na cuce ta 36

8.3K 474 62
                                    

🧡💜💙💚💛❤
NA CUCE TA
💜💙💚💛❤🧡


®Zuwairat (ummummaryam)


3⃣6⃣



_Follow me on:_

*Wattpad @ummumaryam29*

*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*

*IG: zuwairatummumaryam*

*Website:Www.ummumaryam.com*

*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*

*Snapchat: ummumaryan29*


*Wishing all my beautiful people happy sallah, Allah yasa dukkan ibadun mu* *karbabbune, Ameen*



Ahankali ya bude kofan yana aduan Allah yasa Matan da suka rakota sunyi bacci, yana shiga falon luckily mata biyar ya gani kwance kasan tiles suna bacci, kaman barawo ya taka yana aduan Allah yasa tana inda she's suppose to be, yana bude kofan bedroom daya fi dukkan sauran haduwa ya ganta kwance kasa sannan babu kowa, da Sauri ya shiga kaman Mara gaskiya ya maida kofan ya rufe, ya yazo ya zauna gabanta bata san ya shiga ba, zama yayi yana kallon yanda take sauke ajiyan zuciya kaman wacce tayi 360 race.
Kawai sai ya saki murmushi yana lumshe eyes kaman Wanda aka yiwa albishir da aljanna. Kallon yanda take shessheka  kawai yake don ya san ba karamin kuka tasha ba, kallon hannunta dake kan maranta yayi., ahankali ya mike  bayan ya ajiye drugs da abinci daya shigo dasu. Cikin saddo ya bude kofa ya fita yana tafiya ahankali har ya isa kitchen, kara kallon kitchen din yayi yana tunanin ya gan dija tana amfani da kayan kitchen din don ko shi da kanshi bai san amfanin wasu kayan ba don he's not use to kitchen. Wani cup ya. Dauka cikin kayan da aka jera ya kai sink ya wanke sannan ya dauki plate shima ya wanke sannan ya fito. Kara shiga dakin still tana kwance yanda take. Zama yayi ya cika cup da milk sannan ya fiddo ragolis water ya ajiye gefen milk din, plate ya dauka ya zuba roasted meat, hannu ya daga kaman ya tadata amma baisan abinda zai tada mata hankali, yafi minti biyar yana daga hannu amma yana rasa courage, amma ganin wankin hula zai kaishi dare yasa yayi karfin halin dan taba kafanta, aikam a firgice ta farka tana mazurai, kallon Wanda ya tadata tayi da kyau ta tabbatar yazid ne, nan take ta fara ja da baya tana yarfe hannunta at the same time tana fashewa da kuka
Cikin kuka ta fara cewa
"Wayyo Allah na....wayyo ammi na shiga uku..." Tafda sounding very tired and fed up, sai ka take da baya while shikuma yayi kuri ya kura mata ido babu abinda yake sai kallon ta. Dija najin ta kai bango ta kara volume din kukanta. Yazid ji yayi kaman ya rikota amma yasan it will only make it worst. Gyara zamanshi yayi tare dayin ganmo da legs dinshi duk eyes dinshi kan ta,
" tashi ki shiga bathroom ki wanko bakinki..." Ya fada sounding formal, da sauri ta girgiza kai batare datace Kala ba, kuka tacigaba dayi
"Nace ki shiga bathroom ki wanko bakinki..." Yafada da karfi, aikam da sauri ta mike tashiga bathroom, tana shiga ya fara dariya yana girgiza kai, ya gano one of her weakness, which is tsoro, yasan tamkar monster yake wajenta and he's going to use it to his advantage, dija na shiga ta dafa bathtub tana kuka, tana mamakin duniya bayan duk abinda yayi mata amma sun hadata aure dashi, cikin kuka ta fara cewa
"Don sunga bani d baba....don Abba ya mutu...shiyasa sukayi min haka..." Tafada cikin kuka, ji tayi muryan yazid nacewa
"Ina jiranki...." Da sauri ta dubi toothpaste rack and dispenser ta dauki brush ta zaro toothpaste ta zuba jikinta sai rawa kawai yake, cikin sauri ta wanke bakin ta fito face dinta sharkaf da hawaye, daga kai yayi babu faraa sosai kuma fuskanshi ba daure yake ba, tsaye tayi bata da niyyan zama
"Ki zauna mana...." Yafada mata, da sauri ta saki jikinta ta zauna sai kuma ta rike maranta, mikewa yayi ya dauki milk da plate ya ajiye gabanta.
