BABI NA TALATIN

1.2K 111 8
                                    

MARAICIN 'YA MACE

Rubutawa
Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN

   Tana shiga d'aki ta saka sabon kuka mai ratsa jiki, b'angare d'aya kuma tsanar Muhmud ne ta k'ara jin tayi, saboda shine yaja mata wannan bugun, rabon da mummy ta saka hannu a jikinta tun bayan ta fiyar Moh, amma gashi sanadiyar soyayyar da yace yana mata yau an mata bugun da ba'a tab'a yima ta shi ba. Kuka ta cigaba da yi sai da tai mai isar ya ganin kanta ya fara sarawa yasa ta tashi ta shiga toilet dan ta watsa ruwa.

Hajiya kaka ce ta shigo gidan bako sallama, sakamakon kiran da mummy ta mata tana kuka, tare da zayyane mata komai, Husna take kwalama kira. Jin muryan hajiya kaka yasa gabanta ya fad'i dan tasan yau sai ta d'and'ana kud'arta b'angare d'aya kuma tsanar Muhmud ta k'ara mamaye mata zuciya, dan gani take duk shine ya jefata wannan halin. Fitowa tayi jiki ba kwari, parlor ta tarar da Hajiya Kaka da Mummy, duk'awa tayi tare da fad'in.
"Hajiya Kaka Ina wuni."

Saukar marin da taji yasa ta had'iye sauran maganarta.
"Dan ubanki yau sai kin bar gidan nan shiyasa nace maku na tsani zaman yarinyar nan gidan nan amma kika dage sai ta zauna, ni nasan mahaifinta maye ne, dan in ba maitama ba da ta lashe ma Muhmud kurwa ta ya zai so ta, yarinyar da ya tsana fiye da komai. Dan haka yau sai kin bar gidan nan tun da ba gidan ubanki bane ba."

Kanta k'asa yake tana kuka mai cike da tausayi.
"Ki tashi ki tattaro kayanki ki bar gidan nan tun da ba gidan ubanki bane ba."
"Babu in da zata."

Muryan Muhmud suka jiyo, gaba d'aya suka kai dubansu gare shi, takowa ya yi ya k'araso in da suke zaune tsaye yayi bisa kansu tare da kallon su.
"Babu in da Husna zata je Hajiya kaka Husna bata da gidan da ya wuce nan dan haka wallahi ba zata je ko Ina ba."
"Dan ubanka uwata kake gayama haka? To Husna sai ta bar gidan nan kuma idan kaga ka auri Husna to sai dai idan bani da rai."

"To shikenan naji Husna zata bar gidan nan, amma ki sani daga ran da Husna ta bar gidan nan kin kore ta daga nan zaki rasa ni wallahi daga ranan zan bar gidan nan kuma ba zaki k'ara gani na ba sai a lahira, zan kira Moh kuma na fad'a mashi duk abinda kuke yi kinsan shima zaki rasa shi dan ba zai dawo ba, dan dama sanadiyar muzguna mata da muke yasa ya bar gidan kin ga kuwa shima zaki rasa shi dan ba zai dawo ba, kin ga sai ki zauna da Hajiya kaka amma ke kin rasa yaranki."

Yana gama fad'in haka ya kama hannun Husna dake zaune tana kuka, mik'ar da ita ya yi tsaye ba tare da ya tanka mata ba. Janta ya dinga yi har suka bar wurin, suna barin wurin ta fizge hannunta tare da ja mashi tsaki ta bar shi nan tsaye. Girgiza kai yayi ya bar gidan cike da k'unar rai.

"Hajiya gaskia mu hak'ura da koran Husna dan dagaske suke in dai Husna zata bar gidan to wallahi duk zan rasa su, ni kuma kin san ban had'a yaran nan da komai ba."

"Ni kaina na janye maganar korar ta dan naga idan aka ce za'a kore ta to suma zamu rasa su sai dai abinda nake so ki sani muddin kika bari akayi auren Muhmud da wannan figaggiyar yarinyar to wallahi zakiyi danasani."

"In kin ga anyi auren nan Hajiya to wallahi ban da rai amma muddin ina da rai to ba za'ayi wannan auren ba."

Sallama tayi ta shiga ba tare da ta jira ya amsa ba, kanta ta tura cikin d'akin, fitilan d'akin ta kunna haske ya mamaye d'akin, tsakiyar gado ta han goshi ya d'aga kanshi sama kamar mai bacci. Ka'rasawa tayi bisa gadon tare da dafa kafad'anshi. A firgice ya kai dubanshi gare ta tare da ajiyar zuciya, wuri ta samu kusa dashi ta zauna, tare da k'are mashi kallo. Tausayin shi ya kamata lokaci guda.
"Yanzu Muhmud rayuwar da ka d'aukar ma kanka kenan?"

Kanshi k'asa bai ce mata komai ba, kuma bai da niyar tanka mata, ganin bai da niyar tanka mata yasa ta cigaba da magana.
"Yanzu Miye amfanin soyayyar da kake ma Husna? Miye amfanin san yarinyar da baka gabanta?"

"Mummy na cancanci Husna taman fiye da abinda take man yanzu baki tunanin Allah ne ya saka mata ta hanyar d'ora man soyayyar ta? Wallahi rasa Husna a rayuwata dai dai yake da rasa raina."

"To dan ubanka ba zaka auri Husna ba, idan Ina da rai auren ka da Husna ba zai tab'a yuwuwa ba, dan ba zan had'a jinsi da dangin Matalauta ba."

Mik'ewa ya yi tsaye tare da kai dubanshi gare ta.
"Wallahi Mummy ban da mata idan ba Husna ba, idan har kin ga ban auri Husna ba to bani numfashi, duk ran da kika yi yunk'urin raba ni da Husna to ki sani a ranan zaki ra bani da
duniya, dan nasan mutuwa ce zanyi."

Yana gama fad'in haka ya bar cikin d'akin ranshi b'ace. Kanta ta dafe.
"Wannan wace irin k'addara ce , taya zan bar Muhmud ya auri Husna, dagaske idan na hana shi auren Husna zai rasa rayuwar shi?"
Ita kad'ai take surutanta, ganin bata da amsa yasa ta tashi jiki ba kwari ta bar d'akin. Tana shiga kitchen dai dai Husna na fitowa, fizgota tayi tare da kai mata wani wawan mari wanda sai da ta fara ganin stars, bugunta ta din gayi tun tana kuka har ta kai ga bata iya kuka.
"Dan ubanki idan har ba zaki fita harkan Muhmud ba yanzu ki ka fara ganin azaba, wallahi sai na halakaki, in ga ta yan da zai yi ya aure ki, shegiya dangin mayu."

Hankad'a ta tayi gefe guda ta wuce cikin b'acin rai, da kyar ta mik'e tayi hanyar d'akinta tare da sakin sabon kuka mai cike da tausayi.

RIJF MOTHER 🙏🏼

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now