BABI NA SHA D'AYA

1.9K 190 4
                                    

MARAICIN 'YA MACE

Rubutawa
Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

Thank you to each and everyone who prayed for my mother, please continue to pray for her no matter how little it is. Thank you so much for the love, indeed I'm the luckiest and i see it now, you all mean a lot to me and I don't know what I would have done without your love and support thank
you and love y'all Fisabilillah ♥️

BABI NA SHA D'AYA

     Tun k'arfe shida yake faman shiri, wasu kod'add'un kaya ya saka wanda sun gaji suna buk'atar a bada su, haka ya d'auke su ya saka, Hameed na gefen shi yana ta faman kallonshi, tausayi ya bashi irin halin da ya tsinci kanshi. A zahiri kuma cewa ya yi
"Kaga angon Nafeesah."

Wuri ya samu ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya, kafad'ar Hameed ya dafa kallon shi yake yi.
"Hameed gabana fad'uwa yake yi, gani nake yarinyar nan kamar ba zata amince dani ba."

Murmushi ya sakar mashi wanda bai kai ciki ba yace
"Nafeesah rabonka ce ina ji a jikina kai ne zaka zama mijin Nafeesah."

Har ga Allah ya ji dad'in yanda Hameed ya ke k'arfafa mashi guiwa, da taimakon Hameed Habeeb ya cigaba da shirin shi.

Sanyayar iskan magrib ne ke kad'ashi, da yake lokacin damina ne, garin ba k'aramin dad'i ya yi ba, tsaye yake bakin k'ofar gidan su yana tunanin taya zai ga Nafeesah, kasancewar unguwar shiru take ba mutane, yasa ya kasa samun wanda zai aika, had'a kan shi ya yi da mashin d'in shi ya rasa ta ina zai fara, tunanin ya kwankwasa gidan ya yi amma kuma Idan aka lek'o ya ce wajen wa yazo?, sai da ya kwashe awa biyu k'ofar gidansu Nafeesah yana tunanin ta ya zai samu ganinta, ganin ba yanda zai yi ga hadari ya had'u ya yi bak'in k'irin yasa ya tada mashin d'in shi jiki sanye ya nufi unguwarsu.

Yana isa gida, bai tsaya rufe mashin d'in shi ba ya sake shi ya nufi shagon su, ganin haka yasa Hameed ta shi da sauri ya gyara mashin d'in ya rufa mashi baya ya bishi cikin shagon.

Yana shiga ya tarar da ya yi rub da ciki ya k'ura ma silin ido, kusa dashi Hameed ya zauna tare da dafashi
"Dan uwana Lafiya kuwa, na ganka cikin wani hali?"

Tashi ya yi zaune yana fuskantar Hameed, fuskar nan ba yabo ba fallasa yace
"Ban ganta ba."
"Wacece baka gani ba?"

Dan shi har ya manta Habeeb wajen wata ya tafi, kallon mamaki Habeeb ya bishi dashi, can kuma ya tab'e baki yace
"Nafeesah."
Tare da kauda kanshi gefe guda, dafe kanshi Hameed ya yi sai yanzu ya tuna da Habeeb ganin Nafeesah ya jeyi.
"Ya akai baka ganta ba? Ko bakaje bane ba?"
Tambayar da ya wurgo mashi kenan.
"Naje mana."
"Kaje kuma ka kasa ganinta, ko bata fito bane ba."
"Ah ah."

Juyo dashi Hameed ya yi yace
"Kaman bayani yanda za gane mana."

Zama ya gyara tare da fad'in
"Na kai awa biyu k'ofar gidansu na kasa samun wanda zai kira man ita, kuma ina tsoron na yi masu knocking saboda bansan mi zance ma mai gadainsu ba."

Ajiyar zuciyar Hameed ya sauke, tare da sakin murmushi.
"Yanzu Habeeb kana nufin ka ce man awa biyu kayi k'ofar gidansu, amma ka kasa yima maigadinsu magana ya kira maka ita, anya kuwa dagaske kake kana san Nafeesah?"

Dasauri ya juyo ya kalle shi ya ce
"wallahi Ina santa mana."
"Naji kana santa, amma miya hana ka yima maigadinsu magana ya kira maka ita?"
"Hameed am scared ina tsoro, ina tsoron wulak'anci amma nasan ina santa, kuma har cikin raina nake jin ta, ka taimkeni d'an uwana in sami Nafeesah itace farin cikina."

Sosai ya ba Hameed tausayi.
"Wannan wace irin jarabawa ce Allah ya jarabci Habeeb da ita."

