MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohAssalamu Alaikum
Ina mai ba makaranta MYM hak'uri akan ba zaku dinga samun post d'in MYM kullum ba saboda wasu yan dalilai. Amma In shaa Allah idan nayi settling zaku jini kullum. Thnx y'all for d love..NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA UKU
Sanyin asuba ne ya farkar da ita, da sauri ta mik'e ta nufi hanyar toilet, alwalla ta yi ta fito ta kabbara sallah, bayan ta idar ta dad'e tana azkhar. K'arfe bakwai dai-dai ta fito parlour, shiru parlourn yake kamar ba kowa gidan, tsintsiya ta d'auko ta share tayi mopping, tana gamawa ta nufi kitchen nan ma sai da ta gyara tsaf kana tayi turaren wuta, tana gamawa ta nufi haraban gidan, ta fara shara kenan mai gadi ya taso da gudu.
"Uwar d'akina mi zan gani haka? Dan Allah ki bari zan share da na gama jin labarai."
"Karkadamu Baba zan share kaje ka huta"
"Kinaso abinci na ya k'are a gidan nan Daga yau ne?"Ido ta zaro tana fad'in
"Akanmi abincinka zai k'are?"
"Akan kina shara mana wanda ni ya kamata ace na share haraban gidan nan bake ba, ko so kike Mohammed ya koreni daga aiki yau?"
"Bazai koreka ka ba saboda ya ganni ina shara, Daga yau ba zaka k'ara shara ba Baba nice zan din gayi."
"Miyasa?"
Umurni ne na Mummy"Tana gama fad'in haka ta duk'a ta cigaba da share haraban gidan, girgiza kanshi ya yi ya koma bakin k'ofar shi yana mai tausayama Husna akan irin azabar da ake mata a cikin gidan.
Tana gama sharan, ta koma cikin gida dan d'ora masu kalaci, kicin ta nufa ta fere dankali, mai ta d'ora a wuta ta fara soyawa, tana ga mawa ta soya kwai, ta dafa ruwan shayi da yaji kayan had'i. K'arfe tara dai-dai ta gama komai ta kawo su dainning ta jera.
Jin takun tafiya yasa ta waiga dan ganin waye, tana juyawa suka had'a ido da Mummy, da sauri ta zube k'asa.
"Mummy Ina kwana?"
"Lafiya"
Ta bata amsa a dak'ile, tashi ta yi ta nufi d'akin Mummy dan ta gyara, tana shiga taga d'akin anyi kaca-kaca dashi, girgiza kai tayi tana fad'in
"Sai kace yara ne suka kwana a d'akin."Ba yanda ta iya, haka ta gyara d'akin cikin d'an k'ank'anin lokaci ta gama komai ta fito daga d'akin.
Ji tayi ta bugi wani abu, d'agowa tayi dan taga abinda ta kaima karo, ganin shi tsaye yana mata kallon k'ask'anci yasa ta fara kyarma.
"Dan Allah kayi hak'uri bangani ba."
"Ke dabbar ina ce da baki duba gabanki?"Shiru tayi tana kyarma.
"Dan ubanki ba da ke nake magana ba?"Kafin ta bashi amsa, ya zaro belt bugunta ya farayi ta ko ina, ihu take tana bashi hak'uri amma bai saurareta ba. Da sauri ya k'araso wajen dan ganin kukan mi ta keyi, ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba ganin irin bugun da Muhamud ke mata ga Mummy zaune tsakar parlour bata ce komai ba. Han kad'a shi yayi gefe guda.
"Kai wane irin azzalumi ne? Anya kuwa kana da imani Muhamud?"
"Dan ubanka ni kake cema azzalumi?"
"Na fad'a ai zaluncin kayi mi ta maka da zaka kamata kana bugu haka sai kace ka samu jaka."
"Mohammed yau ni kake kira azzalumi saboda na hukunta Husna akan laifin da ta man? Duk Ina soyayyar dake tsakaninmu duk ina k'aunar da kake man? Duk ina shak'uwar dake tsakaninmu?"
"Zakaji fiye da haka In dai zaka cigaba da k'untata ma Husna, wallahi ka sani a yau nafi kowa tsanarka saboda mugayen halayenka."
"Dan ubanka d'an uwanka kake ma wannan mugayen kalaman?"Mummy ce ke magana cikin zafin rai.
"Mummy zakuji fiye da haka, in dai ba zaku daina takura ma Husna ba, wallahi idan ba kuyi wasa ba zaku nemeni ku rasa."
Yana gama fad'in haka ya wuce, yabar cikin parlour cikin zafin rai, breakfast d'in da baiyi ba kenan ya fita. Ba k'aramin tashin hankali Mummy ta shiga ba da taji kalaman Mohammed, dan tasan zai iya aikata abinda ya fad'a.
Mik'ewa tayi ta nufi d'akinta da gudu, bisa gado ta fad'a tayi rub da ciki, Sabon kuka ta fashe dashi tana tunanin rayuwarta a da, da kuma yanda yanzu lokaci d'aya rayuwarta ta sauya.
Juyawa yayi shima ya bar parlour, Mummy na kwala mashi kira amma in da take bai kalla ba saboda b'acin rai. D'akinshi ya nufa, yana shiga ya banko k'ofar, za gaye d'akin ya kamayi yana sabbatu.
"Yau ni Mohammed ke kira azzalumi marar imani kan Husna? Tabbas daga ita har shi sai sun raina kansu, wallahi Husna sai na maki abinda zaki tsani kanki sai na maki abinda sai kin buk'aci mutuwarki da rayuwarki, a dalilinki d'an uwana dana fi k'auna sama da kowa yake kirana da Mugu Azzalumi, wallahi sai kin biya, Sai na nuna ma duniya ke ba kowa bace ba."
Haka ya dinga surutu shi ka d'ai cikin d'aki...K'arfe hud'u Moh ya shigo gida, d'akin shi ya nufa, yana shiga ya zube bisa gado ko takalmi bai cire ba, abinda ya faru d'azu ya dinga dawo mashi a kwakwalwa tsanar Muhamud da Mummy shi ya ke k'arayi.
Zumbur ya mik'e, d'akin Husna ya nufa dan ganin halin da take ciki, ya na shiga d'akin ya fara kiran sunanta.
"Husna! Husna!! Husna!!"Sunan ta yake kira, amma bata amsa ba. Fitilar d'akin ya kunna, haske ya gauraye d'akin. Can k'arshen gado ya ganta ta lullub'e da bargo ga kyarma ta nayi.
Da sauri ya k'arasa bisa gadon ya kware bargon, hannunshi ya kai kan goshinta zafin da ya ji goshin yayi ba k'aramin firgita shi ya yi ba.
"Baby Sis baki da lafiya shi ne baki kirani ki ka gayaman ba?"
"Ya Moh ka taimakeni zan mutu kaina kamar zai cire."
"Bazaki mutu ba Baby Sis."Yana gama fad'in haka ya tashi da sauri yayi waje yana kwalama, Mummy kira. Zaune ya tarar da ita parlour ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya tana girgizawa.
"Mummy Baby Sis ce ba lafiya gata can tana numfashi da kyar."
"Ubanmi zan mata to? Tama mutu mana, ai da mutuwa tayi sai nafi kowa murna, wallahi sai nayi maganinka saboda yarinyar nan, sakarai wanda bai san ciwon kanshi ba, matsa kaban wuri tun ban tsine maka ba."Please don't forget to vote comments and share to ur love one's
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Mystery / ThrillerLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...