KUSKUREN IYAYENMU.
Na
U_F & Ashnur❤®
NWAGareku feenahmanzo,samiraAminu,user143...and gausiya47
12.
Ta biya mai mashin kenan sai ta ji ana fadin
"Malama Salamu Alaikum".
Ta amsa da
"Amin wa'alakumus salam".
Kamal ya ce
"Mu na tambaye ne".
"Allah Yasa na sani".
"Amin. Don Allah gidan Malam Hambali mu ke nema".
Ta jinjina kai
"Tab wallahi ban sani ba. Yana da wani inkiya?".
"Uhumm toh yana dai bada maganin iska ko sammu ko ciwon kan da ya tsananta".
"Wallahi ban sani ba".
Kamal ya ce
"Eyya. Toh ba komai, mungode".
Har zasu wucewa ta ce
"In har baku gane ba, idan kun je gida a sami ruwa a ka karanta masa, Fatiha ×1, Ayatul kursiyyu ×3, suratul Daha, aya ta 56-74 ×, suratul Yunus aya ta 117-122, FuruQan aya ta 23, suratul Zilzilat ×2, suratul Iklas × 3, suratul Qalam ×3.
Sai kuma a karanta masa wannan addu'ar.
A'UZU BIWAJHILLAHIL KAREEM WABIKALIMATULLATULLAHILLATI LA YUZAWIJIHINNA BIRRUN WALA FAJIRUN MIN SHARRI MA KALAQA WAZARA'A WABARA'A WAMIN SHARRI MA YANZILU MINASSAMA'I WAMIN SHARRI MA YA'ARUJU MINHA WAMIN SHARRI FITINATILLAILI WANNAHARI WAMIN SHARRI KULLI DARIQIN ILLA DARAQA YADRUKU BI KHAIRIN YA RAHMAN ×3.
Insha Allahu zai warware daga matsanancin ciwon kan, ko da shafar aljannu ne ko sihiri, kowanne iri ne.
Allah shine masani".
Godiya sosai Kamal ya yi tareda yi mata addu'ar miji nagari.
Kamal ya dan tsakuri Ali da shima ya dan ce wani abu. Ali kuwa mugun burgesa tayi, yarinya da ita sai tarin ilimi. Karaf suka hada ido da shi, tayi saurin kai nata kasa, saboda mugun kwarjini da yayi mata, kamar ba zai yi magana ba ya ce
"Ali na bada tasa godiya, Allahu shi biya".
"Meramu ma ta gode".
Kallonta ya dinga yi har ta bacce ma ganinsa. Cikin mota Kamal kuwa ya dinga zolayansa yana shammatarsa.Ko da ya koma gida ya tarar da Babansa na fizge-fizge sai sunan Sahiya dake fitowa bakinsa, Basiru ne kansa yana iya kokarinsa don A'i kwananta biyu kenan bata gidan. Ruwa yasa Fadima ta kawo mashi tareda Al-kurni, gefe ya samu guri ya zauna ya shiga karanta duk yadda ta fada masu.
Bayan ya kammala ya ba Babansa ga baki ya sha saura ya shafe jikinshi da shi.Karfe dayan dare bacci ya gagara daukansa sai filon dake manne a kirjinshi, idonshi ita yake gani, kunnuwansa muryarta ke yawo, juye-juye yake yana tunani birjik. Haka a bangaren Meramu da tunani Ali ta kwana.(Love one tin tin)
****Happy Island.
Bisa jan carpet ne Jidda da abokanta suke zaune, wanda jan carpet din ke shinfide kan grass carpet din dake malale a wurin. Dangin kayan fruit, snacks, drinks ne gabansu. Kowace ta dau ado tamkar zasu je gasar kyau, dama kuma gasar masoya suka zo don kuwa ya gayyaci nasa saurayi, sai dai Jidda wanda ta so ya zo(Sajid) ba zai samu damar zuwa ba.
Meramu na daga gefen zaune a kasa, yau ta samu nasaran an fita da ita sakamakon itama yau ado tayi da tsarabar Haj. duk da ba wata kwalliyace dauke da fuskarta ba amma tayi matukar kyau, rigar tamkar donta aka yi ta. Daga cikin kawayen Jidda wata ta kira ta, aladabce ta je, 1k ta mika mata ta ce
"Ungo ki je wurin can ki sawo man popcorn, a baki leda guda ukku".
Cikin rashin fahimtar me zata siyo ta ce
"Me zan siyo?".
"Gugguru zaki sawo, yeye girl".
Jidda ta ce tana zabga mata harara. Tashi ta yi tabi inda aka yi mata nuni.
Bayan tafiyarta wacce ta aike ta ta ce da Jidda
"Masha Allah yarinyar akwai kyau Jidda Tahir".
