Da tsarin fararen fata(turawa). Kai ku shigo".
Maganar da ta ita yasa suka dubi kofar shigowa. Gadanga ne da wani dattijon mutum dake sanye da manyan kaya da hular taba ni ka ji hadisi ga tarin geme. Dattijon ya mika ma Abba hannu suka gaisa, Gadanga ya mika na shi kenan Haj. Rahma ta ce cikin fushi don ranta ya sosu, a zatonta jajeme-jajemen da Inna ta saba jawowa ne don Abba ya taimaka masu da wani abu yasa ta ce
"Wai ku su waye?!".
Tsawar da tayi ne yasa Gadanga maida hannunsa ya dan ja baya, cikin rashin sani ya ture kofin lemu dake gefen Abba. Wani wawan tsaki Haj. Rahma ta ja ta ce
"Kai! Duk yadda kayi da jaki sai ya ci kara, duk inda suka je sai sun nuna halinsu na gidadanci".
Fyace majinar da Inna tayi yasa hankalinsu ya koma kanta, tuni Inna ta fara matsar ido.
'Ta fara abunnata'
Cewar Jidda cikin ranta tana ya motsa fuskarta.
"Inna lafiya? Ko jikin ya tashi?"
Abba ya fada cikin saurin murya, don yana matukar kaunar mahaifiyarsa, duk abun Haj. Rahma ta taba Inna sai taji ba dadi a wurinsa, sam baya dauka.
"Wannan zagi haka Rahamu? Anya Rahamu kina so kiga hawa?"
"Toh Inna kasa kike so ki gani?".
Cewar Hameed yana dariya.
"Ungo nan".
Dattijon yayi gyaran murya ya ce
"Ayi hakuri Hajiya".
Shima Gadanga ya bada hakuri cikin girmamawa. Inna ta ce da Dattijon
"Malam muna saurarenka".
Ya gyara zamansa sannan ya fara magana
"Jiya a masallaci wani bawon Allah ya turo da takarda dauke da tambaya shin in ya saki matarshi daga baya ya ce da wasa ne, shin aurensu yana nan ko ko ta saku? Shine na bashi amsar tambayarsa. Bayan na kammala bada karatu ne sai ga Gadanga ya zo man da tasa tambayar, ya matsayin auren da ya cika sharuddan aure amma da wasa aka yi sa? Shine na bashi amsa kamar haka.
Aure ya kullu matukar aka cika sharudda shidda.
"Hahahahaha ka ji wani rainin wayo Alh."
Abba yayi murmushi ya ce
"Ta ina aure zai yuyu bada sanina ba? Wannan ai shirme ne, wai me yasa bakwa da tunani ne? Abunda aka yi cikin wasa shine zaka ce ya kullu?".
"Kasan bakauye bai san ainahin abunda turawa ke nufi da April fool ba".
Haj. Rahma ta ida maganarta yana mere baki. Dattijon ya cigaba da magana
"Tabbas aure ya kullu, don aure ba abun wasa bane. Da farko dai aure yana tabbata ne idan aka cika sharudda shida. Sharuddan kuwa su ne; na daya. A samu ma’aurata biyu, namiji da mace, wadanda ya halatta a daura masu aure a shari'ar musulunci.
Na biyu. Waliyin mace: ya aurar da ita ga wane. Shi kuma ango ya ce ya karba ko kuma wakilinsa ya karba masa a madadinsa.
A shari'ar Musulunci mace ba za ta iya aurar da kanta ba, sai dai waliyyinta. Domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallama ya ce: ﻻ ﻧﻜﺎﺡ ﺇﻻ ﺑﻮﻟﻰ Ma’ana: Aure ba ya tabbata sai da Waliyyi.
