PART 4

5.7K 313 5
                                    

Three days later

Dija ce dauke da roban furan ta tana yawo tana shiga manyan gidaje don ita gani take yan kananan gidan basu da kudin siyan fura
"Duk daya muke daku..." Take fada duk sanda taga yar karamar gida. Tana cikin tafiya ta shiga cikin wani beautiful house, daga tsakar gidan ta hangi wata mata zaune kan carpet tana waya, daman ta taba shiga gidan Kuma an saye dukan furanta, hakan yasa ta tsaya Bata tafiba ta tsaya tana sauraron abinda matar ke cewa
"Eh wallahi Hajiya ce tace kanwata na son yar aiki Kuma duk Wanda NA samu sai suce Kano yayi masu nisa..." Ta fada ahankali tana sauraron abinda ake  fada mata, bayan few seconds ta kara da cewa
"Ni ma ko kadan banason ace wasu su kai mata yar aikin ba muba saboda cewa tayi yayarta matar isa bala ce..kinga da akwai samu...." Ta fada Sannan shuru ya kara biyo baya tana sauraron abinda ake fada mata,
"To shikenan.. Dan Allah ki bincika.. Nima zan cigaba da nema amma fa ance wacce zata Iya aikin komai..." Matar ta fada, dija kam duk tana jin abinda  matar ke cewa, shuru tayi tana tunanin inama a dauketa, bayan kaman minti biyu matar ta kashe wayan ta Sannan ta daga kanta ta kalli dija, da Sauri dija tace
"Kuna sayen fura?..." Ta fada ahankali, matar murmushi tayi Sannan tace
"Ki kawo in gani..." Ta fada mata fuskan Hajiyan dauke da murmushi da ganinta kasan irin yan duniyan nan ce don da gani tana shan taba, ahankali dija ta karasa ta sauke furan gaban Matan ta yaye ledan furan don matar ta samu daman ganin furan da kyau,
"Kece kika kawo min fura kwana kin baya?..." $ matar ta tambayeta, da Sauri dija ta gyada mata kai tare dacewa
"Eh nice..." Ta fada har lokacin Bata daina tunanin abinda taji matar NA cewa ba,
"To ki bani NA dari biyu in saka a fridge...don naji dadin furan kwanakin baya..." Da Sauri dija ta dauko Leda daga gefen roban ta ta fara zuba furan cikin natsuwa kaman ba ita ba, sai da ta gama ta ta dauko biyu ta kalli matar tana cewa.
"Ga gyara..." Ta fadawa matar, murmushi matar tayi Sannan tace
"Nagode..." Ta fada tana daukan purse dinta, budewa tayi ta dauko dariya biyu ta Bata, dija ta amsa tare dacewa
"Nagode..." Rufe furan tayi da ledan Sannan ta mike tana son yiwa matar magana amma ta kasa, daukan furan tayi har ta kai bakin gate ta juyo ta kalli Matan dake latse2 wayanta, tsayawa tayi bakin gate din Wanda yasa matar kallon ta,
"Lafiya dai ko?..." Matar ta tambayeta, da Sauri tace
"Eh...daman...." Sai tayi shuru, matar tsaya kallon ta tayi don sauraron abinda zatace, jin tayi shuru Kuma Bata tafi ba yasa ta cewa
"Daman me?..." Inji matar cikin natsuwa, dija kasa cewa komai tayi Kawai tayi tsaya kikam dauke da robanta akanta,
"Dawo inji..." Matar ta fada mata, ahankali dija ta dawo , gefen ta matar ta nuna mata
"Sit..." Matar ta fada mata, dukda dija batajin turanci ta gane abinda  matar ta fada mata, ahankali ta sauke roban kanta ta zauna gefen Matan.
"Ki fada min...me kike son fada min..." Matar ta tambayeta, dija dai shuru tayi tana wasa da yatsunta,
"Ke nake sauraro..." Matar ta sake fada mata, ahankali ta fara cewa
"Daman....naji...kina...cewa....kinason... Mai..aiki...shine..." Sai tayi shuru saboda yanda gabanta ke faduwa, Matar ta gane inda ta dosa dukda muryanta NA cracking
"Ina jinki..."  inji matar,
"Nace..in..babu...damuwa....zan....yi..."  ta kai.karshen maganar da kyar, murmushi matar tayi tana cewa
"Da kaman bazaki ida maganar ba...kina Iya aikin ne?..." Da Sauri dija ta gyada mata kai tana cewa
"Eh.." Yanda tayi maganan yasa matar dariya tana cewa
"In iyayenki basu yarda ba fa?..." Da Sauri tace
"Babanmu ya rasu..nasan ammi zata yarda...in kin je ..kin fada mata ..." Ta fada muryanta na cracking, matar kura mata ido tayi tana kallon beautiful and innocent face dinta Kuma tana tunanin wane irin dalili ne zaisa yarinya ta so zuwa gidan aiki Kuma da kanta ba wai forcing dinta akayi ba, amma tana kallon how faded her hijab and wear looks sai ta gane she will definitely needs some income Kuma Tasan ta cancanci irin gidan da ake magana.
"In Bata amince ba fa?.." ta sake tambayan ta, muryan NA rawa tace
"Nasan zata yarda..." Ta Bata assurance dukda tana ganin da kyar hakan zai yiwu don Tasan stand din ammi kan barin ta tafi wani wuri aiki amma gaskiya ta gaji da wannan wahalan tallan Kuma tayi deciding zatayi  anything necessary don ammi ta amince NA wannan zancen
"Wane wuri kike?..." Ta tambayeta, nan dija ta fada mata sunan kauyensu, baki matar ta bude
"Yanzu daga Chan kuke zuwa nan cikin garin?.." Kai dija ta gyada mata
"Lallai kam..amma ina ganin da nisa Kuma aikin ba a garin katsina zaayi ta..Kano ake bukatan mai aiki..."  Da Sauri dija ta katseta dacewa
"Ai ba komai... Tunda baa kasa zanje ba..." Dariya matar tayi
"To..yanzu tunda an fadamin ana bukatan mai aikin da wuri bari in kaiki garin naku sai muyi magana da amminki..." Wani irin dadi dija taji amma sai cewa tayi
"Ai ban gama saida furan ba..." Dariya matar tayi tana cewa
"Ki kirge min sauran..." da Sauri dija tayi counting sauran cikin Leda ta mika mata
"NA nawane?..." Matar ta tambayeta
" sauran na dari uku da sabain..." Dari biyar matar ta dauko ta Bata,
"Ki jirani nan..." Inji matar Sannan ta shiga cikin falonta, Bata yi wasting time ba ta fito da gyale tare da car keys dinta, sai adua take Allah yasa a amince don Tasan ba karamin samu bane in kayi hulda da family isa bala, dija sai mar mar da idanuwa Kawai take,  mota matar ta fidda daga parking lot dija ta shiga ciki duka kama hanyan garinsu.

NA CUCE TADonde viven las historias. Descúbrelo ahora