Dayar ta karba da cewa
"Ji yadda take tafiya don Allah daya bayan daya".
Tsaki Jidda ta ja ta ce
"Wallahi na tsani yarinyar nan don't why. Mtsw dalla ku tashi mu je daga can bangaren can da suke(samarinsu) mu dau selfie".
Dukkansu suka tashi suka bi bayanta(yan a bi yarima a sha kida)Ko da Meramu ta dawo ta tarar basu nan ta aje masu popcorn din su da canji, wuri ta samu ta zauna daga gefe, ko da wasa bata zauna kan shinfidarsu ba dukda basa kusa.
Ali.....................
Shigar black suit yayi rigar ciki ja, fuskarsa dauke da tabarau mai shegen kyau, agogon Rolex ne a tsintsiyar hannunshi, rufaffen takalma, designer turare ya shafa, adonsa tun daga samansa har kasansa a tsadance. Wayarsa tayi ring ya dauka
"Oga shegiyar yarinyar nan tana gurin ta gayyato dan SSG, labari mai dadi kuwa tare a ka zo yarinyar, yarinyar na zaune daga bangaren farko-farkon shigowa. And akwai wata gasar masoya da zaa yi gurin wacce ake gudanarwa bayan shekara-shekara".
"That's good. Ka cigaba da sa ido akan komai".
"Ok sir".
Ya katse wayar. Yana fitowa mota ya shigo cikin happy island cikin kasaita. Direct ya shiga don already yaronsa ya gama clearing komai. Tun daga nesa yake kallonta har ya karaso inda take zaune.
"Assalamu Alaikum".
Sallamar da ta ji a bazace hakan yasa tayi saurin dagowa. Amsa sallamar tayi kanta a kasa, ta rasa dalilin da yasa take jin nauyi a duk sa'an da suka hada ido. Zaunawa yayi kan carpet din, ta zaro ido cikin fargaba, labbanta har rawa suke wurin fadin
"Meramu na rokon a rufa mata asiri a zauna inda ba carpet ba".
"Ai kuwa Ali ba zai tashi ba sai yasan dalilin haka".
"Ashe kuwa zai sa Meramu cikin tashin hankali".
"Ali zai tashi amma sai yasan wurin na waye da baa so ya zauna".
"Na uwar dakin Meramu ne. Jidda Tahir".
"Waye kuma haka?".
"Laaa baka san ta ba, 'yar Alh. Tahir Gwadabawa, wata fara sol, kyakkyawa haka, tsayinta dai-dai misali".
Bai san sadda ya murmusa ba saboda yadda ta zuzutata.
Tashi yayi ya wucewarsa, sai taji duk ba dadi.Duk inda ya gifta kallonsa ake, Jidda harda sakin waya wurin kallonsa, a ranta masha Allah kawai ke fita.
Can yaji an fara gasar, launching cake zaa yi, akan duk wanda yafi sayansa da tsada zaa bashi damar yanka shi ya ciyar da masoyiyyarshi, sannan zaa ba masoyan damar cinkar rigar polo mai tambarin sunan masoya, sannan zasu hada sunayen masoyan.
Tun daga 10k wani ya fara har aka zo kan 100k wanda dan SSG ya aza su, nan Mc ya fara kirge ya kai lamba tara sai Ali ya ce ya aza 200k, Mc ya kuma sabon kirga har ya kai goma shiru ba wanda ya aza fiye da nashi. Tabi aka shigayi tareda saka kida. Mc ya umurce Ali da shiga fili, bayan ya shiga fili, aka basa wuka ya yanka. Nan yan mata suka shiga raba idanuwa don ganin wace ce mai sa'ar kyakkyawan masoyi haka.
Cikin kasaita (dama shi yana da surkin jinin sarauta) yake tafiya har ya isa inda Meramu ke tsaye, caa idanuwan kowa yayo kansu ciki harda na Jidda. Gaban Meramu ya dinga dukkan uku-uku.
Yadda ya kashe ta da ido yasa ta bude baki a hankali ya saka mata, gaba dai wurin ya kaure da tabi, Mc ya umurci da Ali ya zabi riga daya da aka yi wrapping daga gefen damanshi. Bayan ya dauka, Mc ya umurci da Meramu ta dau daya daga hugunsa, ta dauka.
Sai wani daga cikin yaran Dj ya fito ya karbi rigar dake hannun Ali ya cireta daga wrapping sheet din, ya duba wane suna Ali ya cinka. "My Lady" haka tambarin rigar yake, yaron ya anshi ta hannu Meramu ya walwale, ta ta koma "My Angel" aka dau tabi kowa, Mc ya hada sunansu ALMA. A zuciya ce Jidda ta bar gurin, tana ma Meramu mugun kallo.

VOUS LISEZ
KUSKUREN IYAYEN MU
Mystère / ThrillerKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...