Waliyyi a nan shi ne mahaifinta, ko kane ko wan mahaifinta, ko kaninta namiji, ko yayanta namiji, ko kuma 'ya'ya mazan da ta haifa da sauransu. Kuma hadisi ya tabbata, Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallama ya ce duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyyinta ba, to, auren ta batacce ne, auren ta batacce ne, auren ta batacce ne (ya fadi haka har sau uku)… A wani hadisin kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallama ya ce: ﻻ ﺗﺰﻭﺝ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ . ﻭﻻ ﺗﺰﻭﺝ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻧﻔﺴﻬﺎ …
Ma’ana: Mace ba ta aurar da mace kuma mace ba ta aurar da kanta… Wannan hadisin yana nuna mana cewa mace ba za ta zama waliyyiyar wata ba, ko da 'yarta ce ko kanwarta ko 'ya uwarta. Haka kuma ba za ta aurar da kanta ba.
(Don haka ne muke kira ga ‘yan uwanmu musulmi da su guji al’adar nan ta turawa, idan dangin mace ba sa son Ango sai su hada baki su gudu, su je wani guri wasu su daura musu aure, su Sani lallai auran su ba aure bane kuma zaman zina suke yi).
Na ukku. Wakilin ango: wanda zai karbawa masa aure ko kuma shi ango da kansa.
Na hudu. Akalla shaidu guda biyu wadanda za su yi shaidar aure a tsakanin ma’auratan.
Na biyar. Sadaki: Za a iya bayar da shi, ko wani abu daga cikinsa, kafin daurin auren, ko a lokacin da za a daura, ko kuma bayan an daura..
Na shidda. Sigar bayarwa da karba. Waliyyin mace ya ce ya aurar da ita ga wane. Shi kuma ango ya ce ya karba ko kuma wakilinsa ya karba masa a madadinsa..
Sigar daurin aure takan zo da lafazi kamar haka, Na aura maka ko kuma na halatta maka ita, dukkan wadannan lafazai sun tabbata daga bakin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallama yayin da ya ce da wani daga cikin sahabbai (alhali yana daura masa aure da wata mata), “Na mallaka maka ita”. Kuma wannan lafazin bai tsaya ga Larabci ba kawai, duk lafazin da zai iya nuna bayarwa da karba ya halatta a yi amfani da shi, ko da wane irin yare ne kuwa.
Wannan shi ne abin da Ibn Taimiyya ya fada a cikin fatawarsa. Wannan zancen kuma, shine mafi rinjaye a wurin mafi yawan malamai.
Misali a harshen Hausa, za a iya cewa, na mallaka maka ita, ko na aura maka ita, ko kuma daga yau ta zama halal a gare ka, da sauransu. Haka kuma mai karba zai iya amfani da lafazi kamar haka, na karba, na amince ko kuma na yarda da sauran lafuzzan da al’adar gari ta saba amfani da su wadanda suke nuna cewa an mallaka maka ita kuma ka karbi auren. Saboda haka kada a tilastawa waliyyai (na ango ko na amarya) cewa dole ne su fada da Larabci. Kuma ya kamata a fahimci cewa auren ba zai taba kulluwa ba, face an yi amfani da sigar aurarwa da kuma ta karba.
Don haka da waliyyin ita Jidda ya ce na baka, sai waliyyin Gadanga ya ce ya karɓa, kuma kuna nufin da wasa Ku keyi, toh ba zaku bini bashin rantsuwa akan wannan aure ya kullu daram".
Cikin firgici kuwa Jidda ta zaro ido barin ma Haj. Rahma da gabanta yayi mummunan faduwa. Malam ya cigaba da magana
"Ko da kuwa minti biyar da haihuwanta, abinda zai warware wannan aure kawai shine saki.
Kamar ka ce ka sake matarka daga baya ka ce ai wasa ka keyi to ya zama gaske sai dai in akwai sauran Igiya sai ka dawo da ita. In dai babu kuma to ta tafi kenan, In kuma kayi taurin kai ka zauna da Ita a haka zaku yita zina ne kawai kuna Haihuwan Shegu Allah Ya Sauwake".
Inna tayi ajiyar zuciya ta ce
"Alhakimu Allah. Uhummm yaro nan ka ji wani ikon Allah ko? Allah ya saukar da tashi hikima cikin auren Hauwa'u. Yo dama me zaa yi da Dan iska?".
"Sajid din ne Dan iska Inna?".
Haj. Rahma ta tambayi Inna tana dafe kirji
"Shi din mana, ranar ba Allah ne ya tsare ba daya b'ata min rayuwa".
