part 19

5.9K 312 11
                                    

💙💚❤🖤💛💜
NA CUCE TA
💙💚💜🖤💛❤



®zuwairat( ummu Maryam)

1⃣9⃣


Yana tuki suna hira kaman babu abinda ya taba hadasu, yazid kam ban da tunani babu abinda yake, Wai shi yazid ne zaiyi fathering da out of wedlock, har yanzu tamkar mafarki yake don he can't believe it, sai yanzu ya yarda don't take yourself to be perfect, don't feel too perfect cos in har baka bar duniya ba to baka wuce jarabawa ba,
"Ganawa kaddara...." Tafada kasan makoshinshi Wanda yasa mufida dake lumshe swollen eyes dinta kaman zatayi bacci ta kalleshi, shima kallon ta yayi ya sakar murmushin karfin hali,
"Am sorry I hit you..." Yafada kaman shine main problem dinshi,
"Nace ya wuce..." Tafada tana rike hannun shi dake kan staring, duniyar tunani ya kara fadawa, yanzu ya yarda cewa not all that glitter is gold,  don before gani yake most of his friends are corrupt with dirty different characters amma duk cikin su babu mai shege sai shi, tuna how young khadija is yayi, shi har yanzu gani yake kaman dream don a nashi tunanin she can't get pregnant. Yasan yanzu duk zaa tsaneta gidansu, yasan she will be stigmatized, he can't wait for tomorrow, tamkar ya jawo gobe yake ji, yanzu baiji kunyan kowa kan wannan maganar, haka Allah ya kaddara mashi kuma he will take it in good faith. Sai around after 11 sukaiso gidansu, part dinshi suka shiga ta ajiye bag dinta Sannan ya kama hannun ta sukayi bangaren Hajiya babba, yasan its late amma yasan for sure mom dinshi bazatayi bacci ba. Kofan falo ya bude suka shiga yana rike da hannun mufida, bakin kofan bedroom dinta sukaje ya radawa mufida tayi sallama, tanayi mom ta amsa mata,  sakin hannun ta yayi ya koma baya don har yanzu basu kebe da  mom ba tunda aka fara wannan magana Sannan he's so ashamed of himself da bazai Iya hada ido daita ba. Falo ya koma ya zauna ya dafe kai yana counting seconds to dawn.

Mufida NA shiga mom ta daga kai ta kalleta da idanuwanta da suka chanza tamkar ba nata ba, tana ganin mufida tayi saurin goge face dinta don ko kadan bata dau muryanta ba.
"Daughter kece da wannan Daren?..." Ta tambayeta ahankali, kan mufida kasa tace
"Eh..." Sannan ta durkusa ta gaida ta, amsawa tayi
: Cikin sanyin murya tana nuna mata wurin zsama kusa daita, ahankali ta zaune gefen ta, itadai mufida tunanin abinda ke damun Hajiya tayi sai kuma ta tuna kilan sai yanzu suka San abinda  yazid ya aikata not knowing they is more to it. Cikin rawar murya Hajiya tace
"Kiyi hakuri kinji?... Komai mukaddari ne...haka Allah ya kaddara... Ki rike mijinki hannu bibbiyu..." Tafada tana fashewa da kuka, itama mufida fashewa tayi da kuka,  ahankali Hajiya ta jawota jikinta suka bude sabon babin kuka kaman anyi mutuwa.
"Bansan irin wannan kaddara ba...ko sau daya ban taba kama yazid da wata karamin laifiba sai Kawai Ace yayi wa yar karamar yarinya ciki...." Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, gaban mufida yayi mugun faduwa dajin ciki, ahankali ta daga kanta daga shoulder Hajiya ta kalleta, cikin kuka Hajiya ta kalleta, surprise look dake face dinta ya tabbatar mata batasan wannan zancen ba kuma bataso ace ita ta fara sanar mata ba.
"Mom ciki gareta?..." Ta fada cikin kuka, Hajiya dafe kai tayi tana kuka,
"NA shiga uku...Hajiya gidanmu zani...ban iya zama dashi....." Ta dinga fada kaman wata zautatta, dafa ta Hajiya tayi tana girgiza mata kai,
"Don't say that....hannun ka bai rubewa ka yarda...mijinki ne kuma bazaki kishi saboda jarabawan Allah ba...kiyi hakuri wata rana zakiji kaman ba a taba hakan ba..." Tafada tana shafa bayanta, mufida kukan bakin ciki da kishi Kawai take, watanta biyar da yazid ko batan wata bata tabayiba, kullum tana fadawa mom dinta rashin batan watanta amma sai mom dinta ta fada mata its nothing wai itama saida tayi shekara uku Sannan ta samu cikin mufida, amma yanzu shine wata zata rigata haifawa yazid da ko ya
"Shege ne..." Ta fada cikin ranta, hakan yasa ta Dan saka ranta a inuwa amma still bata bar kuka ba. Tana cikin kuka bacci ya dauketa nan kan gadon Hajiya. Yazid kam yanda ya ga dare haka yaga rana. Haka Hajiya babba da Hajiya karama ma duk basuyi bacci ba.

