BABI NA BIYAR

2.1K 226 6
                                    

MARAICIN 'YA MACE

               Rubutawa
                     Phirdaucee Jeeboh

Kuna ina mutanen kirki Khadejah Candy (Deedee) Husna Mai Sharif nd Meelah Adeel wannan page d'in na kune na baku shi kyauta. I love you y'all fisabilillah.

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA BIYAR

   Da sallama ya shiga d'akin, kwance take bisa gado tana bacci, numfashi take fitarwa akai akai k'arasawa ya yi gabanta, kallon ta ya yi ya girgiza kai.
"Allah ya baki lafiya Baby Sis."

K'ura mata ido ya yi yana kallonta lokaci guda duk ta rame, tayi fari, shafa kanta ya yi ya bar d'akin yana k'ara tausaya mata irin rayuwar da ta tsinci kanta, wanda a baya ba haka take rayuwa ba..

Ganin ba kowa parlour ya nufi d'akin Mummy, da sallama ya shiga d'akin wuri ya samu kusa da ita ya zauna, kanshi ya d'ora bisa cinyarta. Duk yanda take jin haushin d'an nata bai hana taji tausayin shi ba. Shafa kanshi tayi tana mashi magana.
"Auta lafiya?"

Hawayen da suka gangaro mashi ya goge dan bai san ta gane yana kuka.
"Lafiya lau Mummynah."
"Ina fa lafiya na ganka kayi wani iri."

D'agowa ya yi ya kalleta.
"Mummy ulcer ya kama Baby Sis kuma cronic, Doctor ya tabbatar mani da cewa idan har ta cigaba da zama da yunwa zata iya rasa ranta saboda tana neman tab'a mata yan hanji, mummy ta ya akai Husna ta kamu da ulcer haka? Ban d'auka zaki mata horon yunwa ba saboda ba halinki bane ba, Mummy kin manta Husna amanace wajen mu Mummy kin manta Allah zai tambayemu akan yanda muka rik'e amanar da ya bamu Mummy kin manta Husna marainiya ce ba  ta da kowa sai mu, Mummy kin manta Husna jininmu ce, Mummy Miyasa ba zaki canja ba akan ak'idarki wanda Allah bai so, dan Allah Mummy ki a je komai ki rungumi Husna a matsayin d'iya wallahi baza kiyi danasanin rik'e Husna d'iya ba, zakiyi alfahari da ita."

Kukan da ya ci k'arfin shine ya sa yayi shiru, k'afarta ya kama yana kuka.
"Kiyi hak'uri ki gafarta man akan abinda na maki, banyi komai da niyya ba, sai dai ina tsoron Allah ka da ya kamaki akan marainiya."

Sakin ta yayi ya bar d'akin yana hawaye.

Sosai jikin Mummy ya yi sanyi, dan maganganun Moh sun shigeta.
"Tabbas nasan gaskiya Mohammed ya gaya mani, kuma ba zan k'ara hana Husna abinci ba, sai dai ba zan iya daina tsanarta ba saboda wasu dalilai."
Haka ta dinga surutu ita ka d'ai cikin d'aki.

Yana fita d'akin Husna ya koma, yana shiga tana farkawa, da sauri ya k'arasa gabanta da taimakonshi ta tashi zaune.
"Ya Moh zan shiga toilet."
A hankali take magana dan muryan bata fita sosai, k'arin ruwan ya cire mata, ya kamata har bakin toilet ya kai ta.
"Zaki iya shiga ko?"
"Eh zan iya"
Ta bashi amsa. Tana shiga toilet, ya dawo ya gyara gadon tsaf, yana gama gyaran gadon dai-dai tana fitowa daga toilet, a hankali ta k'araso gabanshi.
"Da ka bari na gyara."
D'agowa y yi yana hararanta.
"Ta ya zakiyi aiki ko har kin samu sauk'i?"
Dariya tayi ta zauna bakin gado,
"Ya Moh zanyi sallah."
Carpet  ya shin fid'a mata wardrobe d'inta ya bud'e ya d'auko mata hijab ya mik'a mata, karb'a tayi ta saka ta kabbara sallah. Fita yayi ya nufi kitchen, tea ya had'a mata mai kauri, da sallama ya shiga d'akin dai-dai ta sallame sallah, zama yayi kusa da ita ya mik'a mata kofin tea.
"Ya Moh na k'oshi banjin yunwa."
Fuskar shi ya d'aure kamar bai tab'a dariya ba.
"Zaki karb'a ko sai na tattakaki, kinsan irin bala'in da kike neman jefa kanki ne? Ki karb'a ki shanye shi tas in ba haka ba wallahi sai ranki ya b'aci kuma ba zan k'ara shiga harkanki ba sai su ya Muhamud su ji dad'in ta kura maki."

