Tafada cikin matsanacin kuka tare da kwantawa kasa tana rolling kaman wacce akayi wa albishir da mutuwa, babu Wanda ya tanka mata su binto tsayawa sukayi kanta suna kallon yanda take birgima kasa, ko kallon ta ammi batayi ba har tagama zuba wa su binto miya kan tuwon dake cikin kwano Sannan ta shiga ciki, har lokacin dija NA kwance kasa yaran neighbors sai lekota suke don ba karamin ihu take ba tana cewa
"Ban kara zuwa talla...ban kara zuwa talla...saidai yunwa ta kashe mu gidan nan...." Ta fada cikin kuka, ammi na shiga cikin dakin ta nufi inda take ajiyan bulala ta yo waje, dija dake kwance na ganin ammi da bulala ta tashi tayi waje da gudu tana kuka,
"Shegiya da kin tsaya yar banza...." Ammi ta fada tana maida bulalan. Har bayan sallan magrib dija Bata dawo gida ba tana nan labe gefe daya tana kuka gashi har lokacin Bata bar fargaban abinda ammi zatayi mata ba.Ammi na ganin Bata dawo ba tasa binto ta nemota, sanin inda take zama in tana kuka yasa binto bata sha wahalan gano ta ba,
"Kizo inji ammi..." Ta fada mata, hararanta dija tayi da red eyes dinta tana cewa
"Ki wuce ki bani wuri..."
"Ammi tace kizo ..." Binto.ta sake fada mata, aikam sai ta rarumi takalminta binto NA ganin hakan ta bar wajen da gudu taje ta fadawa ammi yanda sukayi daita,
"Ta shigo Dan kanta..." Ammi ta fada tana shiga cikin daki, har bayan sallan ishai dija da zaune inda take tana kukan bakin ciki, gani take gwara Kawai ta amince tana son dan Musa suyi aure kamar yanda yake yawan fada mata dukda batasan burouban da akeyi cikin aure ba amma ko kadan batason ta kara talla, tana nan zaune Bata ankaraba taji an damketa da Sauri ta daga kai taga ammi, baki ta bude zatayi kuka ammi ta dora yatsanta daya kan bakinta tana cewa
"Wallahi kika sake naji bakinki sai NA lahira ya fiki jin dadi...maza tashi ki shige min gaba..." Amma ta fada tana rike daita don tasan dija da kafan gudu kaman taci kare, da Sauri dija ta mike ra shiga gaban ammi suka taho gida sai shessheka Kawai take saboda yanda tayi kuka, daki ra shiga ta rabe jikin bango tana sauraron abinda ammi zatayi mata, ammi ce ta shigo rike da kwanon tuwo ta ajiye gaban dija
"Maza ki zauna ki cinye kafin ki ci ubanki...." Ammi ta umarceta, babu musu ra zauna ko hannu Bata wanke ba ta fara cin tuwon, ko kai Bata dagaba har saida ra cinye tas saboda sanin halin ammi, tana kamawa ta daga kai ta kalli ammi dake kallon ta, ahankali ammi ta fara cewa
"Yanzu dija kin fi son gidan wasu kan gidan mu?... Kinfi son zama da wasu kan zama damu?..." Ta tambayeta cikin natsuwa, dija shuru tayi batace kala ba, ammi ta cigaba dacewa
"Yanzu kinfison inda zakije a maidaki kaman baiwa?...baki da gatan komai sai yanda akayi dake?... Dija njasan bani da ko sisi amma ban barin wani ko wata ta wulankanta Mani Ku....yanzu tambaya daya nakeson yi maki...kin fison zama dxa wasu kanmu?...." Da Sauri dija ta girgiza mata kai,
"To wane dalili ne yasa kike kuka don NA hanaki zuwa aikatau?..." Ammi ta sake tambayan ta, tana shessheka ta fara cewa
"Ammi....Kawai inason mu dinga samu kaman yanda su hase ke samu..."
"Kinsan halin da take ciki?..." Bata idaba dija ta katseta dacewa
"Ammi babu halin da take ciki..kalli yanda ta koma ranar da ta dawo...Kuma tace min har boko take zuwa...nidai ammi ki bari in je...in babu dadi zan dawo..." Tafada da gaske, ammi.zama tayi tana kallon ta cike da mamakin yanda take magana babu alaman tsoro, kara fashewa tayi da kuka tana cewa
"Dan Allah ammi ki bari inje...in da akwai matsala zan dawo...Kuma ni wallahi inason boko..." Ta fada cikin kuka,
Ammi tsaya kallon ta kawai tayi saida tayi kukan mai isanta Sannan ammi tace
"Amma kinsan cewa ba ni kadai ke da iko da Ku ba ko?.... Dukda yan uwan ubanku basu damu da Ku ba nasan da zaran wani abu ya faru zasu samu bakin magana..." Da Sauri dija tace
"Ai duk suna birni...kawu nanu Kawai ne nan...ammi muje mu fada mashi...." Ta fada har jikinta NA rawa,
"Badai yanzu kike nufi bako?..." Ammi ta tambayeta, sadda kanta kasa tayi Sannan tace
"yanzu.." Tafada tana murmushi,
"Jaira... Babu inda zamu yanzu ..saidai gobe..in bai yarda ba sai ki hakura..." Inji ammi,
"Nasan zai yarda...ai ba damuwa yayi da rayuwata ba...." Tafada cikin jindadi, hararanta ammi tayi Sannan tace
"Je kiyi salla...nasan rabonki da salla tun NA zuhr..." Bata idaba dija tace
"Ai har yanzu ban gama ba..."
"Amma kaman kinyi salla da zuhr
" aa NA duba naga har lokacin bai tsaya ba balle inyi wanka..."$ ta amsa mata kaman ba ita bace ke kwance kasa tana kuka kaman wata yar karama yarinya.
"Je ki kara dubawa..." ammi ta fada mata, da Sauri ta mike ta fita.