part 20

7.1K 464 76
                                    

💙💚💛🖤💜❤
NA CUCE TA
💜💙🖤💚💛❤

®zuwairat(ummumaryam)

2⃣0⃣

Don't forget to follow and vote me on wattpad @ *ummumaryam29*

_Thanks sweetie, novel am feeling your love and affection_

Ahankali ya amsa ya ajiye gefe daya sannan ya dafa chest dinshi saboda ba karamin zafi yake ji ba, gani yake kaman romon naman zai hau mashi brain dinshi, idanuwanshi su kara ja, Hajiya karama hannu tasa ta dinga shafa bayanshi ahankali Har ya samu sauki.
"Pls kasha tea..." Tafada mashi ahankali, ba musu ya dauka ya sha zuwa rabi amma da gudu ya mike ya kama hanyan bedroom yana kakarin amai,
"NA shiga uku...wannan yaron nason saka kanshi cikin matsala...." Inji Hajiya karama, kafin ya shiga bathroom ya saki amai kasa yellow kaman mai rashin lafiya. Saida ya amai da Dan tea din daya sha ya mike ya shiga bathroom ya wanke bakinshi sannan ya taka ahankali ya dawo bedroom ya kwanta. Hajiya karama ce tasa asabe taje ta goge inda ya bata, yana kwance yana kallon ta tana aikin ta, asabe kam cikin tsoro Kawai take don yanda take ganin kaman zai kamata ya danneta.
Jikinta na rawa ta gama goge wurin Har zata bar wajen ya kirata, jikinta na rawa ta juyo ta kalleshi, ahankali ya daga manyan idanuwanshi ya kalleta sannan yace
"Pls..kinga....khadija sanda tazo nan gidan?..." Yafada ahankali,  surprise look ne kwance kan fuskar asabe,
"Ko baki ganta ba?.." Ya sake tambayan ta, da Sauri tace
"Tunda ta tafi..ba kara ganinta ba...." Ta amsa mashi muryanta na rawa,
"Ok..you can go..." Yafada idanuwanshi lumshe. Bayan kaman minti biyar ya mike ya fito tsakar gidansu masu gadi sai gaidashi suke amma banda wannan tsohon guda daya dake da masaniya kan abinda ke faruwa. Ko kallon su baiyi ba ya shiga part din mom dinshi, lokacin an shirya su marzuq da zasu school. Mom dinshi na tsaye rike da lunch box dinshi tana gyara mashi button din Riga, yana gani yazid ya tafi da gudu ya fada mashi, bayanshi Kawai yazid ya shafa bai daukeshi kaman yanda ya saba daukan shi ba cos  da kyar yake daukan kanshi. Mom juya baya tayi yayi saurin durkusawa gabanta
"Mom...pls....forgive me...." Yafada hawaye na taruwa idanuwanshi, kokarin wucewa tayi amma ya rike mata kafa,
"Pls ki yafemin..." Yafada yana fashewa da kuka dukda muryanshi bai fita sosai . marzuq tsayawa yayi yana kallon su, horn din motan da akayi yasa marzuq barin su cike da tambaya cikin ranshi abinka da inquisitive child. Mom kwace kafanta tayi
"Laifin me kayi min...its your life.. And you have decided to live it the way you want... So ni babu ruwana...." Tafada tana kokari barin wurin, da rarrafe ya tare gabanta,
"Wallahi..mom ba halina bane...kaddara ne ya fadamin....ban taba kama hannun mace ba..."
"Amma Har ka Iya raping yar yarinya ..." Mom ta katseshi,  yana girgiza kai yana cewa
"Mom sharrin shaidan ne...am sorry.. Pls...." Yafada cikin matsanacin kuka, mom goge hawayen face dinta tayi ta fixge kafanta daga hannun shi ta bar wajen, ahankali ya koma ya zauna kasa  yacigaba da kuka, kofa aka bude ya daga kai ya ga mufida ce tsaye itama Sam fuskanta babu walwala, amma ganin yanda yazid ke kuka yasa ta saki ranta, ahankali ta karaso wajenshi itama ta zauna nan kasa, kura mashi ido Kawai tayi tana mamakin irin wannan kaddara.
"Baby am sorry... Khadija is pregnant..." Yafada mata cikin kuka, dukda zuciyanta na tafasa hakan bai hanata tallabo face dinshi ba,
"Stop crying... Haka Allah ya kaddara..."
"Baby NA CUCE TA...NA zalunceta...she's too young for this...." Yafada cikin kuka, baki mufida ta tabe
"But she's not young for you to sleep with... Yanzu dai zaa Haifa maka shege kafin ka samu na halal..." Tafada sounding very angry,
"Ba laifina bane...laifin kaddara ne...." Dan guntun tsoki taja,
"Da wannan kaddara yasa kaje kayi sata an harbeka dayafi maka gaskiya..." Ta fada atakaice ta mike ta barshi nan zaune, yana nan zaune yana tunanin halin mufida, one second she nice the other second she's mean. Ahankali ya mike ya shiga dakin da mom dinshi ta shiga, tana zaune bakin gado tana kuka, ya karasa gabanta
"Mom am sorry... Pls..." Banza tayi dashi ta cigaba da hawaye abinta
"Mom zan tafi....zanje Neman ta...." Yafada ahankali yana hawaye, mom dai batace uffan ba. Yana nan durkushe gabanta yana kuka tana kuka Har Salem yazo suka bar gidan. Yanayin shi ba karamin tadawa Salem hankali yayi ba don gani yake kaman wani mugun abu na Iya faruwa da best friend dinshi.
Yana tuki ya juyo ya kalli yazid daya rumtse idanuwanshi yana Allah Allah su isa katsina yace
"Guy wai ka manta kaddara ne?... Duk kabi ka damu kanka saboda wannan abun...we can't stop destiny... What will be will always be...ka sassautawa kanka pls...." Inji Salem, yazid dai baice kala ba Kuma bai bude idanuwanshi ba. Kusan a haka suka isa garin katsina around 10:30, amsan address din yayar Hajiya karama yayi yaga goruba road da number gidan, baisan goruba road ba don wurin grandparents dinshi Kawai yake zuwa
"Bari muje family house dinmu don mu nemi wani cousins dina su rakamu...." Salem ya fadawa yazid, ahankali yazid ya girgiza mashi kai,
"No pls...zaa bata mana lokaci...Kawai Bari in kira small mom ta fadawa sister dinta muna wajen round mai kwarya don ta aiko driver dinta yayi directing dinmu...." Yafada ahankali Sannan ya fiddo wayan shi yayi dailing number Hajiya karama ya sanar daita.

NA CUCE TADonde viven las historias. Descúbrelo ahora