A zahiri kuma dafa shi ya yi yace
"Habeeb wannan fighting d'in na kane ba kowa zai maka shi ba, ya kamata ka fitar da tsoro ka fuskanci abin da ke gabanka, ka da ka tsaya wasa ka zo ka rasa Nafeesah."
Baki shi ya buge yana huci
"Bazan tab'a rasa ta ba, ina ji a jikina ita ce zata zama  uwar 'ya'yana."

Tausayin shi ya kama Hameed sosai.
"To in dai hakane sai ka fitar da tsoro, kaje ka sameta ka gaya mata abinda ke zuciyarka."
"Zanje gobe kuma zan fitar da tsoro zan fad'a mata abinda ke raina."
Da wannan shawarar suka kwanta, akan gobe zai je ya sami Nafeesah.

Da gudu take saukowa daga saman bene tana kiran Mummy.
"Mummy! Mummy!! Mummy!!!"

Da gudu Mummy ta k'araso wajen ta tare da rik'eta cikin tashin hankali take tambayar ta.
"Feenah lafiya? Mike damunki? Miyafaru dake?"
Gaba d'aya ta jero mata wad'annan tambayoyin.

Murmushi tayi taja hannun Munmy suka zauna.
"Mummy duk ni kad'ai zan amsa maki wannan tambayoyin?"
A k'agare Mummy tace
"Duk ke zaki amsa man, fad'aman miya sameki?"

Murmushi tayi tana fad'in.
"Guess What?"
"What?"
Mummy ta tambayeta.
Ya Ruk'ayya ta haihu ta samu baby boy."
Tun kafin Nafeesah ta fara Mummy ta mik'e da murna tana rawa, sakin baki Nafeesah tayi tana kallon Mummy.
"Wannan wace irin rayuwace, ita da zata ma Allah godiya sai ta kama rawa."
Duk a zuciya take magana, a zahiri kuma hannun Mummy ta kama ta zaunar da ita, tana murmushi.
"Gobe zan wuce Mummy dama kin san kin man Alk'wari idan an haihu zan tafi."
"Eh amma tare zamu tafi goben"
Dasauri ta kalli Mummy tana fad'in Mummy
"Mi zakije kiyi?"
Murmushi ta saki tace
"Zanje in ga jikana mana."
Tana gama magana ta d'auki waya takira, ringing biyu aka d'auka.
"Amadu kamana booking flight ni da Nafeesah wanda zaije Abuja gobe amma ka tabbata an samu na rana, muna nan zuwa kano gobe."
Bata jira mi za'a fad'a ba ta kashe wayarta.

Tsaye yake  yana kallon gate d'in gidansu, dogo ne, gashi fari sol gashin kanshi bak'in k'in ya kwanta ya yi luf da ka ganshi kaga fulanin asali bakin shi daidai shi, murmushi ya ke d'auke dashi, wanda ya sa gefen kumatun shi lotsawa, agogon hannunshi ya kalla ganin takwas da kusan minti goma yasa shi gyara mashin d'inshi ya tun kari gate d'in gidan, cike da fad'uwar gaba. Kwankwasawa ya yi, maigadi ne ya lek'o yana k'are mashi kallo, a zahiri bai sanshi ba, bai tab'a ganin shi ba.
"Malam Lafiya?"
"Lafiya lau, nazo wajen Nafeesah ne."

Da mamaki maigadi ya bishi da kallo, k'are mashi kallo ya yi sama da k'asa yana mamakin mi wannan yazo yi wajen Nafeesah, tunawa yayi da yanda take taimakon talakawa yasa ya kauda zancenshi da fad'in
"Ayya bawan Allah gashi kuwa tayi tafiya."

Cikin tashin hankali ya tambayeshi
"Ina taje?"
"Gaskia bansan in da sukaje ba, Hajiya dai tace man zasuyi tafiya in kula da gida sai sun dawo."
"Yanzu yaushe zasu dawo?"
"Malam wallahi bansani ba a k'aidar Hajiya bata gaya maka in da zata bare kasan yaushe zata dawo."

Bai k'arasa jin maganar maigadi ba ya juya ya nufi in da mashin d'in shi yake aje, kasa tuk'a mashi d'in yayi, gungurashi ya din gayi. Sosai ya ba maigadi tausayi.
"Allah sarki bawan Allah lallai kana cikin halin talauci gashi kayi rashin sa'a yar aljanna bata nan bare yau ta share maka kukan ka."

Hello y'all my people's zan da katar da rubutun MYM Sai bayan sallah idan Allah ya kaimu, dan Allah ina baran aduar ku duk wanda ya yi azumi yau da ya sakani a dua Allah ya biyaman buk'atuna na alkairi. Ayi sallah Lafiya kuma a ci nama Lafiya. Thnx y'all

Biko drop your comments, vote nd share with your family and friends

RIJF MOTHER 🙏🏼

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now