💛💚💜🖤💙❤
NA CUCE TA
💛💚❤🖤💜💙®zuwairat(ummu Maryam)
1⃣8⃣
Bayan Hajiya babba ta koma falo zama tayi tare da rafka uban tagumi tana tunanin abinda ke faruwa, confirm Tasan something is wrong amma ba ta hanyan yazid ba kilan wasu yaran gidan
"Wai menene anty?..." Hajiya karama ta tambayeta tana kallon how lost in thought she is, ajiyan zuciya Hajiya babba ta saki
"Kawai ina tunani ne...ni ina ganin yaranj gidan nan are involved..." Bata idaba Hajiya karama ta katse ta dacewa
"Haba anty... Why will you think such...yanzu kina ganin yazid will do such thing?..." Itama Hajiya babba girgiza kai tayi
"No...amma what about your naughty children... Kinsan sarai suna iya aikata..." Baki Hajiya karama ta turo kaman wata karamar yarinya Sannan tace
"Gaskiya anty yarana ba zasu yi hakan ba...gasu asabe basuyi masu komai ba Sai ita da ko wata batayi a gidan nan ba?...Gaskiya anty ki bar irin wannan maganar kar suyi succeeding...." Tafada tana cika tana batsewa daman tafi Hajiya babba zafi da fada.
"Ni abinda nake tunawa shine yanda Yarinyan ta bar gidan nan...in baki mantaba har kuka kika cemin tanayi don ta koma gidansu...kilan.at that time da akwai abinda sukayi mata that made her change her mind at once..." Hajiya babba ta fada cikin sanyin murya, itama Hajiya karama shuru tayi tana tunanin maganan Hajiya babba don itama Sai lokacin ta tuna yanda dija ta koma kafin a kaita gida, she remember ko abincin kirki bataci, itama ajiyan zuciya ta saki
"It can't be...." Tafada cikin ranta tare da kallon hajiya babba da ta Dora kafa daya kan daya tana girgiza su ahankali, Sai kuma Salem ya fada mata a rai,
"Maybe Salem ne..." Hajiya karama tafada da Sauri tana kallon Hajiya babba, Hajiya babba daga kai tayi ta kalleta,
"Yes it may be him...kinsan NA fada maki ya tambayeni address dinta...kilan shine sanadiyan cikin...." Hajiya karama ta fada da Sauri, ahankali Hajiya babba ta gyara zamanta
"To in shine Sai ta kira sunan yazid?... Ai Sai tace Salem..." Da Sauri Hajiya karama ta kara katseta dacewa
"Ai kinsan Yarinyan bata da wayau...Sannan bata gane yan gidan ba sosai...kuma kinsan Salem da yazid suna yanayi..." Ta fada mata, Hajiya babba dai baki ta saki tana kallon ta, itama tayi tunanin hakan,
"Kina gani Salem zai iya aikata hakan?..." Hajiya babba ta tambayeta, da Sauri Hajiya karama tace
"Ai mutum bai gane halin yaran zamani ba..." Dariya Hajiya babba tayi
"Ashe kin San baa rantsewa yaran zamani amma kika rufe idanuwa kan yaran nan bazasu Iya aikata hakan ba..." Hajiya babba ta fada cikin dariya, iatam Hajiya karama dariya tayi
"Ai dole...wa zai yarda a goga ma nashi ...every mother will do all they can to protect their offspring..." Inji Hajiya karama
"Even if they are wrong?..." Hajiya babba ta tambayeta,
"Hmm am sure basu da laifi...yanzu meye abinyi?... Don duk fadan nan da kika ga inayi...deep down inajin tausayin wannan Yarinyan..." Hajiya karama ta fada,
"Ni ai duk jikina yayi sanyi..am just imagining how it will as a mother yar ka ta zo da cikin shege while the person responsible yana chan yana hutawa.." Hajiya babba ta fada kaman zatayi kuka,
"Allah dai ya kare mana zuria..." Hajiya karama tq fada Sannan tace
"Yanzu meye abinyi don we can't just fold our arms ...kuma Wallahi in nan gidan Salem yayi wani abu daita Sai naci ubanshi Wallahi..." Tafada sounding very serious,
"Ko dai mu kirashi nan mu tambayeshi?...." Hajiya karama ta tambayi Hajiya babba,
"Gaskiya I can't have such a shameful discussion da shi...Kawai ki kira yazid ki tambayeshi in ya San da akwai wani abu daya shiga tsakanin dija dashi don mostly basu boyewa junansu secret..." Inji Hajiya babba,
"To hakan zaayi...." Hajiya karama ta amsa mata
