BAN KWANA....

1.9K 147 91
                                    

KUSKUREN IYAYENMU

Na
U_F & Ashnur❤

®
NWA

16.
Ali ya gama shirinsa kenan, cikin kanan kaya, kayan sun karbe sa tamkar don shi aka yi su, kiran wayarsa ne ya shigo, dauka ya yi a can bangaren Bello ne ke ce masa
"Oga labarin marar dadi, an kwantar da Alma asibiti".
"What? Yaushe? Kuma a ina?".
"Jiya, a Uduth".
"Ok".
Ya katse wayar.

Tsayawarsa kenan a ma'adanar motoci dake cikin asibiti ya hango Umman Meramu, fitowa ya yi ya karasa wurinta. Hankalinta sam ya tafi da tunanin da take barkatai.
"Anty".
Sunan da yake kiranta kenan tun lokacin da aka kawo ta gidan Babansa. Juyowa ta yi saboda sananniyar muryar da taji, hannu tasa ta rike gemen bakinta alamun mamaki
"Gadanga? Kai ne?".
Murmushi ya yi ya ce
"Ni ne Anty. Na tsaya ne na hango ki na ce bari na karaso in gaishe ki".
"Allah Sarki! Ya Yaya Amadu da matar Yaya? Da su Sageer duk lafiya?".
"Lafiya lau Alhamdulillah. Waye ba lafiya Anty?".
"Yarinyar nan ce wallahi tun jiya ba lafiya, zazzabin ciwon sauro, ganin galabaitar da ta yi shine na muka kawo ta asibiti, yau kwananmu daya, yanzu ma na bar an kara mata ruwa ta samu bacci, magani ne Likita ya ce a sawo, shine na karbo".
"Mu je na ganta, ni ma na zo ganin......"
Bai ida ba sai kawai ya yi murmushi, ita ma Umma murmushi ta yi don ta dago shi, ta ce
"Ai da mun tafi nima na gaishe da 'yar tawa sannan sai mu je ka ga kanwarka".
"Aa Anty mu tafi in ga kanwata tukunna, hasalima ai na dade bangan ta ba, tun tana 'yar kankannuwarta".
"Gaskiya ne".
Ta yi yar dariya.

Mamaki sosai ya bayyana a fuskarsa lokacin da ya ga ta tsaya gadon da Meramu take.
"Ka ga har yanzu bacci take".
Mamaki yasa ya kasa furta ko kalma daya. Alhakimu Allah, ashe alma jininsa ce, haba gaske yake jin soyayyarta ta zarce ta ko ina. Ji ya yi Umma ta ce
"Zauna mana Aliyu, ko sauri ka ke?".
"Aa".
Tareda yin murmushi, farar robar kujera dake gefen gadon ya ja ya zauna. Kallonta yake ta yi, ta yi haske sai dai ta yi rama ta yi kyau abunta. Waya ya ciro ya kira Kamal cewa gashi cikin asibiti a female ward ya zo ganin Alma, Kamal ya ce da shi gashi zuwa.
A hankali ta bude idonta suka yi ido hudu da Ali, mamaki ya bayyana a fuskarta, ganin yaki jaye idonsa gareta ya sa ta kauda nata. Wayarsa ta yi ruri alamun kira ne ya sake shigowa.
Iya burgewa ya burgeta yadda yake gwamatsa hausa da yaren nasara, kallonsa ta yi ta yi har ya kare, dubanta da zai yi suka sake hada ido, ta yi saurin kauda na ta.
"Anty ina zuwa".
Ya mike ya fita. Nan Umma ke ce mata
"Ai shine Yayanki Gadanga dan Yaya Amadu, don nasan ba zaki shaidasa ba, yaron kirki".
"Allah Sarki".
Ta ce tana lumshe idonta, ashe shi din jininta ne
'Allah Sarki'
Ta koma nanatawa a ranta.
Umma fita tayi suka hado a waje. A gefe suka tsaya ya ce
"Su Daddy na gaishe ki da mai jiki".
"Muna amsawa"
Ya gyara tsayuwarsa ya ce
"Amma Anty Baba bai san Maryam bata da lafiya ba ko?".
"Ta ya zai sani kuwa bayan ya yafe mani ita".
Nan ta fayyace masa komai, ya jinjina abun, lallai akwai makarkashiyar Innar Fadima a cikin lamarin. Maganar Umma ce ta dawo da shi daga tunanin da ya shiga
"Na san kulbajima watarana sai Mal. ya anshi 'yarsa ko kuma ita ta bukaci komawa wurin Babanta watarana, shiyasa nake addu'a ta samu miji nagari ta aura don ko kadan bana son ta zauna da A'i don rayuwarta zata kuntata, zata shiga garari da wahalhalu na rayuwa, Aliyu na yaba da halayenka, shiyasa nake sha'awar ina ma a ce Yarinyar nan ta same ka a matsayin miji, da ta more har abada, Aliyu na baka Meramu har abada, amana ce na baka ko bayan bani a duniya, ka kula min da ita ko da abunda nake mafarki bai tabbata ba, ina so ka daukar man alkawari rike man ita don Allah".
Ta ida maganarta cikin muryar kuka, don ita kadai tasan yadda take ji a ranta, cikin tausayawa ya ce
"Anty ki yi hakuri ki koma gidan Baba"
"Me kuwa zan yi bayan aure ya kare, zan koma gidan ne bayan bai maida aurensa ba? Ko dai-dai da rana daya bai waiywaye mu ba, ai ko bakomai akwai jininsa a hannuna, sai dai a wani bangaren bana ganin laifinsa don bayinsa ba ne, ni dai ka yi min alkawari Aliyu".
Cikin sanyin murya ya ce
"Na yi Anty".
Godiya ta yi masa tareda sa masa albarka ta wuce tana share kwalla.

 KUSKUREN IYAYEN MUWhere stories live. Discover now