MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA SHA UKU
Assalamu Alaikum my beautiful people nagode sosai da aduarku, Allah yaban Lafiya In shaa Allah zaku dinga ganin post akai-akai. Thnx y'all nd love y'all Fisabilillah
Tun da suka tashi take ta faman had'a kayanta, d'akin Mummy ta shigo ba tare da tayi sallama ba, wuri ta samu ta zauna tana kallon d'iyarta yanda take had'a kaya cikin akwati.
"Ina zaki haka kike ta faman had'a kaya?"
"Zan wuce gida ne mummy"
Amsa ta bata ba tare da ta d'ago ta kalleta ba kuma bata daina saka kayanta a akwati ba."Yaushe zaki wuce ne?"
Maganar Mummy ta sake ji a karo na biyu, dan kwalin dake hannunta ta ajiye ta zauna kusa da Mummy dan tasan sai tayi da gaske zata barta ta wuce yau.
"Yau nake san wuce wa mummy."
"Yau?"
"Eh"
"Ban amince ba, taya zaki wuce yau kamar wadda ake kora ki bari sai gobe mana, yanzu na sa ai maki booking flight gobe ki wuce danni ba yanzu zan tafi ba."
Marairaicewa tayi tana fad'in
"Mummy please ki barni na wuce yau, Monday zan fara exams Gashi yau Friday, banyi karatu ba ko kina san na d'auko maki carry over ne?"Jin Nafeesa tace carry over yasa Mummy jikinta yayi sanyi dan bata san yaranta ace suna da matsala a school.
"Naji zaki wuce yau amma waye zai kaiki?"
"Na riga da nayi shatar mota wajen 9:00am zata zo mu wuce."
"Auta na miyasa kike san mai da kan ki d'aya da talaka da gatanki da komai, akanmi zaki bi motar haya duk ina direbobin gidannan da ba zasu kaiki ba sai motar haya zaki shiga, bansan kina shiga motar haya, idan kika tafi da mai k'arar kwana ku kayi accident fa?."
Ba k'aramin b'acin rai maganar mahaifiyarta ta sata ba, a kullum tana mamakin yanda mahaifiyarta ta ke nuna kyama ga talaka Ko kuma wani abu da talaka keyi to yanzu idan itace mai k'arar kwana fa ya zatayi idan Allah ya d'auki ranta. A zahiri kuma murmushi ta sakar mata wanda bai kai ciki ba tare da fad'in
"Karki damu Mamana In shaa Allah zanje Lafiya babu abinda zai sameni ke dai ki cigaba da yiman adu'a."
Murmushi ta sakar mata tace
"Allah ya tsare hanya ya kai man ke Lafiya na dawo na iskeki Lafiya Autana."
"Har gobe Mummy ba zata tab'a canjawa ba, taya zatayi man adu'a ni kad'ai while tasan ba ni kad'ai zanyi tafiya ba nida sauran al'ummar Annabi zamuyi tafiya."
A fili kuma rungumeta tayi tace"
"Allah ya barni dake Mamana."
Amsawa tayi da
"Ameen."
Haka ta cigaba da had'a kayanta, k'arfe tara dai-dai direban da tayi shata yazo d'aukarta rakota sukayi cikin so da k'aunar juna, Muhmud ne hannunta, da kyar ta mik'ashi ta shiga mota, hannu suka dinga daga mata har suka bar cikin farfajiyar gidan.Suna hawa titi tayi hamdala tare da aduar Allah ya sauke su lafiya, d'an k'aramin alqur'ani ta d'auko tana karantawa. Sai fatan Allah ya saukesu Lafiya.
Tun da ya tashi yak'i kulashi, babu yanda Hameed bai yi da Habeeb ba amma yak'i tanka shi, d'an tsakar gidansu ya tarar dashi zaune yayi ta gumi, k'arasawa ya yi inda yake tare da cire mashi tagumin da ya yi, d'agowa ya yi ya kalleshi ba tare da ya tanka mashi ba, harara ya wurga mashi daga bisani ya maida kanshi k'asa yana wasa da yan yatsun shi. Wuri Hameed ya samu kusa dashi ya zauna kafad'arshi ya dafa yana magana.
"Nasan ni mai laifine a wurinka, bansan taya zan baka hak'uri ba, nasan ban kyauta maka ba, amma kuma ni a waje na ba laifi bane ba, idan na bari ka fita cikin ruwan nan wani abu ya sameka mi zance ma iyayenmu da suka damk'a amanar junanmu hannunmu, infact ba zan tab'a yafe ma kaina ba, kayi hak'uri d'an uwana ka yafeman ba zan daina ganin laifin kaina ba idan ka cigaba da fushi dani."Rungumeshi Habeeb yayi yana fad'in
"Ni kaina nasan ina wasu abubuwa wanda basu dace ba, amma ba yina bane ba, Allah ne ya saman soyayyar ta cikin ruhina, wanda a dalilin rashin ta zan iya rasa raina."
"Ba zaka rasa taba, Nafeesah ta kace har abada, ka sa a ranka ka kusa mallakarta a matsayin mata."
K'ara rungume Hameed yayi yana jin k'ara sanshi a ranshi.
"Amma yau zakaje ka duba ko ta dawo ko?"
Murmushi ya saki yace
"In shaa Allah zanje dan inaji a raina yau zan ganta."
"Allah ya yarda.
