KUSKUREN IYAYENMU
NA
U_F & Ashnur❤®
NWA6.
TUSHEN LABARI (Waiwaye)
Waye Jidda? Waye Meramu? Matar Gadanga. Waye shi kanshi Gadangan?Meramu....... A kauyen Fanfo.
Mal. Iro nada mata ukku. Uwargida itace A'i sai amaryarsa Sahiya. A'i ke da ya'ya biyar Basiru shine babba ga Mal. Iro sai Zali, sai Larai, Nasiru sai yar autarta Fadima. Sahiya ke da kwaya daya tak Meramu.
Mal. Iro baya da wani kwakkwaran aiki sai noma, daga bisa ni ya fara sanar saida takalma, gidansa gidan kasa ne a da amma yanzu ya zama na bulo kasancewar dan uwan haihuwarsa dake birni mai wadata ne. Shi kam baya da hali sai karfin hali amma hakan ya iya aje mata biyu, duk da yana da dan uwa mai kudin gaske kuma yana taimaka masa sosai, amma zuciyarsa ba ci ma kwance ba ce, ya kan neme na shi na kanshi, irin mutanen nan ne masu dogaro da kansu. A da yaransa basa boko sai islamiyya, ganin cutarsa da ake saboda rashin karatun zamani da baya da kuma cikin 'ya'yansa ba maida, hakan yasa ya saka su, dama dan uwansa ya saka dansa da Basiru makaranta. Amma basu tsaya suka yi ba suka wofintar, sai dai yana alfahari da dan-dan dan uwansa da ya tsaya yayi karatu.
Mal. Iro bai kuma samun sassauci a wurin A'i ba tun randa ya kawo Sahiya a matsayin kishiyarta ba, don haka duk ranar da ya ce babu toh ranar cikin tashin hankali zai kasance, in ka ga ya samu sassauci toh wurin Sahiya ne.
****Tunda Meramu ta girma ta kai shekara goma cikin ta goma sha yanzu, kai tun tasowarta take shan ukuba, matsi, tsangwaba da bugu wurin yan uwanta don ko kadan basa raga mata saboda suna tama uwarsu kishi ga Sahiya.
Shi kuwa Mal. Iro tsaye yake baya barin su cuceta indai yana gida, kuma yana kyauta ta masu, shiyasa mutane suyi ta tsegumin baya da adalci tsakanin iyalansa, yana nuna bambanci tsakaninsu, Sahiya da yarta su yafi so a gidan, har watarana abokinsa ya taresa da wannan magana, ya bashi amsa da
"Wallahi ba haka bane ita fa rayuwa tana son mai kyautata mata, hakan kuma tana kin mai munana mata, ko kadan bana jin sassauci ko kadan daga A'i, fitinar yau daban ta gobe daban, duk ranar da na wayi gari bani da toh ranar bala'i sai wanda ta manta, ta koyama yaranta mugun hali irin nata, ita kuwa Sahiya hakuri gareta, ga sanin ya kamata, duk fa ta saida wasu kayan dakinta don tayi sanaa mu samu abunda mu rufawa juna asiri, ga natsuwa duk abunda suke mata bata tanka masu, ka ga kuwa dole in so ta".
A'i kam kullum cikin sintirin hanya take, ita dai burinta bai wuce ta mallaki Mal. ta kori Sahiya daga gidan ba. Yau tana wurin wannan boka gobe tana wurin wancen, tareda taimakon babbar kawarta Ladiyo.
Tun baa nasara har aka dace, domin tun ranar da Mal. Ya shiga dakin Sahiya ya ji warin mushe, cikin lokaci guda cikinshi ya lallace bai sake shiga dakin Sahiya ba, saboda wani warin mushe da yake ji duk lokacin da ya kusantota.
Washegarin ranar a gaban A'i yake cewa ba zai sake shiga dakinta ba har sai ta daina warin da take, kuma ba sai ta zo koda gaisheshi ba ya gode, ai kuwa murna a wurin A'i baa magana, harda su rawa da shewa, 'ya'yanta kuwa kida suka dinga yi suna rawa, Meramu kuwa sai kuka take ita da Innarta.
A haka dai rayuwa ta dinga yi masu kunci, barinma Sahiya da Mal. Ya bar zuwa dakinta, ita ma tabar zuwa dakinshi don ko ta je korota yake, abinci ma ba koyaushe suke bata ba sai in Meramu ta samo makota. Ranar girkinta kuwa ya maidasa duka ga A'i a cewarsa baya iya cin abincinta ko kwana dakinta da wannan warin da zai iya hallakashi.Watarana tana zaune a tsakar gida tayi ta gumi abun duniya ya isheta, ta rasa ina zata sa kanta, sai ga Mal. Ya shigo ta fara'arsa yana ganinta ya turmuke fuska, nesa da ita ya tsaya ya ya mutsa fuska ya ce yana rufe hancinsa
"Gaskiya na gaji, iya hakuri na yi hankuri, a ce ni da gidana cikina baya da sukuni, wannan wari da me yayi kama? Gaskiya na gaji, don haka na sauwake maki, na sake ki, idan kin samu miji ki yi aure, kuma 'ya ki tafi da ita na yafe maki ita, kuma kada ki sake in ji ki gidan Dan uwana. Fakat".
