KUSKUREN IYAYENMU
Na.
U_F & Asnur❤®
NWA15.
Da kyar suka ga safiya, Jidda kam sai da Abba ya kira Dr. aka sa mata karin ruwa, saboda tsananin galabaitar da ta yi. Haj. ma wani wahallan bacci da Shiga yi.
****Karfe goman safe sai ga A'i ta dawo dauke da 'yan komatsai, Mal. na kwance a tsakar gida kan tabarma. Daki ta shiga ta aje kayan tareda mayafinta kana ta fito, wurin shi ta zauna daga gefe, kallonta yayi ya girgiza kanshi cike da takaicinta, can ya nisa ya ce
"Ina kika je kwana biyun nan?".
"Ai dama nasan tambayar da zaka yi kenan, Mal. kana da damuwa wallahi. Toh bikin yar dan uwan Ladiyo dake Kaduna muka je, ka dai san yadda Ladiyo take a guna, bai dace a ce ta kawo man alawar gayyata in ki zuwa ba".
"A'i kin san fa ban ji dadi amma kika iya tafiya ki barni sai yaran nan kaita dawainiya da ni, toh wai wa ya baki izinin zuwa?".
"Zamana a gidan shi zai sa ka ji sauki ne Mal.? Ko ko ya abin yake? Yau ka ji min Mal. da wata magana".
"Na ce da izininwa kika je?"
"Da izininka. Na fada maka kila dai ko baka fihimce ni ba"
"Ni?"
Mal. ya zaro ido yana sake fuskantarta, Nasiru dake dayan gefen Mal. ya ce da A'i
"Innanmu ba kyau karya fa, kawai ki bashi hakuri, kai kuma Baba don Allah kayi hakuri".
Ya ida maganar cikin marairaicewa. A hasale ta ce
"Yau ga dan iskan yaro, shege, ni zaka gayawa ba kyau karya? Iyee shege dan iskan banza, in ka ji muna magana ka kuma sa baki ni da kai ne gidan nan".
Ta tashi fuuuu ta koma daki. Bakin cikin A'i yayi mashi katutu a rai, ya rasa yadda zai yi da ita, ta kai matakin da tafi karfinshi yanzu. Hakuri Nasiru ya koma bashi ya ce da shi bakomai.Nasiru ya fita banbam da sauran 'ya'yanta, yaro ne mai natsuwa da sanin ya kamata, karatun islama kam sai sai a ce Alhamdulillah, ina zaka makaranta ina ka dawo makaranta, ko a gidanma yana fin karatun Al-Qur'ani fiye da zaman banza, don Malaminsu ya kan fada masu Al-Qur'ani dadinsa ya wuce misali, wani gurin ya saka kuka, wani gurin ka ji dadi, haskensa ya wuce tunanin mai tunani, Al-Qur'ani waraka ne, duk wanda ya barsa tabbas rayuwarsa ba zata yi dadi ba, karanta shi na yaye dukkan bakin ciki da damuwa, yayi ta fada masu falalar karantashi, don haka ko kadan Nasiru baya wasa da karanta shi.
Ga tsafta, ta fannin kayanshi harma dakinshi dake zaure koyaushe tsaf-tsaf, kwata-kwata baya son kazanta.Mal. ne ya yunkura ya tashi tsaye, ya ce da Nasiru dake sharar tsakar gida, yana sharewa ganin ga Innarsu ga Fadima babu wanda yayi tunanin daukar tsintsiya ya share gidan gashi yayi kaca-kaca, shine shi ya dauka yana sharewa.
"Jeka ka ce ma A'i ta kai man ruwa baye zan yi wanka, ina so in fita shago tunda yaron nan(Basiru) baya nan. Ke kuma Fadima dama man furan nan dake cikin leda, indan ta gama Nasiru a samu kofi mai murfi a zuba a kai ma Gadanga, yana gidansu".
Ya ce da shi toh ya nufi dakin A'i, sai gata ta fito da bombami, dama ta ji me Mal. ya ce
"Daga dawowa ta ko hutawa ban yi ma ka fara sani yan aikace-aikacenka, gaskiya Mal. kana da damuwa wallahi".
Tana zuba ruwa tana mita har takai baye, ya shigewarsa ba tareda ya ce uffan ba.Fadima ta dauki furar ta shiga damawa tana gunguni
"Ni kullum-kullum ni ce yi kaza yi kaza, ni wallahi na fara gajiya".
"Aikin Baba ne kika fara gajiya? Indai baa yi ma kurum ba ayi ma zugum, a je can ai ma wani katon banza".
"Eh din, eh din".
Tana mugun hararanshi
"Ni kike harara? Zan mare ki Allah kuwa".
Sai ga A'i ta fito da gudu tana fadin
"Don Allah ka zo ka mareta, shege dan shishshigi, ba dole ta gaji ba, Mal. da kura mai rai yake".
Nasiru ya cigaba da abunda yake ba tareda ya kara cewa komai ba.Mal. ya shirya tsaf cikin shaddarsa fara mai babbar riga, ya ciro dari biyar na cefane ya mika ma A'i tareda fadin
"Zan fita, wannan kuma ayi cefane da su"
"Toh"
Kawai ta ce ta amshe kudin.Ta shiga sanwar abinci gadan-gadan sai ga 'yarta Larai tareda danta Usy ta zo ganin Mal, suka dunguma zuwa daki.
Bayan sun gaisa ne Larai ke ce mata
"Tare fa muka tsara zamu zo ganin Baba ni da Zali, na biya mata shine Mahe ya hanata zuwa, ina jin shi yana cewa ba zata ba kuma shi ma ba zai je ba, wai shi ko ubansa bai je gani ba bare ya je ganin nata, sai gata ta dawo sum sum jiki ba kwari, na ciji yatsana zalla takaici da batai mashi tas ba, ni in Baban Usy ne ya ce man haka ba sai na mai wankin babban bargo dan uban da ya haife sa".