Abangaren dija kam nan asibiti ta kwana inda yan waiting ke tsayawa, Allah ya taimaketa babu Wanda ya damu daita, kowa ta kanshi yake duk suna jiran yan uwansu su haihu lafiya kuma har garin Allah ya waye baa rasa mutane wajen ba, dija batayi wani baccin kirki ba saboda kuka da cizon sauro, tana fara ganin hasken gari mike ta dauki bag dinta, banda fitsari babu abinda ke damunta, kusa da wata mata dake zaune taje
"Dan...Allah... Ina.. Ake...fitsari?..." Ta tambayeta matar daga kanta tayi ta kalleta from head to toe tana mamakin me yasa zaa zo da irin wannan karamar yarinyan wajen haihuwa,  wata kofa ta nuna mata batare data ce mata uffan ba. Da Sauri dija ta shiga cikin wurin rike da bag dinta don rike taje da bag dinta tamkar her life depends on it. Wurin babu laifi its neat, durkusawa tayi ahankali saboda yanda wani abu ke tokare mata maranta, tana fitsari tana wash, saboda yanda fitsari bai zuwa da yawa sai zafi da take ji ba don komai ba sai don tun jiya take jin fitsarin amma batayi ba sai yanzu
Tafi minti goma nan durkushe, for the very first time sai taji motsin abunda ke cikinta, dafe cikinta tayi don kara tabbatar da abinda taji amma sai komai yayi still. Kallon tap dake running tayi sai tayi tunanin why not tayi wanka tunda batasan kowa ba balle ta samu inda zatayi wanka later in the day, ajiye bag dinta tayi ta leka waje don tabbatar babu mai jira Sannan ta koma ciki ta kulle kofan, rataya bag dinta tayi Sannan ta cire kayan cikinta, tsayawa tayi tana kallon cikinta. Jikinta ta kalla da tsawun dukan ammi dake kwance bisa skin dinta. Kuka ts farayi. Tana kuka har ta gama wanka amma bada sabulu ba. Kayan data cire ta maida, bude bag dinta tayi ta koma gefe ta fiddo kudin da ammi ta watsa mata da yawa amma babu kudin kirki cikin su, duk yan biyar, goma, ashirin ne babban kudin dake ciki shine Dari biyu,  ta kusa hour tana counting dinsu. Sun kai kusan dubu sha biyar, arranging dinsu tayi according to girmansu daman abinda ta sabayi kenan tun a gida. Saida ta gama ta fito tana tafiya ahankali. Bakin asabitin da akwai masu saida kayanci kala2 irin su taliya, kosai, koko da sauran su, wurin wata mkata dake soya kosai da koko ta nufa ta ajiye bag dinta ta zauna sama Sannan tace a bata koko da kosai, daman jos ba kaman sauran garuruwa yake ba, babu Wanda ya damu da ita. Nan ta zauna taci ta koshi Sannan ta koma gefe tana kallon masu harkokinsu.
Tagumi tayi tana tunanin abinda zai biyo baya, ammi ta fado mata ga rai,
"Yanzu ammi ta yafeni kenan?... Yanzu ammi bata Sona kenan?... Yanzsu ammi ta cire ni cikin yaranta kenan?..." Ta dinga tambayan kanta cikin ranta, Dan take baki tayi hawaye suka fara gangaro mata, da Sauri ta da hannu ta goge face dinta.

NA CUCE TAWhere stories live. Discover now