Ya juya ya fita. Sahiya ta rushe da kukan bakin ciki.
Ta koma daka tayi ta kuka ita da 'yarta, yayinda A'i ta zo kofar tana mata shewa a dole ta bar mata gida, don yanzu ita ce da gida ita ce da maigida. Sai da A'i ta sulala mata maganganu masu zafi sannan ta wuce.
Ganin kukan ba shi ne mafita ba yasa ta tattare inata-inata dana yarta suka bar gidan, dama ba wasu kaya masu yawa bane.
Allah yasa akwai dubu biyu hannunta, suka yi kudin mota suka shigo cikin birni wato birnin Shehu(Sokoto).
A tasha dake gefen fulai oba aka sauke su daga nan suka hau napep zuwa Tudun wada.
Baa wani dau lokaci sosai ba suka isa, ta biya mai napep sannan suka gangara kasa zuwa gidan 'yar uwarta Ladidi.Bayan sun ci abinci sun sha ruwa sun yi sallah sannan Sahiya ta zayyana ma Ladidi yadda aka yi. Budewar bakin Ladidi ta ce
"Allah Ya saka maku, karshensu ba zai yi kyau ba. Amma nayi mamakin Iro".
A haka dai suka cigaba da rayuwa a gidan, daga bisani Sahiya ta bukaci neman aiki ko da kuwa aikatau ne, shine ta ce zata kai ta gidan wata Haj. Da take ma kitso ko zaa da ce.
*****JIDDA....... A Sokoto
Jidda kyakkyawa son kuwa kin wanda ya rasa. Yarinya ce fara mai yalwantaccen gashi, jikinta matsa kaici, yarinya mai ji da kanta.
Jidda ta zama abun so ga kowa barin ma iyayenta.
Mahaifinta Alh. Tahir(Abba) dan asalin jahar Sokoto ne a karkashin karamar hukumar Gwadabawa.
Malami ne da yake koyarwa a makarantar dake gaba da furamari dake cikin garin Gwadabawa, a makarantar ne ya hadu da Haj. Rahma matsayin daliba, suka kulla soyayya daga bisani ta amince ya aure ta saboda kudi da kwalame-kwalamen da yake bata, haka Haj. Rahma take da son abun duniya, tun tana karama haka take, idan gidanku ba masu arziki ba ne bata kawance da kai.
Suke zaune da Mahaifiyarsa Abu(Inna) kasancewar shi kadai ne danta, kakansa kuma ya rasu wato Mijinta.
Yana karantarwa kuma yana taba kasuwanci, ya kan dauko atanhinne daga Kano ya kawo garinsu yana saidawa. Kadan-kadan Allah yasa ma kasuwancinsa albarka, a lokacin ne aka haifi Jidda.
Tun yana zuwa Kano kadai har ya soma zuwa Lagos, nan ne Allah ya hadasa da ubangida wanda baya da keta a rayuwarsa. Ya cigaba da kasuwanci karkashinsa. Tun yana kasuwancinsa a iyakar kasa Nigeria har ya fara fita kasashen ketari.
Jidda na da shekara biyu da watanni aka haifi Hameed.
Abba ya samu kudi sosai hakan yasa ya a jiye aikin gwamnati.
Ya dawo cikin garin Sokoto ya gina gida na alfarma. Ya tare da iyalansa da 'ya'yansa biyu wato Jidda da Hameed da Innarsa. Ya cigaba da kasuwancinsa.
Ganin dubin arzikin da ya tara yasa ya canza halayarsa.
****"Haj. Wannan baiwar Allahr tana neman aiki ne dafatar zaki taimaka mata don Allah".
"Zata iya kuwa?".
"Eh zan iya, ai mai nema baya jin gajiya".
Cewar Sahiya aladabbce.
"Gaskiya yanzu babu wani aiki da yawa, don ina da mai aiki Izzatu, sai dai mai rage mata wasu ayukkan kamar shara da wanke-wanke, sai kuma yi ma 'ya'yana abunda suke so ai masu, ina ga 'yarta ma ta isa".
Ta so a ce ita ta samu amma ya ta iya, dawainiyarsu tayi ma Ladidi yawa. Ta ce
"Bakomai Haj. Allah Ya saka da alkhairi Ya yi mana jagora".
Suka amsa da Ameen.
Ladidi tayi ma Haj. Rahma godiya sannan suka bar cewa Meramu zata fara zuwa aiki daga gobe.
Vote and comments hiliis
KAMU SEDANG MEMBACA
KUSKUREN IYAYEN MU
Misteri / ThrillerKyakkyawa ce ita ajin farko, gani take talaka ba abakin komai yake ba, abin ataka ne a murkushe domin baida wani 'yanci, ta tsani talakan mutum bata kaunar ganin talaka ko kadan...........sai gashi daga wasan April full Aure ya hadata da dan talak...