"Mtsww ni na rasa ya akai Zali tayi sanyi har katon banza na juya ta yadda ya ga dama, sai ka ce ba jinina ba".
"Shine ai, mu da muka fito tsotstsonki har ana nuna mana bala'i da masifa, muda muka yi gadonsa".
Tana rufe baki sai ga Fadima ta shigo a firgice, hankali tashe, duk suka rude suna tambayar lafiya.
"Ina fa lafiya Innanmu, Baba ne na ji yana maganar Umman Meramu shi da Mal. Mamman".
Maganar da ta zo ma A'i a bazace, ta mike tsaye sai da tiren da take tsintar shinkafa ya fadi, bata ce komai ba zira mayafi sai gidan Ladiyo. Hankalinta in yayi dubu ya tashi. Tafiya take sai sambatu take
"Yau sunan Sahiya a bakin Mal. ina na ga zama".Sallama ma bata samu yi ba haka ta fada gidan, hajaran majaran.
"Lafiya A'i? Ko jikin Mal. ne yayi tsanani?".
"Ina fa lafiya?".
Kafafunta sai rawa suke ko tsayi dai-dai ta kasa, sai da Ladiyo ta zaunar da ita kasa.
"Wai Mal. din ne ya mutu? Ko ya ya abun yake?".
"Ai in shine ya mutu da da sauki da wagga annobar dake shirin dawowa".
"Wa kenan? Sahiya?".
"Ita fa, Mal. ya fara maganarta kinga kuwa gaba sai cewa zai je bikonta ya maida aurensa, ina cikin tashin hankali Ladiyo, na shiga uku".
Ladiyo ta yi jimm sannan ta ce
"Innalillahi..... Amma na yi mamakin yadda asirin nan yayi saurin sakin Mal. ko dai kin fara karya dokokin boka Ilu ne?".
"Yo ni yaushe rabo na da alwala in zan sallan asuba, ai tunda Boka ya ce in nayi magani zai kare ban sake ba, hakan nake sallata".
"Toh kuwa ana yawan karantun Al-Qur'ani?".
"Eh toh Nasiru na yi koyaushe".
"Haba! Shiyasa, dole magani ya walwale da wuri, ni dai nayi mamaki don aikin Boka Ilu nayi sosai".
"Innalillahi.... Ni dai Nasiru zai zameme bala'i a rayuwa, wai shi Ustaz, dan Ustaz din da Mal. ya hana ni fadi, duk cikin 'ya'yana shi ya fita zakka, shegen yaro."
Ta kara gyara zama tareda dafa Ladiyo ta ce
"Ni yanzu ya zaa yi Ladiyo?, in ta dawo ai sai sharan gidan Mal. tafi ni martaba a gun Mal, Zali itama na can sai fama take da tsinannen mijin nan nata".
"Ki bari wani sati sai mu sake komawa wurin Boka Ilu, amma fa ki tanadi kudi da yawa don yai muna babban aiki".
"Zan tanade su kuwa".
"Ba tun Zali kuwa duk laifinki ne, kayan matanga na mallaka baki sai mata ita kuma bata dabarar saye, yau mazan nan sai da haka, Larai ta fita wayo, don ita tana aiko kudi ana sawo mata, shiyasa kika ga sai abunda ta ce a gidanta, Fadima ma yanzu ya kamata ki fara tsumata"
"Ita da ko lokacin auren baa saka ba".
"Ehen! Ba tana da mashinshini(saurayi) ba?".
"Eh. Don kwanakin baya ma ya so a bashi dama ya turo Mal. ya ce sai yayi bincike kan shi".
"Kai! Baccin Mal. yanzu har wani binciki ake tsayawa yi mazan da suka yi karanci a wannan zamani. Uhumm! Toh ko ba dai yanzu ba, ki fara tsumata, ko da zaa kai lokacin ai ta tsuma, miji ya ji zam-zam, shi kuwa ya dinga dunkula abun duniya yana bata, ke kuma da ta samu wurinki ta yo".
A'i ta ji mugun dadi harda shewa, tabi shawaran da Ladiyo ta bata, nan ta saye gumbuna da garirrukka harda tsimi don fara tsima Fadima, tayi da ita bayan kwana biyu zata kawo mata kudinta don dari biyu ne hannunta.Tun kan hanyarta ta komawa gida ta saye madara ta gari ta dari, kafin ta ida gida kuma ta ga mai nono ta saye na dari.
Ko da ta koma Larai ta wuce gida, Fadima ta jawo daki, ledojin ta bude na magunan mata ta ce
"Kin ga na an so maki wurin Ladiyo ta ce a dinga baki tun yanzu kafin zuwan aurenki".
Nan ta shiga yi mata hudubar shedan, Fadima ta ji dadi dama in ta je gidan kawayenta tana ganin suna sha, amma kuma wasu na cewa da dadi wasu na fadin zafi, ita dai koma mene ne tana so itama taji.Ai kuwa kwana biyun nan ta maida abu damrin azimun, don kuwa gumba dame ta tayi cikin kwanon sha, ajima-ajima tana daukowa tana sha, tsimi kuwa tamkar ruwan sha ta maida sa.
Fadima ce kwance tana waya da saurayinta Buhari, wayarta kirar itel karama wacce Bahuri ya bata. Waya suke sai faman matse kafafunta take saboda tsananin feelings din da take ji, kalaman soyayya ne game da na batsa suke yi, sai fata take ina ma a ce yana kusa da ita.Vote and comments👌
YOU ARE READING
KUSKUREN IYAYEN MU
Mystery / ThrillerKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...