na cuceta 35

8.3K 490 46
                                    

🧡💜💙💚💛❤
NA CUCE TA
💜💙💚💛❤🧡


®Zuwairat (ummumpls am)


3⃣5⃣



_Follow me on:_

*Wattpad @ummumaryam29*

*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*

*IG: zuwairatummumaryam*

*Website:Www.ummumaryam.com*

*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*

*Snapchat: ummumaryan29*








Bayan an gama aka saka mata shoes da suka hau da sky blue Arabian gown dake jikinta. Perfumes matar ta fesa mata sannan ta tattara kayanta cikin bag tace
"Amarya kinyi kyau...." Tafada tana fiddo waya daga cikin pause dinta, pics tayi mata sannan ta fita daga dakin, ita ai dija sai feeling so weird don gani take kaman an damkar mata buhun cement a face dinta don nauyi taji fuskanta yayi mata.
"To ki tashi mu tafi...." Wata yar uwan ammi ta fada mata, jiki ba kwari ta mike idanuwanta cike da kwalla amma basu zubo ba, wurin grandparent dinta aka  kaita suka karayi mata adua sai wajen amminta nan dija ta dinga kuka kaman ranta zai fita, tana kuka tana dafa maranta. Saida ammi ta daka mata tsawa sannan tayi shuru
"Kuma wallahi kar ki bari inji ance kiyiwa mijinki laifi...duk abinda yace kiyi kiyi kina jina?"..." Da Sauri ta daga mata kai
"Allah ya kaddara saduwanmu...tashi ki tafi Allah ya yi maki albarka ya yafe maki kurakurenki...." Jiki na rawa dija ta mike mata na biye daita, suna fita waje mata na tsaye cike da waje wasu sunyi ready zasu bi ta don kashe qarkwatan idanuwansu. Bayan an nunawa dija motan Salem ta shiga baya sai kuka take, sai yau Salem yaga dija, duk da kanta na kasa jikinta ya nuna karamar yarinya ce, murmushi yayi ya kauda kanshi gefe cikin ranshi yana cewa
"Shege yazid...." Salem lekawa yayi a mirror yaga yanda mata ke rige2 shiga mota
"Allah yasa kar su lalata masu mota. Bai Ankara ba wasu mata kusan su uku suna kikarin shiga gidan gaban motanshi, sai ture juna suke kaman wasu awakai, kaman yayi magana sai kuma yayi shuru
"Ki bari ni na kamata in bita ba ke ba..." Inji daya daga cikin su,
"Lallai ma..." Daya ta fada, matar datayiwa dija makeup dake zaune baya kusa da dija ta tabe baki sannan tace
"Haba kubi ahankali mana...ko so kuke Ku lalata masu mota..." Tafada cikin tsiwa da Sauri suka ja baya daya ta shiga. Salem ya fixgi motan suka bar wajen, duk sauran cars na dauke a mutane 8 biyar baya sai biyu gaba da driver. Salem kam yayi deciding bai maidosu saidai ya samo bus da zai maidosu, babu abind ke tashi cikin motan sai sheshekan dija.

Bayan sun gama sukayi wanka tare mufida ta zauna gaban mirror yazid ya goge mata gashi da karami towel sannan ya shafa mai hair cream tare da combing kan, kawai yanayi yana kallon ta tacikin mirror yana aduan Allah yasa this is not a trap don ko kadan babu wata damuwa tattare daita hes wondering how comes don lokacin daya shaidawa mufida halinda ake ciki tamkar zaa kwantar daita hospital, hannunta data dora kan hannunshi ya maidoshi hayyacinshi, murmushi ya sakar mata yana cewa
"Baby I love you... Kinsan wannan shine abinda kikayimin daya fi komai burgeni...thank you.. " murmushi tayi dukda maganar shi ta bata mata rai wato duk kokarin da take wajen biya Mashi bukatan shi bata burgeshi kaman wannan ba, amma ko kadan bata nuna Mashi hakan ba saboda advice da mom dinta ta bata.
"Baby na zauna nayi tunanin babu komai duniya...sannan banason rabonda ke tsakaninka daita ya aikadani lahira...so kawai Allah ya bamu zaman lafiya...kuma pls promise me you will love and cherished me all the days of my life...." Tafada Mashi cikin natsuwa, hannuwanshi yayi rounding waist dinta daga inda take zaune yayi hugging bayanta,
"Baby I will love you for ever...I wish dukkan mata zasuyi yadda kikayi...su San cewa what will be will always be nor matter what...." Yafada yana kissing bayan wuyanta
"Baby I love you too..." Tafada tana shafa face dinshi dake bayanta.
"Yanzu baby tell me abinda kikeso inyi maki...." Shuru tayi kaman tana tunani for a while sannan tace
"Why not mu bari muje umrah tare...." Dadi yazid ya karaji ya kara rungume yana jin wani irin sonta da kaunarta har cikin system dinshi.
"That sounds perfect my Queen... Yanzu yaushe su Aisha zasuzo?..."
"Zuwa later..."
"OK muyi sallah...kafin ki shirya kafin su zo...and pls my Queen kar ki biyewa duk abinda zasuce....I know them too well...."  Murmushi mufida tayi tace
"Baby don't worry... I won't let anyone lead me astray..." Tayi assuring dinshi
Murmushin jin dadi yayi bude closet ya saka jallabiya  ya fita sallan asr.  Itama doguwar riga tasa tayi sallah.

NA CUCE TAWhere stories live. Discover now