MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
Parking yayi daidai in da take tsaye, fita Inaaya tayi tana murmushi.
"My runaway friend sai Ina?"Daga baya ta jiyo muryanta, da murmushi ta juyo tana fad'in.
"Inaaya zaki fara ko?"
"Ai gaskia na fad'a yanzu dai Ina zaki?"
"Alqalam zani kinsan na samu admission, shine zanje nayi registration."
"Kinga kuwa dama School zani sai mu wuce."
"Ah ah Inaaya karna sa kiyi latti."
"Wane latti Ina cewa duk hanya ce tun da yar'adua zani sai dai idan ba zaki je ba kawai dama ai kin saba man wulakanci"Dafa ta tayi tana murmshi.
"Yi hak'uri Hajiyanah abun bai kai na fad'a ba muje."Da murmushi Inaaya ta bud'e mata bayan mota ta shiga.
Da sallama ta shiga tun da ta shiga ya kafeta da ido bai masan mi take cewa ba, ganin kallon bai k'arewa yasa Inaaya magana.
"Ya Naufal meet my runaway friend her name is Husna."
"Wow what a nice name."Ita dai murmushi Husna tayi tare da sunne kai k'asa.
"Husna wannan cousin d'inane his name is King Naufal."
"Ya Naufal Ina wuni?"
"Lafiya lau Husna."
"Ya school?"
"School Alhamdullah.""Madam Ina zamu je yanzu?"
Inaaya yake kallo yana magana.
"Alqalam zamu ajiyeta."
"Dama alqalam kike?"
"Ah ah yanzu zan fara."
"Shiyasa ban sanki ba, dan can nake."Da mamaki Inaaya ta dubeshi ita a sanin ta tasan ya gama school d'in shi kuma a ABU zariya yayi, kashe mata ido yayi alaman kada tayi magana, murmshi tayi ba tare da tace komai ba.
Tafiya suke suna fira, rabin firan King Naufal ne da Inaaya suke yi dan Husna ba ta cika saka masu baki ba, gate d'in makarantan suka shiga daidai admin blog suka tsaya, kallo Husna yayi yace
"Dana ajiye ta zan dawo dan ina da lectures why not ki ban number ki idan kin gama sai mu wuce gida."
"Ah Yaa Naufal da ka barshi karna baka wahala."
"Ba wani wahala sai dai idan ba zaki bashi ba dama kin saba."Dafe kanta tayi
"You guys am sorry ba abinda kuke nufi nake nufi ba, kawo wayan ka na baka number."Da murna ya mik'a mata wayan, number ta saka mashi ta mik'a mashi wayan, godia ta masu ta fita. Motar yaja ya bar cikin makarantan.
"Yanzu Yaa Naufal miye amfanin k'aryan da kayi?"
"Tana da amfani mana, saboda ta hakane kad'ai zai sa na shak'u da ita, kuma lokaci guda ba zan nuna mata soyayya ba, da abota zamu fara."
"Yanzu idan ka ajiyeni dawowa zakayi?"
"Eh mana."Bata sake magana ba, shima kuma bai sake magana ba har suka isa Umyu.
Wayarta ta fiddo ta kira wanda Moh ya had'ata dashi, ba tafi minti biyar da kiranshi ba ya fito, da taimakonshi ta gama komai, k'arfe shida da minti biyar ta gama komai. Wayanta ya fara ringing, new number ta gani, dauka tayi tare da sallama.
"Princess kin gama?"Shiru tayi dan bata gane mai magana ba.
"King Naufal ne."
"Yaa Naufal yi hak'uri wallahi ban gane ba."
"Karki damu Princess, kin gama ko?"
"Eh na gama."
"Okay ki sameni in da na ajiyeki ina nan."
"To shikenan Yaa Naufal."Da saurinta ta isa in da yake saboda bata san ya jirata. Tana isa ta mashi sallama cikin sakin fuska, shima amsawa yayi fuskanshi sake.
"Sannu da makaranta ya gajiya?"
"Lafiya lau Ya Naufal."
"Shiga mota mu tafi dan nasan kin gaji."Gaba ta shiga dan ta gaji gida kawai take san ganinta. Tafe suke suna fira kamar sun dad'e da sanin juna, nesa da gidansu tace ya tsaya.
"Yanzu sai yaushe? Ko da yake zan kiraki anjima."
"Okay shikenan Ya Naufal nagode sosai."
"Shhh karki damu ai ke sister d'ina ce."Ban kwana ta mashi ta fita daga motan, sai da ya ga ta shiga gida kana ya tada motar ya bar cikin unguwa cike da murna.
Tana shiga gida babu kowa parlor, d'akin mummy ta wuce, zaune ta tarar da ita tana karatun jarida.
"Mummy Ina wuni?"
"Lafiya lau Husna ya School?"
"Lafiya lau."
"Allah ya taimaka."
"Ameen mummy."
Shiru ta d'anyi can kuma tace
"Mummy babu abinda za'a maki?"
"Karki damu Husna ke da kika dawo yanzu jeki huta dai zuwa anjima kinyi man gyaran wardrobe."Tashi tayi cike da mamakin sauyawan da Mummy tayi daga jiya zuwa yau, tana shiga d'aki ta zube kan gado.tana nan kwance har aka kira sallah magrib sallah tayi , Tana idar da sallah ta tuna da zata ma Mummy gyaran wardrobe, da sauri ta tashi ta nufi d'akin mummy da sallama ta shiga d'akin bata ciki, wardrobe ta nufa ta fito da kayan, a tsanake take gyarasu ta mai da komai in da yake, mummy ce ta shigo.
"Husna kina nan kina gyaran?"
"Eh mummy nama gama."
"Sannu da aiki."
"Yauwa mummy, yanzu mi za'a maki?"
"Bakomai Husna kije ki huta."Tashi tayi ta nufi d'akinta tana ta mamakin Mummy, tunanin Moh ta fara tana mamakin da har yanzu bai kirata ba.
Wayarta ce tayi ringing ganin sabuwar number yasa ta d'auka tana fad'in
"Hello Yaa Moh."Jin wata murya bata Moh ba yasa tayi shiru.
"You mean ba kiyi saving number na ba?"Da sauri tace
"Yaa Naufal am sorry dan Allah."
"Bakomai Princess, ya kike and gajiya?"
"Lafiya lau."Nan fa suka fara fira sai kace sun shekara da sanin juna, a gaskia taji dad'in had'uwa da Naufal, dan da alamu zai d'ebe mata kewar Moh, haka dai suka dinga fira har goma na dare, ganin lokaci yaja su kayi bankwana.
"Gobe zanzo muje School."
Yana fad'in haka ya kashe waya dan karta mashi gardama. Dariya tayi tana k'ara jin Naufal a ranta.Kwance yake d'aki yana juyi babu abinda ke ranshi sai wulak'anta Husna, agogon wayanshi ya duba k'arfe biyu da rabi na dare, murmushi yayi dan yanzu ne dai dai lokacin da zai nuna mata matsayinta, ta shi yayi ya nufi hanyar d'akinta, a hankali ya tura k'ofan da mamaki ya sameta bud'e d'akin ya shiga wutar d'akin ya kunna haske ne ya gauraye d'akin, takawa yayi yaje gaban gadon ta, fuskar shi d'auke da murmushin mugunta..
RIJF MOTHER 🙏🏼
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Mystery / ThrillerLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...