Hammed ya bashi amsa, haka suka cigaba da fira cikin shak'uwa.K'arfe had'u dai-dai suka isa garin katsina, kwatance ta din gayi ma direba har suka iso bakin gate d'in gidansu, horn ya yi, maigadi ne ya fito dan ya duba su waye ke horn, ganin Nafeesa ya sa ya koma da sauri ya wangale gate, cin na kan motar direba yayi ya shiga cikin gidan, wurin parking ya samu yayi parking, dasauri maigadi ya k'araso yana washe baki.
"Sannu da zuwa uwar d'akina an dawo lafiya?"
Dariya tayi tace
"Lafiya lau Baba, ina fatan na sameku lafiya?"
"Ah ah ba lafiya amma yanzu tun da kin dawo za'ayi lafiyar."Dariya tayi dan tasan halin baba maigadi da raha, kayanta direba ya fitar mata dashi, zata d'auka Baba maigadi yayi sauri ya d'auka ya nufi cikin gida dasu, tsakiyar parlour ya ajiye ya fito.
"Baba akai direban nan parlour bak'i a sa a kawo mashi abinci da ruwa idan ya gama sai a gayaman."
Tana fad'in haka ta wuce cikin gida
"An gama yar aljanna yanda kikace haka za'ayi"
Kanta ta tsaye ta shiga parlour tare da sallama, gaba d'aya tsaye suke tsakiyar parlour ganinta ya saka suka zub'e k'asa suna mata sannu da zuwa.Murmushinta ta fad'ad'a tana fad'in
"Bana ce kudaina duk'awa ba idan zaku gaidani?"
"Gaba d'aya suka had' baki kin cancanci hakane."Murmushi tayi ta nufi d'akinta, tana shiga k'amshin turaren wuta ya bigi hancinta, idanunta ta lumshe tana murmushi, a hankali ta bud'esu tana ma Allah godiya. Kan gado ta fad'a tana juyi, tashi tayi ta shiga toilet, wanka tayi ta fito kasancewar tana fashin sallah yasa bata b'ata lokaci ba tana fitowa ta feshe jikinta da turare, wardrobe ta bud'e bak'ar abaya ta d'auka ta saka, tana cikin fesa turare wayarta tayi ringing, matsawa tayi kusa da inda wayar take ganin sunan Mummy yasa ta fad'ad'a murmshinta ta d'auka.
"Hello Mummynah."
D'ayan b'angaran aka amsa da.
"Autana kun isa lafiya ko?"
"Lafiya lau Mummynah."
"To Allah ya huta gajiya bari na barki zamuyi magana anjima."
"Shikenan Mummy bye i miss you."
"Miss you too."
Tana fad'in haka ta ajiye wayar, bud'e k'ofarta akayi tare da sallama, amsawa tayi tana bada izinin a shigo.
"Ranki ya dad'e maigadi ne yace agaya maki direban da ya kawoki ya gama."
"Gani nan zuwa."
Ta bata amsa.Slippers ta saka Aldo, gyalen jallabiyarta ta d'auka ta yane kanta, ta d'auki Jakarta ta nufi hanyar fita, farfajiyar gidan ta tarar dasu tsaye, k'arasawa tayi inda suke tace
"Har ka gama?"
"Eh nagama hajiya."Jakarta ta bud'e ta d'auko kudi yan 1k ta mik'a mashi.
"Ga kud'inka 20k wannan kuma 10k kasha ruwa a hanya."
Zubewa direba ya yi k'asa yana godia har da hawayenshi, murmushi tayi ta koma cikin gida, mai gadi ne ya tadashi tsaye yace
"Kad'an daga cikin aikin yar Aljanna kenan, baka ga komai ba idan kana ganin alkairinta tabbas sai hawayenka sun k'are wajen kuka."Hawayenshi ya share yace
"Tabbas taci sunanta yar Aljanna."
Bankwana direba yama maigadi ya bar gidan cike da farin ciki.Tsaye yake bakin tagarsu yana sharce kai, fuskarshi d'auke da fara'a, kafad'arshi Hameed ya daka cikin wasa yana fad'in
"Wannan fara'ar fa sai kace wanda akace an mallaka maka Nafeesah."
Fara'arshi ya k'ara fad'ad'awa yace
"Yau inaji a jikina yau zan ganta."
"In shaa Allahu yau zaku had'u, garama ku had'u Ko na huta da mafarki cikin dare kana kiran sunanta."
Bugu ya kai mashi, kaucewa yayi yana dariya.K'arfe takwas dai-dai ya fito cikin shirinshi, kallonshi Hameed ya yi yace
"Lallai yau Nafeesah nada babban bak'o."
Baice mashi komai ba yayi hanyar fita daga shagonsu, yakai bakin k'ofa ya juyo ya kalle shi
"Dan uwana ka sani a adu'a Allah yasa ta amince dani idan muka had'u, wallahi tak'i amincewa dani Sai dai ka d'auko gawata."Yana gama fad'in haka ya fice daga shagon, zama Hameed yayi bisa katifarsu, hannunshi biyu ya had'a ya d'aga sama yana rok'on Allah.
"Allah ka dubi marayanka baida kowa bai da komai kai ka sa mashi san baiwar nan taka Allah ka bashi mafita."
Ya dad'e yana ma d'an uwanshi adu'a daga k'arshe ya shafa, kwanciya yayi yana tunanin irin wahalar da suka sha a rayuwa wanda har yanzu cikin wahala suke.Don't forget to vote comments and share with your Love ones
RIJF MOTHER 🙏🏼
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Bí ẩn / Giật gânLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...