Sai ta walwale habar zaneta alamun yan matse-matsen hawayen ya tashi. Ta ci gaba da magana
"Wai ace tsohoi-tsohoi dani amma yaron nan ya zo yana rungumata, da kadan fa ya sumba ce ni, inyi...to me yake nufi dani? A haka zamu dauki yar tamu mu bashi aure?, wayasan iya mata nawa yake runguma, tunda dai ace ni duk da tsufana amma hakan bai hanasa rungumata ba, oh ni! jikanyar Tumba! Da mutuniyar banza ce ni daya lalata ni a ranar".
"Haba Inna mai yasa kike Irin wannan kalamai? Shi fa rayuwar turawa ne da shi, wannan bakomai ba ne"
"Haba! Gaske ashe har da arnakku yake hulda, shiyasa ranar harda suna irin na su na arna ya kira ni. Yaron nan ta ya ya za mu so surukuntaka da wannan Irin? Alhamdulillah Allah ya huce mini haushi daya hada Jidda da mijin arziki irin Gadanga, kun ga fa can gun wa'azi yake har yaji Malam na amsa tambayoyi shima yayi nasa tambayar, in ba mutumin arziki ba wake zuwa wajen taron wa'azi? Ai sai yan arziki Irin albarka. Kai! Allah dai ya maka albarka Gadanga".
"Inna don Allah ki dakata mu ji da abu d'aya mana, kin wani rik'e wai suruki, ni ban gane abinda ke shirin faruwa ba ne, wai Malam yanzu kana nufin dagaske kake aure ya kullu tsakanin wannan abin da Jidda?".
Haj. Rahma kenan ta idasa maganarta tana mai nuna Gadanga da bakinta.
"Tabbas ai yama wuce wai, bisa hujjojin dana kawo mu ku a shar'ance".
"Inaa! Sam! Hakan ko ba zai taba yuyuwa ba. Dan talaka da 'yata? Can you imagine? Impossible!".
Abba ya idasa maganarsa yana bugun hannun kujera. Malam ya ce
"Alh. yarda yariga ya rage naku ni nayi me wuyar tunda na isar mu ku da sako kuma na sauke nauyin hakkin daya hau kaina, yaron nan ya zayyana min duk yanda suka yi, a shari'ance kuma aure ya tabbata, shiyasa ma na biyosa don na zo na mu ku bayani in fidda hakki, Jidda mata ce ga Gadanga, haka ma Gadanga miji ne ga Jidda, kowannensu hakki ya rataya gareshi. Maasalam".
Malam ya yi sallama ya fita dama yana da wani uzuri. Gadanga kam da Jidda kamar ruwa ya cinye su, Gadanga yayi shiru kansa a kasa. Bangare daya ya ji dadi da Allah ya nuna masa mafarkinsa ya zama gaskiya, sai dai bai taba sa ran mafarkinsa watarana zai zama gaskiya ba don yasan Jidda tayi masa zarra ta ko'ina. A wani bangaren kuwa yana ganin kurar da zata ta so don shi kam komai zaa mashi ba zai sake ta ba. Maganar Haj. Rahma ce tasa ya dawo daga tunanin da yake.
"Kada ka daga hankalinka Alh. Dama tsabar kwadayi ne, yanzu dole ya walwali auren nan".
Ta jefa mashi bandir din 'yan dubu-dubu guda biyu tareda takarda da biro tareda fadin
"Idan ka rubuta mata sakin, toh wannan naka ne".
Cikin sanyin murya Gadanga ya ce
"Haj. Kiyi hakuri ba zan iya sakinta ba".
"Saki Rahamu? Ai aure ya dauru daram! Ba kuma me kwancesa in dai ina raye, ba gudu ba ja da baya, Jidda sai gidan Ali Gadanga kusar yaki!..".
"Inna ki bari don Allah".
Cewar Abba yana kai kawo cikin falo.Ashnur pyar❤ naam hei mera💃🏻💃🏻💃🏻
Vote and comments
YOU ARE READING
KUSKUREN IYAYEN MU
Mystery / ThrillerKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...