BABI NA SHA TAKWAS

1.8K 156 22
                                    

MARAICIN 'YA MACE

               Rubutawa
                     Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHA TAKWAS

Anty Amina, Meelah Adeel and Teetee wannan shafin na kune  na baku shi kyauta kuyi duk yanda kuke so dashi, yanda kuke comments yana faranta man rai ya zama dole nima na faranta maku. You guys I love you Fisabilillah.

     Masifa Mummy ke yi sosai, su Ruk'ayya ne ke bata hak'uri akan tayi hak'uri zasu yi komai dan suga Nafeesah bata auri Habeeb ba.

Yak'e Mummy tayi wanda yafi kuka ciwo tace
"Habeeb yake kowa? Zanyi maganinshi cikin d'an k'ank'anin lokaci sai ya yi dana sanin cewa yana san d'iyata  sai na nuna mashi cewa akwai tazara sosai tsakanin talaka da mai kud'i."

Dariya su Ruk'ayya sukayi dan sun san Mummy zatayi duk abinda ta ambata akan yaranta dan taga ta karesu, har dai Nafeesah da tafi so sama da komai.
"Muna bayanki Mummy ai mashi hukunci dai-dai da abinda ya aikata."

Tun daga wannan ranan tsakanin Mummy da Nafeesah gaisuwa ne, ko gaidata Nafeesah tayi ciki-ciki take amsawa, ita kuma abin bai dameta ba dan ta shirya karb'an kowane irin hukunci akan Habeeb.

Yau monday ta fara final paper d'inta gaba d'aya hankalinta ya koma kan karatu, dan Habeeb ma sun rage waya dan burinta bai wuce ta gama school ba ta samu abinyi kodan ta tallafa ma mijinta bayan sunyi aure.

***********
Tun da ta fito d'akin jarabawa gabanta ke fad'uwa, tanajin a jikinta wani abu zai faru da ita, course mate d'inta ne ke fitowa cikin murna, dan yau suka zana jarabawan k'arshe ta barin jami'a, murna suke suna d'aukar hotuna, banda Nafeesah data koma gefe guda tana tunani, friend d'inta ce ta dafata.
"Feenah lafiya?"
"Lafiya lau Aira."
"Ah ah ba lafiya ba kowa yana murna ana pictures an gama school ke kina nan."

Baki ta washe mata tace
"Babu fa komai."
"To idan babu komai ki tashi muje ayi hotuna dake."

Dole yasa Nafeesah tashi ta shiga cikin course mate d'inta suna pictures, sai kusan k'arfe biyar suka gama abinda suke, kowa gida ya nufa, haka Nafeesah ta wuce gida zuciyarta bata mata dad'i kuma ta rasa mike damunta.

Da sallama ta shiga cikin parlour babu wanda ya amsa mata dan babu kowa cikin parlour, hanyar d'akinta ta nufa ta aza k'afarta bisa bene taji magana daga bayanta
"Congratulations Autana."

Da murmushinta ta juyo jin muryan mahaifiyarta, da gudu ta k'arasa wajenta ta rungumeta
"Thank you so much Mummy."

D'agota tayi daga jikinta tace
"Allah yasa ki amfana da abinda kika karanta."

Ta bud'e baki zata bata amsa wayarta tayi k'ara, ganin new number yasa ta d'aga wayar ta kai kunnenta.
"Hello dan Allah inasan magana da Nafeesah."
"Eh nice."

"Dama Habeeb ne wasu mutane suka zo har gida suka mashi mugun bugu sun ji mashi ciwo sosai yana FMC."

Tun bai ida magana ba ta kashe wayar tana kuka. Tsawa Mummy ta daka mata
"Kukan ubanmi kike?"

"Mummy Habeeb ne...."
Kafin ta k'arasa Mummy ta katseta
"an illatashi ko?"

Dariya Mummy tayi tace
"Ni na saka aka mashi."

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now