KUSKUREN IYAYENMU
Na
U_F & Ashnur pyar❤NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
5.
Inna ta ce
"Toh..toh...toh.. toh lallai kuwa, lallai d'an nan kudin naku ma wato har a wannan zancen auren zaka gwada kenan? To ku ji ku kuma sani".
sai ta tsaya ta k'ara gyara daurin zaninta sannan ta cigaba
"Gabad'ayan ku nan babu wanda ya isa ya raba auren nan na Jidda da Gadanga akan kowane irin dalili ne, kar mutum ya yarda in masa baki ehe".
Abba ya san me Inna take nufi yasan dashi take yi, kuma ya riga ya san Inna da daukan zafi inta kafe akan abu to tsiyafa bata maganinta sai lallami, saboda haka sai ya kwantar da murya k'asa-k'asa ya fara tausanta
"Inna abinda nake so ki duba rayuwar Jidda zaki kalla, yarinyar nan ta taso cikin daula tun tana yar karamarta bata san wahala ba, bata ga wahala ba wahala bata ganta ba, komai kankanatar abu nafi son ayi mata, toh yanzu in muka amince da auren wannan yaron wani irin rayuwa kike tunanin zata shiga?".
"Yo ai koyo zata yi, ai ita rayuwa ai duk inda kasami kanka koyan zama zaka yi".
"Inna ba nan kadai fa abin ya tsaya ba ki duba ki gani ko wani matakin karatun kirki baya da, amma yake fad'in yana sonta, Inna ki daure ki duba wannan abun ita kanta ta fishi karatu, toh wace sana'a ke gareshi? dame zai rike'ta?".
Shiru Inna tayi na dan wani lokaci kamar ta amince can kuma kawai sai suka ji ta fara sheshshekan kuka
"Mai kuma ya faru Inna?".
"Mene ne ma bai faru ba..inyin...yanzu d'an nan abin naka har ya kai haka in ce kayi amma ka ce ban isa ba..inyin..inyin..lallai abin naka ya kai d'an nan, ni dai banji dadin huldarka da masu jajayen kunnuwan nan ba(Turawa) dan tunda ka fara mu'amala dasu ka dauki tsare-tsaren da al'ada irin tasu, ka soma fandaremin..."
'Inna fa ba zata taba amincewa ba Ina ganin dabara kawai zan mata na nuna na amince inya so shi yaron nan na san yadda zanyi na tilasta masa yaba Jidda takardan saki, shine kadai abinda Inna zata gani ta hakura da wannan Auren'.
Abba ne ke wannan tunanin cikin zuciyarshi.Hajiya Rahama ko na gefe sai cika take tana batsewa ita auren jari take so tayi ma Jidda ba auren da 'ya zata dawo tana ci a gidansu ba, Sam! Bata san abinda Inna ta gani agun wannan yaron ba, bata taba ganin wanda arziki ke binsa yana guje mai ba kaman Inna,
'Amma koda arziki koda tsiya bazan bari 'yata ta zauna da gaja ba, sai dai in Malaman tsubbu sun kare a duniyannan dole ne in shiga in fita'.
Cikin zuciyarta take wannan sak'e-sak'en.
Falon yayi tsit kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa.
B'angaren Gadanga ko yana gefe guda ya rasa abin fad'i a zuciyarsa yana godewa Allah daya hada auren shi da Jidda wacce ya dade yana mafarkin mallaka a bisa wannan kaddarar data fado musu lallai shi ya isa a kira shi da mai cikakken sa'a. Gefe guda kuma yana tunanin yanda rigimarsa zata kaya da mahaifan Jidda, shin zasu yarda su bashi matarsa? ko ko suna nan akan bakarsu ba zasu canza ba, dukda yakan dan ji kwarin gwiwa na goyon bayan da Inna ke bashi, amma abinda yayi imani ne agunsa shine ba zai taba bada takardan saki wa matarsa ba komai wuya komi tsanani. A d'ayan b'angaren na zuciyarsa kuma tunanin matarshi Meramu yake yi, ya zata fuskanci wannan lamarin idan har ta ji ya kara aure a Irin yana yin halin rayuwar da suke ciki, me zata ce dashi yayo mata kishiya, zata ga don bata taba haihuwa bane shiyasa nayi mata kishiya, kuma kishiyar ma ta 'yar masu kud'i anya nayi mata adalci kuwa?'."Inna na amince yanzu me kike so ayi?"
Dam! Gaban Hajiya Rahama ya fad'i jin cewa mijinta ya amince wa mahaifiyarsa akan auren yarta
"Yawwa ko kai fa d'an nan, yanzu kayi magana, ai ina ganin yanzu ba abinda ya wuce a gayyato jama'a domin yin walima kowa ya shaida mu tattarata mu kaita gidan mijinta, kuma ban yarda kace zaka bashi wani gida ba, taje can ta zauna da abinda Allah ya horewa mijinta... ehen.. meyuyuwa hakan yasa ta koyi darasi a rayuwarta ta duniya, wulakancin da take yiwa mutane zata daina shi".
Jidda na jin mahaifinta ya ce da Inna ya amince ta mike tayi saman stairs tana razgan kuka Hajiya Rahama tabi bayanta tana rarrashi. Mamakin mijinta cike cikin zuciyarta bata san me ya hau kan mijinta ba da har yake ikirarin ya amince da auren Jidda a haka Ina sam! Ba zata sabuba
"Sai dai ki mutu munahinhin kawai, ai wulakan tasa kika soyi ance miki ana yima Allah wasa ne?"...
"Inna kibarta ta ji da d'aya, yarinya ce fa".