"Bissimillah....." Yafada mata tare da nuna abubuwan dake gabanta, da sauri ta girgiza kai tana kuka,
"Kinason ranki ya baci?..." Ya tambayeta, da sauri ta sake girgiza kai,
"To ki cinye yanzu nan...." Bai idaba ta fara cin naman tana kuka, duk cin da zatayi sai tears dinta ya diga, har ta koshi amma tana tsoro daina ci, gani yayi tana Neman cinye kaza daya kuma da alaman ta koshi amma bata Iya dainawa
Kallon yanda take tauna nama kaman paper yayi, kauda kai gefe yayi ya saki murmushi cos he's enjoying the moment don yasan Yana daga cikin abinda zai dinga zolayanta dashi in future, dauke plate din naman yayi ya maidata gefe sannan ya dauki cup of milk ya ajiye gabanta,
"Bissimillah..." Ya sake fada mata, tana shesssheka ta dauki cup din tana sha tana kuka at the same time tana tunanin halin d zata fada yau don tasan bazai fasa yi mata abinda yayi mata da ba, har yanzu bata bar tunanin dalilim dayasa ammi ta yarda aka hadata da irin wannan mutum ba, ajiye empty cup din tayi tare da goge bakinta da bayan hannunta, yazid daukan ledan drugs din yayi ya bude ya ballo wayanda zatasha ya mika mata, ganin yayi bata amsa ba, hannu yasa ya kama right hand dinta Wanda yasa dija kara volume din kukanta, murmushi ya kara saki enjoying the tenderness and warmth of her skin, ajiye drugs din yayi cikin hannunta ya dauko ruwa daga cikin ledan daya shigo daita ya bude ya mika mata, jikinta na rawa ta amsa ta juye dukkan Maganin cikin bakinta ta zuba ruwa ta rumtse ido ta hadiye, mikewa yazid yayi ya shiga bathroom ya hada mata ruwan wanka ya fito,
"Ki tashi kije kiyi wanka...." Ya fada sounding so commanding, da sauri ta mike kaman Kazan
Da aka tsoma cikin ruwa ta shiga bathroom, tana kuka tana cire kayan jikinta, kallon kofan tayi don gani take kaman zai shigo, bathtub ta shiga don already tasan amfani shi tun sanda tayi aiki gidansu yazid. Jikinta na rawa ta gama ta fito ko goge jikinta batayiba ta maida kayanta ta fito kanta kasa sai hawaye ke diga,
"Ko pump albarka...." Yazid ya fada yana kallon  yanda tears ke fita daga eyes dinta.  Yazid mikewa yayi daga inda yake zaune ya je bakin gadon ya yaye duvet dake rufe da gadon sai wata bedsheets ya bayyana daga kasa
"Zo ki kwanta...." Ya umarceta, nan jikinta ya fara shaking to the extent yana ganin yanda duk jikinta ke rawa, yasan he has ruin her life and he promise himself to make things right again, he will do anything to make her trust and rely on him, duk tafiyan da zatayi sai jikinta yayi rawa, ajiye duvet din yayi ya nufeta, bata ankaraba ya dauketa, wani irin kuka ya kufceta mata
"Wayyo na shiga uku....ammi...." Tafada cikin matsanacin kuka, kasa tafiya yayi ya tsaya rike data kaman babu komai hannunshi, kurawa swollen and tired eyes dinta ido yayi yana kallon yanda tears ke rolling,
"Dan Allah..... Ciwona....ciwo gareni....kayi hakuri....." Tafada sounding so tired and afraid, idanuwanshi ne suka ciko da tears, ahankali ya fara girgiza mata kai,
"Khadija.... Kiyi hakuri...." Bai idaba tayi saurin daga Mashi kai tana kuka
"Abinda ya faru tsakanina dake kaddara ne....dan Allah ki yafe min....nayi maki alkawarin bazan cutar dake ba....bazan karayi maki abinda baki raayiba....duk abinda kikeso zanyi maki...." Duk maganar dayake babu abinda take sai daga Mashi kai cike da tsoronshi with her eyes closed, ahankali ya taka zuwa bakin gadon ya kwantar daita, bargon ya dauko ya rufa mata, zama yayi bakin gadon yana yana kallon ta, bayan kaman minti five ya mike yayi pecking goshinta sannan  rage wutan dakin ya fita feeling so happy,  cikin motanshi ya koma ya dauko dayan ledan ya kulle motan ya nufi part din mufida.

NA CUCE TAWhere stories live. Discover now