tsautsayi..

1K 94 11
                                    

KUSKUREN IYAYENMU

Na
U_F & Ashnur❤

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

Okwonko👌👌

13.
Kuka take cike da dana sani, wai ita wani irin tsautsayi ne ya fada mata, zuciyarta sai halbawa take da sauri-sauri ga fargabar haduwarta da mai dakinta.
Mika mata hanky yayi don share hawayenta ba tareda ya ce da ita komai ba, kasa cigaba da sauraren kukanta yayi ya kira Bello ya kaita gida.
Mc dauke da cake din da hawansa ya kai biyar, sai yaransa biyu kowane na dauke da wata jaka, suka karasa gaban motar Ali, a kujerun baya Mc ya saka cake din tareda jukunkunan biyu. Godiya sosai suka yi ma Ali suka wuce.
Cikin wasu yan mintuna kalilan sai ga Bello, Ali ya umurci da ya kai Meramu gida a motarsa, Bello ya ce
"Oga kai fa?".
   "Kada ka damu Kamal zai zo ya dauke ni. Abi a hankali wurin tuki don kayan Ali zaka dauka".
"Insha Allah Oga".

Baya Ali ya bude ta zauna bayan Bello ya kwashe kayan dake gurin ya maida gaba. Shiga tayi ta zauna don bata da zabin da ya wuce haka don babu wani abun hawa a wurin. Murfin motar ya rufe yana kallonta, ita kuwa kanta a kasa don wani haushinshi take ji da ya hadaddasa mata bala'i ga mai dakinta.

A hankali Bello ya tada mota ya fara tafiya.
Bayan wucewarsu da minti ashirin sai ga Kamal.
A hanya suna tafiya Kamal ya ce
"Sorry kayi ta jirana, wallahi wani tsaiko na samu".
    "Ah! Bakomai".
"Ina Meramun?".
    "Meramu? See you, Maryam take ko ka kira ta Alma, zaka shiga cikin jerin masu bata mata daddaden sunanta".
Dariya Kamal ya yi ya ce
"Oh Allah! Yau zan ga wannan rana, Uhmmm soyayya. Toh ina Alma?".
  "Bello ya je ya kaita gida, abun ciwo sai zubar hawaye take saboda fargabar haduwarta da tsinanniyar yarinyar nan, na tsani yarinyar nan to the extent, da na ganta dazu tamkar na shaketa, i can't bear in dinga ganin Alma a karkashinta".
"Yarinyar ce bata da tarbiya komai tsufanka zata iya zazzaga maka rashin kunya ko da kuwa gemenka a kasa yake ja.
    "Don Allah mu bar magananta raina baci yake".
Kamal bai koma cewa komai ba.

Lafiyar lau suka isa, har kofar gida ya taka mata sannan ya dawo mota, yaro ya samu ya daukar masa jaka daya, shi kuma ya dau cake.
Yaron ya fara kai jakar cikin gidan sannan Bello ya bashi cake din ya shiga da shi ya fito, naira hamsin ya ba yaron ya wucewarsa, yaron godiya ya yi shima ya wuce yana tsallan dadi.

Komai bata rufe ma su Umma Ladidi ba da Ummanta, tun daga farkon ganinta da shi har zuwa yau. Fada sosai Ummanta ta shiga yi Ladidi na bata hakuri, Umma ta ce
"Haba! Inda zamu rufa asirin kanmu shine kika bata?"
    "Ki yi hakuri mana Sahiya. Mu dai Allah Yasa haka shi yafi alkhairi. Mu kam Allah ya kashe ya bamu".
"Ya hakuri Umma ba zan sake ba".
Cewar Meramu tana kuka.
   "Bari mu ji shi wannan abu mai matattakala yadda yake".
Ta gustsira cake din, Umma tashi ta yi ta koma daga cikin daki cike da haushi.

******
Saboda tsananin haushi da bakin ciki Jidda kawai ta kamo hanya ta dawo gida, ba don ta damu gayen ba ne, babban bakin cikinta ace wai kamar Meramu matsiyaciya, yar talakawa kuma yar aikinta, ita za a kalla har asawa cake a baki, shima guy din bata san wani irin dakiki ba ne, duk sauran matan da ke wurin masu aji yan wane da wane bai lura dasu ba ne? sai wannan 'yar aikin?
Cizon lebenta tayi cike da takaici.
"Ni na je da ita wurin nan ne don na wulakanta ta na kaskanta ta gaban kwayena, saboda na lura yau da ta zo aiki sai wani rawan kai take yi don tasa doguwar riga, shine yanzu harta sami wani gara yana tayata, ita a dole ta yi kasuwa ko?! Zata zo ta same ni, don sai ta fada min uban da ya sata bude ma guy din nan baki har yana sa mata cake ana musu tabi".
Ita kadai take ta surutunta, tana cika tana batsewa, can sai ta mike tayi sashen Inna.

Habiba na zaune suna hira da Inna kasancewar ta kawo mata kumbarta ta kunu, sai ga Jidda ta shigo ko gaida Inna bata yi ba, ta kalli Habiba a wulakance harda zungurin kanta ta ce
"Ke! Ina wannan wawiyar yarinyar take?" (Meramu take nufi).
Saboda zungurin da tayiwa Habiba sai ta ji haushi madadin ta bata amsa sai ta shareta.
"Kam bala'i! Lallai yaran gidan nan kun fara fetsarewa ni zan miki magana ki share ni?".
Nan take tasa hannunta ta rankwashi kan Habiba.
Har Inna ta bude baki zata yi magana kawai sai suka ga Habiba ta tura kanta tsakankanin cinyoyinta, shiru, can suka ji wani irin kuka da ka ji kasan ba muryanta ba ne, ashe Habiba Aljannu gareta, ba abinda Habiba ta tsana irin a bugar mata kai.
Da sauri Inna ta fito kiran Izzatu, Jidda ma da gudunta ta fito dakin cike da tsoro, harda su tuntube, don a duniya ba abinda take tsoro irin me jinn, bata taba sanin Habiba na dasu ba da baa abunda zai sa tai mata magana bare har ta tabe ta.
Kiran da Inna ta rinka yi ne yasa su Izzatu da Mani tahowa da gudu. Da kyar Mani ya banbare kan Habiba cikin ciyoyinta, Izzatu ce ta rik'e Habiba nan suka shiga yi mata addua ita da Mani har Allah yasa ta dawo cikin hayacinta. Har gida Izzatu ta kaita sannan ta dawo.

Tunda abin nan ya faru Jidda da ta shige dakinta ta kudundune kanta cikin bargo, tsoro da firgici duk ya kamata, abinci ma kasa ci tayi. Haj. Rahma ta shiga matsifa an firgita mata yarinya, fadin take
"Aikin banza aikin wofi, aljanun karya, in ma ajanun ne su zo ni ban tsoronsu".
Haka ta dinga masifa.
*DA DADDARE..............*

 KUSKUREN IYAYEN MUTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang