Daga kitchen dinning area asabe ta kai ta Sannan dakin daukan baki sai dakin su Ameera don dakinta Kawai take gyarawa sauran yaran suke gyara wurin su da Kansu,
"Ba wani aiki ke da akwai da yawa ba...Kawai dai baa sin gani kazanta ko kadan ..." Asabe ta fada mata suna komawa dakinsu, dija dai sauraron ta kawai take don gurin ta dare yayi ta kwanta,
"Kiyi wanka mana kafin lokacin sallan magrib.. Bamu da girki yau don haka babu aikin da zamuyi saidai in Hajiya ta bukaci muyi mata wani abu..." Inji asabe,
"Ina zanyi wankan?..." Dija ra tambayi asabe cikin sanyin murya. Mikewa asabe tayi ta bude kofan dake cikin dakin tace
"Taso ki shiga...." Ta fada mata, ahankali dija ta mike ta shiga bathroom din tana kallon ikon Allah don babu abinda ta Iya amfani dashi a wurin tsaya kallon bathroom din, asabe jawo kofan ta farayi dija tayi Sauri rikewa
"Ban...Iya...ba..." Tafada muryan ta na rawa. Dariya asabe tayi Sannan ta shiga cikin bathroom din ta fara nuna mata amfanin shower da heater tare da bathtub, dija kura mata ido tayi Bata ko kaftawa har asabe ta gama Sannan tace
"Yanzu ki nuna min abubuwa dana koya maki..." Fada mata, nan itama dija ta fada exactly abubuwan da ta fada mata, mamaki ne ya kama asabe cos she explained everything perfectly. Nan asabe ta fita ta barta tayi wankan sai lumshe idanuwa take saboda yanda take jin dadin kamshin sabulun wankan. Atakaice cikin kwana uku dija ta gane kan bangaren Hajiya karama, har da sunayen yan gidan gaba daya kaman yanda asabe ta fada mata Kuma ba karamin dadi take ji gidan ba don within that three days ta chanza cos ko fita batayi Kuma gashi da sun gama aiki kwanciya suke suyi bacci, yanzu kam dija ta bar tsayawa bathroom ta kalli kanta sai dai a gaban mirror dake dakin su amma sai in asabe Bata dakin sai ta tsaya ta kunshe towel dinta ta kalli jikinta da kanta tana kashewa kanta ido tana Dariya , yauma tana tsaye gaban katon mirror tana kallon kanta asabe ta shigo da plate din abinci, da Sauri dija ta gyara towel din tana kallon asabe, itama asabe kallon mamaki tayi mata,
"Me kikeyi haka?..." Asabe ta tambayeta cikin surprise, da Sauri dija tace
"Babu komai..."
"Kaman ya babu komai..."
"Aa... Kawai wanka NA fito....shine nake shafa mai...." Tafada ahankali, asabe dai Bata kara cewa komai ba ra ajiye abincin suka fara ci,.Yazed ne kwance yana bacci, alarm ne ya tadashi ya mike da Sauri tare da godiya ga Allah ya shiga bathroom yayi wanka Sannan ya fito daure da alwallah. Kaya ya saka yayi salla nan cikin dakin Sannan ya cire jallabiya dake jikinshi ya shirya cikin suit ya fashe kanshi da perfumes ya fito looking handsome than ever, kallon agogon hannun shi yayi yaga 6:15am
"I still have some time..." Yafadawa kanshi tare da fiddo wayanshi daga cikin aljihunshi, number Hajiya yayi dailing suka fara hira
"Son ka dawo haka nan mana...wai nan da abuja kake wannan abun kaman Wanda ke abroad?..." Dariya yayi
"Ai mom wahalan tuki nakeji...Kuma sauran sati daya hutuna..."
"To shikenan... An turo maka pic din gidan ?..."
"Yes mommy... It's beautiful... Amma nan abuja zaa kawota....".
Yafada yana naughty laugh
"Kaci gidanku...nan Kano zaa ajiyeta..." Turo baki yayi kaman yana gaban ta Sannan yace
"Mom NA....aikin fa?..."
"Ka dinga zuwa every weekend..." Idanuwa ya zaro, yayi shuru Kawai baice komai ba don kar Hajiya tace yana mata rashin kunya, haka suka gama hiran ya fita daga quarters din zuwa office.Yau Hajiya Aisha ta koma gidansu dija din kai mata kayan data sayo mata, da sallama ta shiga cikin gidan, da Sauri ammi dake zaune ta rafka ban tagumi ta mike
"Ah..ah..Sannu da zuwa..." Inji ammi Tafada cikin murmushin karfin hali,
"Yauwa..." Sannan suka fara gaisawa, ledan Hajiya ta mikawa ammi
"Gashi inji uwar dakinki dija...." Ahankali ammi ta bude ledan Bata wani yi murna kan kayan ba,
"Ya dija take... Ina Iya zuwa ganinta?.." Ammi ta fada har jikinta NA rawa, murmushi Hajiya Aisha tayi
"Ki kwantar da hankalin ki..diyarki tana gidan Hutu...Kuma albashinta dubu ashirin..." Da Sauri ammi ta kalleta,
"Wane irin aikine zatayi da zaa Bata dubu ashirin cikin kwana talatin?.." Ammi ta fada cike da mamaki.
"Ai NA fada maki yarki tana gidan manyan mutane... Yanzu karshen watan nan zan sayo maki waya sai ki dinga waya da yarki..." Inji Hajiya Aisha, dadi ammi taji har cikin ranta.