"In ya shaida maki da akwai Sai ki fada mashi Yarinyan tana da ciki....daga nan Sai mu San abinyi...." Inji Hajiya babba,
"To shikenan... Bari in kirashi...." Tafada tana da juyawa don daukan wayanta Sai tga bai nan wajen
"Ashe duk zaman da nayi a nan babu waya kusa dani..." Inji Hajiya karama
"Daman kin saba ...nasan yanzu miss calls na chan rututu..." Hajiya babba tq fada mata, dariya tayi Sannan ta mike, daman by then an farq kiran sallan zuhr.Tunda dija ta shiga mota take shessheka amma babu hawaye har wata mata dake zaune kusa daita ta tambayeta matsalan ta amsa mata da babu komai
"To ki bar damun mu da hayaniya...." Matar ta fadawa dija, dija hada kai da kujeran gabanta tayi tana tunanin sunan kauyen su ammi, tafi minti biyar tana tunani Sannan sunan wurin ya fado mata, Sai ta tuna tunda amminta da kanta ta gujeta Tasan koina ma gudunta zaa dingayi,
"Allah kasa in mutu..." Tafada cikin ranta wasu new tears suna fitowa daga tired eyes dinta,
"Allah kasa inyi hadari in mutu...banason duniya...." Ta sake fadawa kanta wannan Karin tana fashewa da kuka sosai,
"Wai ke lafiya kike mamu kuka cikin mota?..." Wanda ke zaune gabanta ya tambayeta, da Sauri dija ta share hawayen ta amma deep is side she's boiling,
"Allah yaisa....ban zan yafe ba...mugu....kasa ammi ta koreni..." Tafada cikin ranta wasu hawayen na zubowa, ita ba cikin jikinta ke concern dinta ba, koranta da ammi tayi, Tasan ana cikin haihuwa don tasha ganin Matan kauyen su da manya ciki daga baya ashe sun haihu, to anata tunanin ba irin wannan cikin gareta ba don ita cikinta bai da girma, batasan nan da four months da ko yarinya zata keto ta jikinta ba,
"Wallahi garzali bai da mutunci..." Taji daya daga cikin Matan dake zaune layin da take tana fadi,
"Inafa yaganshi...yarinya da ciki amma ya saketa... Ko tausayinta bai jiba... Yaran yanzsu sun maida aure tamkar wasa...." Wata ta saka baki, dija kasake tayi tana sauraron su, daman bata manta hiran da sukayi da kawarta ba inda take fada masu anasamun ciki in namiji ya sakawa mace abun fitsarinshi, tasan saki don tana jin ana cewa aure ya ruguje tsakanin wasu, shuru tayi tana tunanin abinda zata dinga fadawa mutane in an ganta, don gani take kowa na ganin tana da ciki kuma zaa dinga tambayan ta ,
"Nima sakina yayi...." Tafada thinking that cikin ranta ta fadi hakan, da Sauri Matan dake gefen ta suka kalleta,
"Inna lillahi... Kinga irin abun ko?... Yanzsu wannan yar Yarinyan har ta isa a aureta balle saki?... Gaskiya muna da matsala..." Matar ta fada kaman zatayi kuka tana kallon dija, Dan ajiyan zuciya dija tayi don gani take ana tausayin ta
Ta samu tudun dafawa kenan tunda ta samu an tausaya mata,
"Allah ya saka maki..." Daya daga cikin Matan ta fada,
"Ameen..." Tafada ahankali. Har suka isa jos dija bata bar hawaye ba, Kawai tunanin halin da zata fada in har mutuwa bai dauke ta bha Kawai take, bus stop dake cikin garin jos motan ya paka mutane suka fara fitowa, dija zaune tayi tana kallon mutane dake kai kawo Sannan tana tuna lokacin da suke zuwa da ammi, bata manta irin murnan da suke muddin akace zasu zo jos amma yau gata cikin jos tana jira mutuwan ta.
"Ki fito mana...." Taji wani yana cewa, Sai lokacin ta dawo hayyacinta, bag dinta dake kan cinyanta ta dauko ta fito daga cikin motan ta shiga cikin park dake dauke da mutane kala2 kowa ta kanshi Kawai yake, gefe daya ta samu ta zauna, duk Wanda yaga yar beautiful yarinya zaune dauke da bag kan kafanta Sai ya juyo ya kalleta Sannan su wuce. Irin tambayan da ake yi mata yasa ta mike ta dauki bag dinta tana zagaya park din rike da bag dinta, mutane Sai tambayan ta suke ko zata hau mota amma ki daga kai batayi balle ta amsa.