MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA TALATIN DA D'AYA
Yana fita ba in da ya tsaya sai k'asan layinsu, wuri ya samu ya zauna bisa dakali, baka jin k'aran komai sai kukan tsuntsaye, dan wurin mutane ba su cika bi ba. Tagumi ya yi tare da jan tsoki kad'an, ba fad'an Mummy ke ta da mashi hankali ba, irin tsanar shi da ya hango a kwayar idon Husna, idan ya tuna da yanda Husna ta tsane shi hankalinshi tashi yake.
"Zan jure komai dan na mallakeki, zan ajiye komai dan naga kin zama tawa, Husna ina sanki."
Da k'arfi ya fad'a tare da dunk'ule hannunshi ya kai ma dakali da yake zaune naushi, fashewa hannunshi ya yi, bai damu da fashewar da hannunshi ya yi ba, abinda kawai yake saka ma ranshi yan da za'ayi ya mallaki Husna, ganin jinin da ke fita hannunshi yasa ya ta shi ya nufi gida, yana shiga ya wuce d'akin shi tare da d'auko first aid box, da kanshi ya gyara hannunshi ya d'aure da bandage.
Fitowa ya yi dan ya tafi masallaci, dai dai d'akinshi suka had'u, rab'a shi tayi zata wuce fizgota yayi sai da ta fad'a jikinshi, ajiyar zuciya ya saki, tare da k'ak'ameta yana magana.
"Wai Husna yaushe zaki gane abinda kike bai dace ba? Baki san kin kusa yin kinsan kai ba? Ko baki da imani ne?"Cizon da ta mashi a k'irji ne yasa ya sake ta ba shiri, kallon shi tayi sama da k'asa tare da jan tsaki.
"Muhmud wallahi ko gawar ka na gani ba zan iya mata kallon so ba, ka sani na tsaneka tsanar da ban tab'a ma wani halitta ba, kuma idan har kai d'ane kabi maganar mahaifiyarka ka rabu dani."Tana fad'in haka ta wurga mashi harara tare da wucewa.
Girgiza kanshi ya yi ya wuce masallaci ranshi b'ace, bakomai ke sa ranshi na b'aci ba sai k'iyayyarshi da yake hangowa k'arara a kwayar idon Husna.
BAYAN SHEKARA BIYU
Abubuwa sun faru masu dad'i da marar dad'i a cikin wannan shekarun, duk yanda Muhmud zai yi ya shawo kan Husna ya yi amma abun ya gagareshi, ga Mummy kullum cikin azabtar da Husna ta keyi, dan gani take yi ta mallake mata yara, basu ganin kowa da k'ima idan ba ita ba, a cikin shekara biyun nan idan kaga Muhmud sai ka tausaya mashi yanda ya yi bak'i ya rame kamar bashi ba, babu gayun nan idan yana shi kad'ai babu abinda yake sai tunani, duk soyayyar da yake nuna ma Husna bai sa ta saduda ba, dan kullum tsanar shi take yi.B'angaren Naufal kuwa ya takura mata akan lallai sai ta bar shi ya zo gidansu an san dashi, dan yanzu tana 300L tayi tayi ta fahimtar dashi ya bari Moh ya dawo ya kasa fahimtar ta dan har fushi ya yi da ita, fushi ya yi sosai dan har daina kiranta ya yi sai da ya gaji dan kanshi ya nemeta, kullum dai cikin rigima suke akan tak'i barin shi yaje gidansu.
Zaune take gaban shi tana kuka kamar ran ta zai fita idan akwai abin da ya tsana yaga mace na kuka, kuma ma ace kanshi take kukan.
"Yanzu Amaal ba zaki hak'uri ba? Dole na tafi tunda na gama abinda ya kawo ni dole na koma wurin dangina suma suna da buk'atar ganina."Kukanta ta cigaba ba tare da ta tanka shi ba, d'an k'aramin tsaki ya ja ya tashi ya k'arasa gabanta tare da ruko hannunta biyu.
"Nace kukan ya isa haka nan mana."Tare da share mata hawaye da take yi.
"Moh."
D'agowa ya yi ya kalleta.
"Ina san kaman alfarma d'aya.
"Fad'i komiye ni kuma zan maki shi."
"Inasan kace kana sona, koda ba haka bane har cikin ranka, please kada kace ba zaka iya ba."Shiru ya yi tare da kallonta, bak'aramin tausayi take bashi ba dan yasan irin san da take mashi.
"Amaal ina sanki."
Dariya tayi har sai da fararen hak'oranta suka fito, sai kuma ta fashe da kuka tare da fad'awa jikinshi, kuka take sosai, bai hanata ba kuma baiyi yunk'urin d'agata daga jikinshi ba. Sai da tayi mai isarta kana tayi shiru."Nagode Moh ko a haka Allah ya barni nasan na cika burina, ka furta man kana sona."
Tana fad'in haka tana share hawayen ta, tausayinta ya k'ara kama shi, murmushi ya mata tare da mik'ewa tsaye dan driver d'in da zai kai shi airport ya k'araso, jakar shi ta d'auka suka fito har in da driver ya yi parking, karb'an trolley d'in shi ya yi tare da saka wa mota, juyowa ya yi ya fuskanceta yana murmushi.
"Sai watarana kenan ko?"Jikin shi ta fad'a tana kuka, lallashinta ya dinga yi kamar yarinya amma tak'iyin shiru, d'agota ya yi yana murmushi tare da share mata hawaye.
"Kefa yanzu ba yarinya bace ba, a haka zamuyi auren har ki haifaman yara?"Dariya ta fashe da ita sai da kumatunta suka lotsa, kallonta ya tsaya yi, ya fad'i hakanne dan ya kwantar mata da hankali.
Janye ta ya yi daga jikinshi,
"Idan na isa Nigeria zan kiraki ki kula da kanki kinji ko?D'aga kanta tayi alaman
"To."Murfin motar ta bude mashi, shiga ya yi yana kallonta.
"Allah ya tsare hanya ya kai ka lafiya, kasa a ranka ina sanka fiye da yanda nake san kaina."Kukan da yaci k'arfinta ne yasa ta kasa ida maganar ta.
"I love you too Amaal."Kamar daga sama taji maganar shi d'agowa tayi ta kalle shi kashe mata ido ya yi tare da mata murmushi ita ma murmushin ta mashi, tare da rufe mashi k'ofa. Jan motar driver ya yi tare da barin wurin, hannu ta dinga d'aga mashi har sai da ta daina ganin motar, hawayenta ta share tare da barin wurin.
Yana isa airport saura 30mints jirginsu ya d'aga nan ya yi komai yana gamawa ya shiga jirgi, yana shiga ya zaro wayar shi yana duba hotunan Husna.
"Yau zanzo gare ki yau zan ga yanda baby sis d'ina ta koma."
Yana fad'in haka yana dariya tare da kashe wayarshi dan an fara announcement jirgi zai tashi, wani b'angaren kuma yana ji kamar bai yi daidai ba dan babu wanda yasan zai dawo yau. A haka dai har jirgi ya d'aga yana tunani.RIJF MOTHER 🙏🏼
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Mystery / ThrillerLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...