"Kai tafi can ka bani wuri ku kuka sani da wannan zancen naku ni dai aje asiyo goro dan zuwa rabawa mutane, kai Kuma Gadanga ka tashi ka je gida ka sanarwa da manyanka dan su shiryo su zo daukar amarya Allah ya riga ya kashe ya baka. Kai kuma taho nan mu je Hameedu"
Hameed ya ce
"Toh".
Wanda tun da aka fara diramar yana gefe guda bai tofa ko uffan ba. Bayan Inna yabi suka bar falon.
Shima Gadanga fita yayi bayan Abba ya anshi cikakken adireshin gidansu da kuma kauyen da yake.
****Gadanga kwance a bisa tabarmar dake shinfide a tsakar gida, yayi matashi da pillow. Lumshe idonsa yayi yana tunani birgetai, akwai fargabar faruwar abubuwa da dama.
'Ta ya zan tunkari Meramu yanzu?'
Wata zuciyar ta tambaya.
Ji yayi an dafa pillown da yake kwance akai, hakan yasa ya tashi zaune. Matarsa Meramu ce dauke da fura cikin kwanon sha.
"Kayi shiru me kake tunani? Ka san yadda nake shiga damuwa a duk lokacin da na ganka cikin damuwa kuwa? Nasan duk dan Adam zai so a ce yau ya ga jininsa. Mu kuwa shiru har yanzu. Don Allah kada ka juya min baya, kuma kamin alkawari ba zaka min kishiya ba duk runtsi, ina sonka mijina, kuma zan iya komai don soyayyarka. Sonka da nake yasa ina tsananin kishinka. Ina ga duk randa ka kawo man wata a matsayin kishiyata toh tabbas adadin rayuwata ne ya zo karshe, saboda na dauki adadin soyayyarka da kishinka ne kamar yadda na dauki adadin tsawon rayuwata. Idan ka juya man baya kuma lallai zan lalace. Don Allah kada ka barni na fada cikin girgizan kasa irin ta masoya".
Magana take hawaye ne ke kuranya. Tausayinta ya kama Gadanga, janyo ta yayi a jiki ya rungumeta.
Hannayensa yasa ya goge mata hawaye. Sai da ta dau mintuna kan kirjinsa, sannan ya tado ta daga jikinshi, kwanon sha dake gabansa ya bude ya fara bata ga baki.
"Na san zuciyarki zata tsinci kanta cikin yanayi na damuwa sakamakon ganin tawa zuciyar cikin damuwa, nasan zaki ji haka amma duk da haka kada ki bawa hakan damar yin tasiri acikin zuciyarki, ina sonki matata, u r za fish in my whole stomach".
Murmushin jin dadi tayi lokacin da ya kare maganarsa a cikin yaren nasara, duk da bata fahimci maganarsa ta karshe ba amma hakan yasa ta ji mugun dadi, ko ba komai tana kyautata zaton kalaman soyayya ne. Gadanga ya cigaba da magana
"Ko da gangar jiki tayi nisa ina so ki san cewa zuciyoyinmu sun fi komai kusanci, ki inganta yardar ki gare ni ni kuma zan adana amanar soyayyarki ta zamo mafi kololuwar sirri. Haihuwa kuma lokaci ne da ita, Allah ya bamu 'ya'ya masu albarka".
Ta amsa da
"Amin".
Cikin shagwaba. Zai sake bata furar ta jaye bakinta alamum ta koshi da fura. Ta sake narkewa tayi kan jikinshi.Cikin azam ya tashi tsaye jin kwankwasar kofar waje da ake.
Talkamansa ya saka sannan ya tunkari zaure, a hankali ya zare kubar dake jikin kofa. Cikin girmamawa ya gaida mafaihinsa Mal. Iro.
"Ungo Gadanga yi min magana da inyamurin nan mai talkama cewa zan zo jibi na karbi takalman amma ya rage man kudin sun yi yawa".
Gadanga ya karbi wayar kirar techno karama. Lambar inyamurin ya shiga kira, can sai ya dauka. Gadanga ya fara waya
"Kuda aftanen".
Inyamuri ya ce
"Afternoon Mal."
"No issa no him, isa me Gadanga".
"Oh! How are you?".
"Fine thank you sir.
My faza sed he will going to com tomorrow tomorrow to collect za shoes but u hav to sizors d money bcos d money of shoes is to higher cos".
Inyamurin ya gane mai Gadanga ke nufi don yau da gobe bata bar komai ba, sun dau shekaru da dama suna sarin takalma wurinsa, da baya gane wani turancin amma saboda yau da gobe ya kan gane.
"Ok no problem till he come".
"Thanks"
"Thanks too. Bye"
"Bye".
Gadanga ya katse wayar. Mika ma mahaifinsa wayar yayi ya ce
"Baba ya ce ba damuwa sai ka zo kuma ya gode"
"Yauwa Gadanga. Allah shi yi albarka".
Ya karbi wayar ya wuce. Tafe yake yana kara yi ma Allah godiya da ya fitar mashi da mai ilimin boko da na muhammadiya cikin gidansa. A da anyi cutarsa saboda rashin karatun zamani da baya da kuma cikin 'ya'yansa ma babu, sai daga baya yasa duka yayansa makarantar boko, wasu suka ki wasu suka sa wasa, sai Gadanga kawai yasa mu yayi tundaga firamari har izuwa sakandari.
U_F aur Ashnur pyar✍🏻✍🏻Dan Allah wai meyasa dayawa sai su karanta amma ba vote bare comments, ghost reader ku daina mana ba girmanku bane pls vote comments and share
VOCÊ ESTÁ LENDO
KUSKUREN IYAYEN MU
Mistério / SuspenseKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...