na cuce ta 29

6.2K 560 93
                                    

🧡💜💙💚💛❤
NA CUCE TA
💜💙💚💛❤🧡


®Zuwairat (ummumaryam)


2⃣9⃣



_Follow me on:_

*Wattpad @ummumaryam29*

*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*

*IG: zuwairatummumaryam*

*Website:Www.ummumaryam.com*

*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*

*Snapchat: ummumaryan29*













Ammin data dade batayi tafiyan kirkiba sai gata ta fito daga cikin mota da gudu, haka zalika su binto da driver dake cikin mota, yazid bai San sanda ya karasa inda dija ke wance ba, shima doc daya bugeta fitowa yayi  cikin tashin hankali,
"Khadija!!!....." Yazid ya dinga kiranta yana rike daita nan kasa, hannu ammi ta dora bisa kai tana kuka,
"Khadija dan...Allah... Wake up...." Yafada yana girgiza ta da karfi amma ko motsi batayi, mutane taruwa sukayi suna kallon su, doc daya bugeta ya rike yazid don ya samu daman duba dija amma wani naushi yazid ya kai Mashi Wanda ya tsorata shi yayi saurin ja da baya,
"Khadija... Pls....don't do this to me....I will be miserable for the rest of my life...." Yafada yana dorata kan kafanshi at the same time yana kuka kaman ranshi zai fita, duk mutanen dake tsaye babu Wanda yayi kokarin taimakawa, doc daya bugeta nason taimakawa amma yana tsoro kar yazid ya kara naushinshi, yazid tsaya kallon yanda cikinta ke motsi yayi ya daga kai yana kallon faces din mutane yana cewa
"Dan Allah Ku taimaka min....pls help....." Da sauri doc din nan ya zo ya rike wrist dinta for a while sannan yace
"Ka dauketa muje...." Inji doc cikin sauri, da sauri yazid ya mike ya dauketa, ammi da dasu binto babu abinda suke    sai kuka, bin bayan yazid sukayi shi kuma yazid na biye da  doc, sai sauri yake amma ko gabanshi bai kallo sai dija, yana tunanin yanda ta koma kaman baitaba
"Me zanyi maki in biyaki for all this pain...." Yafada yan kuka, kallon yanda cikinta ke ta motsi kawai yake, bai ankaraba yaji zaa amsheta daga hannunshi, sai lokacin yaga nurses da gadon da ake tura mutum, baisan ya akayi sukazo ba, babu musu ya dorata kan gadon aka fara turata amma yana rike da hannunta, goshinta daya kumbura ya kalla.
Motsin dan cikinta looks so visible da ko daga nesa kana Iya hangen yanda cikin ke motsi kaman zai fito