Tun da take dashi bai tab'a yi mata fad'a ba, yau gashi har tsawa ya mata, hawaye ta goge.
"Kayi hak'uri idan na b'ata maka rai."

Jikinshi ya yi sanyi, shi kanshi bai ji dad'in yanda ya mata fad'a ba kuma bata da lafiya, amma idan ba haka ya mata ba yasan ba sha zatayi ba. Bai ce mata komai ba ya mik'a mata cup d'in ba musu ta karb'a ta kai bakinta, sai da ta shanye tas kana ta mik'a mashi cup d'in tana zumburo baki? Dariya ta bashi.
"Kallarki k'atuwa ko kunya bakiji wai kuka zakiyi, yarinya ai aure za'a maki kwananan, idan kin haihu kin daina shagwab'a ko zakiyi gaban yaranki ne?"

Pillow ta d'auka ta jefeshi, kaucewa ya yi yana dariya. Ruwa ya bud'e ya mik'a mata, magani ya b'allo ya bata ba musu ta karb'a ta shanye, tana gama sha ya mai da mata k'arin ruwa.
"Ki kwanta ki huta, Allah ya k'ara lafiya."
"Ameen."
Ta bashi amsa, wuta ya rage mata ya kunna mata AC ya ja mata blanket, yana fita ya ja mata k'ofar.

"Allah ya saka maka da alkairi Ya Moh yanda kake san ka ganni cikin farin ciki, kai ma Allah ya had'aka da wadda zata saka ka cikin  farin ciki har k'arshen rayuwarka, Allah ya kawo ranar da zaka nemi wani abu wuri na ni kuma ko da yana nufi shine k'arshen rayuwata zan maka shi dan ka samu farin ciki."
Haka ta dinga surutu ita ka d'ai, daga nan har bacci yayi gaba da ita.

Hanyar corridor suka had'u da Muhamud, rab'ashi ya yi zai wuce, hannunshi Muhamud ya rik'e yana murmushi.
"Ya mai jiki?"
Da sauk'i."
Ya bashi amsa a tak'aice
"Allah ya k'ara sauk'i."

Zare hannunshi ya yi sai da ya kai k'ofar d'akin shi ya bashi amsa.
"Ameen."

Wani shu'umin murmushi Muhamud ya saki, ya nufi d'akin Mummy.

Yana shiga d'aki ya fad'a kan gado yana mamakin yanda Muhamud ke tambayarshi jikin Husna.
"Ko dai wani abun Muhamud ke shirin aikatawa ne? In shaa Allah koma miye bazai samu nasara ba."
Shi ka d'ai yake surutunshi, da haka har bacci ya d'auke shi..

Da sallama ya shiga d'akin Mummy, amsa mashi tayi jiki ba kwari.
"Mummy Lafiya?"
"Lafiya lau Muhamud, mi kagani?"
"Naga kinyi wani iri ne "
"Bakomai."
"Mummy ina jin yunwa fa, Husna ba tayi abinci bane ba."
"Baka san bata da lafiya ba?"
"Ops na manta fa."
"Bari naje na dafa mana."
"Mummy da kanki? Bari dai na je na mana take away."
Bai tsaya jin mai zata fad'a ba ya bar d'akin...

Don't forget to vote comments nd share.

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now