Doc kallon ta yayi for ya moment sannan yace
"Take her to the labour room..." Hankalin yazid ne ka Kara tashi, baisan lokacin dayace
"Its just seven months....", doc dai baice komai ba amma deep down yana tunanin wanne relationship ke tsakaninshi da ita don they look so different, babu alaman dangantaka tsakaninsu don duk Wanda yagansu yasan they are from two different part of class and level amma yanda yake nuna damuwanshi is questionable to him
Inda dija ta  kwana for some days aka shiga daita only she was unconscious, tsaye yazid yayi aka shiga ciki daita, ammi dai kuka yaki tsayawa, yazid goge face dinshi yayi ya fiddo wayanshi dake cikin aljihunshi Wanda ya kashe tun 12am na jiya kuma bai kara kunnawa ba saboda kar mufida ta tisashi gaba. Kunnata yayi sannan yayi dailing number Salem, after like ringing biyu zuwa uku yayi picking yana cewa
"Wai me yayi zafi da zaayi bikin lil brothers dinka amma baka zo ba?.... Gaskiya baka kyauta ba... Dazun saida dad dinku yayi min magana bayan daurin auren... Karya nayi Mashi nace kuna port...." Duk maganar da yake yana fada cikin annoyance ne amma gurin yazid shine ya kai aya sannan ya fada Mashi abinda yake son cewa, yana jin shuru  yafara cewa
"Na ganta!..." Ya fada in one word,
"Wa?..."
"Khadija..." Ya amsa Mashi cikin sanyin murya , dasauri Salem ya saki ajiyan zuciya tare dacewa
"Ina?..."
"A jos...."
"Da akwai cikin?..." Ya tambayeshi full of excitement,
"Yes....amma she have an accident while running away from me...." Yazid ya fada muryanshi na rawa,
"Subhanallah!!....how is she?..."
"Yanzu anshiga daita ciki....salem... Na cuceta....you need to see her....ta koma kaman baitaba....I don't know what made me do it...." Yafada yana kokarin sake kuka saboda yanda heart dinshi keyi Mashi zafi,
"Rabo...kaddara...destiny...." Salem ya amsa Mashi in a calmly manner
"Yanzu me doc yace?... Hope it's not serious?..."
"Bata motsi....amma naga cikin na motsi...ka tayani adua...I don't want to loose anyone of them.... Inason in biya Khadija for the pain and agony I caused her....kuma inason abinda zata Haifa....nasan ana iya stigmatizing dan ko yan...amma ba laifin shi ko ita bane....it's all my fault... The child deserve to live...." Yafada in a regretting manner at the same time hawaye na gagarowa daga idonshi,
"Insha Allah the child will live...babu abinda zai samu both of them.... Ka kusa zama dad ko..." Salem ya karasa maganar da zolaya, yazid zai bude baki yayi magana yaji call ya shiga, dubawa yyi yaga small mom,
"Bari zan sake kira...mom is calling..."
"OK..pls give me updates about her..." Inji Salem
"OK..." Kawai ya fada yayi picking call dinta, itama balbaleshi ta farayi kan meyasa baizo daurin auren su Sharif ba, saida ta kai aya sannan ya fada mata ya gan dija
"Kai alhamdulillah...." Ta fada with excitement kaman baita ke fada few seconds ago ba,   dan murmushi yayi sannan ya fada mata halin da ake ciki,
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!....hope it's not bad?..." Fada mata komai yayi
"OK...ka kula daita...zan yiwa anty magana  don she's so angry..." Ta fada Mashi,
"OK nagode...." Ya fada yana juyawa don gani Wanda ke tahowa, ganin doctor ne yasa yayi saurin katse wayan tare da nufanshi
"Doctor... Ta tashi?..." Ya tambayeshi,
"Yes...pls waye mijinta?..." Shine tambayan da doctor yayiwa yazid Wanda har su ammi sunji Sadda kai ammi da family dinta sukayi while yazid ya kasa replying question din doc,
"Pls ya jikinta..hope  its not bad?....." Ya sake tambayanshi,,
"Not that bad...few injuries ne...." Ya amsa Mashi sannan ya sake cewa
"Waye mijinta?..."
"Ni....." Ya amsa Mashi kanshi kasa, kallon up and down doc yyi mashi, yafi minti biyu yana kallon shi inda shi kuma yazid bai yarda suka hada ido na,sai da ya gama kallon  sannan yace
"Follow me..." Ya fada Mashi atakaice tare da juyawa, jiki ba kwari yazid ya bi bayanshi,  wani office dake kusa da labour room doc ya shiga inda wata babbar mace ke zaune, yazid na daf da shiga yaji kaman dija na cewa
"Wayyo ammi cikina...wayyo mutuwa zanyi...."  Da sauri yazid ya shiga cikin office din yana cewa
"Kaman kukanta nakeji....pls what's happening?..." Ya fada cikin tashin hankali,
"Sit...." Matar dake cikin office ta fada Mashi tare da nuna Mashi seat dake opposite to Wanda ya banke dija.
"As a result of event daya faru..ta shiga labor...." Aikam sai ya dafa kai
"Labor doc...its seven months... Anya babyn zai rayu?...." Ya fada kaman zaiyi kuka, kallon juna sukayi don basu yarda He's responsible for the pregnancy ba...kawai suna ganin He's lying,
"Ai seven months na da...baka taba jin an haifi bakwaini ba?... Kawai saidai maganar incidents daya faru...amma da pregnancy is OK..." Inji matar, yazid shuru yayi ya rasa abun cewa,
"So zaa sayo kayan haihuwa...although bamu amsan irin wannan haihuwan but due to the circumstances we will help...." Matar ta sake fada Mashi, yazid dake zufa dag red eyes dinshi yayi ya kallesu
"Pls...Ku cire abinda ke cikinta....I don't think tana da strength da zata haihu...." Ya fada voice dinshi na cracking, kai matar ta girgiza,
"Its a government hospital.. We don't work that way..." Ta fada Mashi,
"Then zan kaita private hospital..." Ya fada yana mikewa, da sauri doc yace
"Ina da private hospital... In that case mu kaita chan..." Ya fada yana mikewa, daman already yazid tsaye yake, fita yayi ya sanar da ammi yanda sukace, fadawa doc din yayi suyi gaba yana biye dasu.
"Who will pay the bills..." Doc ya tambayeshi,
"Money is not the problem..." Inji yazid, cikin mota gidan su Salem ya shiga ya zauna baya, gudun kar dija ta kara  ganinshi ta rude, few minutes later aka fito daita zaune kan wheelchair, sai kuka taka tana cikinta, tana ganin ammi ta mika mata hannu, da sauri ammi ta mike taje inda ake turota ta rike mata hannu, duk ta manta da aladansu, babu abinda ke cikin ranta sai tausayin dija,
"Ammi cikina....cikina...marata..." Kawai dija ta take fadi, yazid na kallon ta daga inda yake zaune cikin mota, cikin mota doc aka sakata su ammi suka shiga suka bar wurin, yazid ya umarci driver yabi bayansu.

Kawai adua kawai yake kar wani abu ya sami dija he can bear loosing the child amma banda dija. Shi gani yake the child won't make it amma yana da hope cewa he will have any number of kids he want in the future
"Pls make it...." Ya fada under his breath, kiran mufidane ya shigo wayan, da sauri yayi picking yana cewa
"Baby am so sorry I lied... Kiyi hakuri....pls don't be offended..." Ya fada mata in a whisper don kwantar mata da hankali,
"What can I say...kawai kullum sai...." Bata idaba  ya katseta dacewa
"Baby ki yafemin....pls don't say anything OK..." Ya fada mata cikin sanyin muryan dayasan she can't resist,
"OK...yanzu kana ina?...." Ta tambayeshi, shuru yayi for a while sannan ya fada mata exactly abinda ke faruwa, cikin karfi hali tace
"To Allah ya bada saa...." Zai bude baki yayi magana yaji ta katse wayan. Murmushi kawai yayi.

Achan family house duk cikan dayayi sabida yan taro bai hana Hajiya karama kebewa da Hajiya babba ba, bayan  sun Shiga inda babu kowa, sai Hajiya karama ta fadawa Hajiya babba exactly abinda yazid ya fada mata, shuru tayi hawaye na taruwa idonta,
"Allah yasa kar dan yazo da rai....in yaso sai ya aureta batare da ansan exact abinda ya faru tsakaninsu ba...." Inji Hajiya babba, idanuwa Hajiya karama ta zaro
"Aa wallahi...Allah yasa yazo da rai...yo haka Allah ya kaddara....besides ni fa ban ga wani aibun abinda ya faru ba...ai duk Muslim na kwarai yasan kaddara...yazid dai ba dan iska bane balle ashe daman ya saba....kuma duk Wanda yaga yanda ya damu yasan ba halinshi bane...don haka ni dai wallahi yazo da rai koni da raineshi...." Ta fada in I don't care manner kuma she's serious,
"Wai ke ko kadan baki tunanin abinda mutane zasu ce?...." Inji Hajiya babba, shoulder ta daga
"Who cares....kowa na da nashi cockroach in thea  cupboard...so kowa yaji da abinda ya dameshi...." Ta fada sannan ta dafa shoulder Hajiya babba da Duk ta susuce
"Anty ki kwantar da hankalinki.... In mace CE ba sai taje waje aure ba balle ayi  mata surutu...cikin dangi zaayi mata miji...in kuma na mijine babu case don for as long as he's rich no body cares...." Yanda take magana yasa Hajiya babba dariya, dan hararanta tayi
"Wato ke har kin gama plan din komai...." Ta fada in a funny way,
"Yo me yafi raina..." Ta fada tana dariya.

Bayan kaman minti ashirin suka isa hospital, hospital din is not that big but it is unique and beautiful, da sauri nurses din wurin suka amsheta deyeka doc ya sanar dasu, fita yayi daga cikin motan yq nufi motan da yazid ke ciki, shima yazid fitowa yayi ya nufoshi,
"Zaa bada deposite of 80k...in an gama kafin a sallameta zaa bada balance of 70k,...150k muke cs anan..." Inji doc, yana kiran 80k yazid ya fiddo wayanshi, few seconds later ya daga kai yana yace
"Pls I don't have cash on me...kuna amsan  transfer?..."
"Yes...no problem..."
"OK...pls account number..." Inji yazid, nan take ya karanto Mashi ya saka
"Bank name pls..." Inji yazid, fada Mashi yayi, ko minti biyu baiyi ba yayi receiving alert na 170K, kallon shi doc yayi zaiyi magana yazid ya katseshi dacewa
"20k din na wanda nakeson ka duba min ne....that woman...."   Ya fada yana ammi data rafka tagumi,
"OK..." Doc ya fada ya juya da sauri. Ciki ya shiga, kafin ya shiga har an shanzawa dija dake ihu kaya, nan take aka hau aiki.

A waje kam ammi mikewa tayi don tasan bai kamata ace tana zaune nan dija ta haihu ba, magana tayi da yar uwarta  kan su tsaya da dija. Ahankali ta zo ta wuce inda yazid ke tsaye,
"Ina zaki kuma?..." Ya bi bayanya yana tambayan ta,
"Gida...." Ta amsa Mashi atakaice,
"Dan Allah ki tsaya  a dubaki..." Ya fada mata cikin sanyin murya, kai kawai ta girgiza sannan tace
"Aa...."
"To bari ya maidaki..." Ya fada yana juyawa, fadawa driver yayi a kaita inda ya dauko ta.

Driver zuwa yayi da mota inda take tsaye ta bude ta shiga. Yazid kallon agogon hannunshi yayi yaga kusan 5:30, sai lokacin ya tuna baiyi sallan asr ba.  Dan shiga cikin yayi yaga har lokacin doc bai fito ba, fita ya karayi yana tafiya yana tunani, har yaje bakin titi bai Sani ba saida wani mai mashin  ya kusa bugeshi sannan ya dawo sense dinshi. 

Bayan thirty minutes ya dawo direct ciki ya shiga ya nufi reception, nan wacce ke nan ta nuna Mashi office din doc, jikinshi na rawa ya shiga ciki, kallon face din doc yayi ko zai iya understanding halin da ake ciki, murmushi ya sakarwa yazid tare dacewa
"Congratulations... It's a boy..."

💜💙💚💛❤🧡

Sweethearts  kuyi hakuri am soooooo busy ne shiyasa kuke jina shuru. Sorry for waiting too long and pls don't forget to vote and comments.

NA CUCE TAWhere stories live. Discover now