BABI NA D'AYA

4.9K 504 20
                                    

MARAICIN 'YA MACE

               Rubutawa
                     Phirdaucee Jeeboh

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ban yarda wata ko wani ya juyaman labari ta wata siga ba ba tare da izinina ba...

Wannan labarin k'irk'irarre ne, banyi sa dan cin zarafin kowa ba, idan ya ci karo da rayuwar wani/wata akasi aka samu..

F.R.I.E.N.D.S. Fight for you. Respect you. Include you. Encourage you. Need you. Deserve you. Stand by you. Thanks you so much Loubah Lubbatu_Maitafsir  da yanda kike k'afafaman guiwa akan duk abinda zanyi, duk wanda ya samu aboki irinki ya gama samun kanshi cikin damuwa. Allah ya barmu tare..

I cried endlessly when you died but I promise that I won't tears mar the smiles that you've given me when you were alive. I miss you Maama. See you soonest my best friend..

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA D'AYA

  Zaune take bisa kujera tayi tagumi, tunani take wanda ita kanta bata san tana yinshi ba. Saukar Marin da taji ne ya sa ta dawo hayyacinta.Da sauri ta d'ago dan ganin wanda ya mareta, kafin tayi magana ta k'ara jin wani marin wanda yasa sai da ta saki 'yar siririyar k'ara.
"Aikin da na saki kenan? Zaki dawo d'aki ki zauna ba tare da kin gama man abinda na saki ba."

Hawayen da suka gangaro mata ta share.
"Kiyi hak'uri Mummy dama sallah na idar, yanzu nake da shirin tashi."

Harara ta wurga mata.
"Baki da aiki sai ba da hak'uri idan kinyi laifi amma baki san kiyi ma mutum abinda ya saka ki ba, zaki tashi ki ban wuri ko sai na zubar maki da hak'ora."

  Tashi tayi jiki ba kwari ta bar d'akin ba tare da ta sake magana ba, sanin halin mummyn nasu zata iya abinda tace a kanta.

  D'akin Mummy ta nufa inda ta tarar da duk ta b'atashi kamar ba d'azu ta gama gyaranshi ba, girgiza kai tayi ta hau gyaran d'akin. Kayan dake bisa gado ta kwashe ta mai dasu cikin wardrobe, ta gyara gadon. Shara tayi tare da mopping, tana gamawa ta nufi toilet inda nan ma da duk anyi kaca-kaca dashi, haka ta wanke shi tas, kana ta fito tayi turaren wuta. Cikin d'an k'ank'anin lokaci ta gama gyaran d'akin Mummy. Parlour ta nufa inda Mummy take zaune tana kallon channel d'in CNN.

Nesa da Mummy ta duk'a kanta k'asa tace.
"Mummy nagama"

Harara Mummy ta wurga mata tana fad'in.
"Sai ki tashi ki d'aura abinci, kafin su Muhamud su dawo."
"Mi za a dafa?"
"Kiyi tuwon shinkafa miyan alaiyahu."

Ba musu ta tashi ta nufi kitchen dan d'aura girkin dare, wanda idan tayi shi ma ba lallai bane su ci, dan kowa da abinda zai ce mata zai ci kuma dole ta tashi ta dafa masu In ba haka ba ranan bugun da Mummy zata mata babu wanda zai iya karb'anta. Tabbas in da bata san su Mummy sune jininta  ba, da tace bata had'a komai dasu ba, amma sanin su waye a wurinta da irin muhimmancin uwa wajen 'ya'yanta shiyasa take adu'ar Allah ya kawo mata d'auki cikin gaggawa..

K'arfe shida ta gama girkin dare, jerasu tayi a dainning. Tana niyar barin parlourn taji ana kwala mata kira.
"Husna! Husnah!! Husnah!!"

Jiki a sanyaye ta amsa da.
"Naam"
Sanin wanda ke kiranta, dan tasan ba kowa bane sai Muhamud wanda yafi kowa tsanarta duk duniya, idan ta ganshi gabanta har faduwa yake.

"Bakiji Ina kiranki ba? Ko sai nazo na tattakaki."
Muryanshi ta tsinkayo Yana mata magana cikin fad'a.
"Kayi hak'uri Ya Muhamud wallahi na amsa bakaji bane ba."
"Dallah rufe ma mutane baki, kije kuma ki gyaraman d'akina, na baki (5minute) minti biyar."

Ba yanda ta iya dole taja jiki ta nufi hanyar d'akinshi. Dai-dai corridor sukayi karo, d'agowa tayi da sauri ta bud'e baki zatayi magana.
"Kayi hak'ur.."
Kafin ta k'arasa ya rufe mata baki.
"Karki damu Baby sis nasan baki gani ba."

Kallonta yayi sama da k'asa yace
"Yana ga duk kin yamutse halan basu barki kin huta ba?"
Girgiza kai tayi alamar.
"Ah ah"
Murmushin takaici yayi yana fad'in
"Karki man k'arya Baby Sis kinsan nasan duk wahalar da kike sha gidan nan."
Fad'ad'a murmushin ta tayi, dan duk gidan idan akwai wajen wanda take jin sauk'i to Ya Mohammed ne.
"Allah Ya Moh ba komai fa."

Girgiza kanshi yayi, ya dai jita ne amma yasan ba gaskia ta fad'a mashi ba.
"Yanzu ina zaki?"
"Zanje d'akin ya Muhamud na gyara mashi ne "
"Ba jiya naga kin gyara mashi d'akin ba? Akanmi kuma zaki k'ara gyarawa, wuce babu abinda zakiyi yanzu jeki huta dan nasan kin gaji."

Marairaicewa tayi tana fad'in
"Dan Allah ya Moh kayi hak'uri kabarni na gyara mashi kasan idan ban gyara ba sai raina ya b'aci yau."

Tsaki yayi ya rab'ata ya wuce, dan yasan gaskiya ta fad'a dan idan bata gyara d'akin ba yau dukan da zata sha wajen Mummy Allah ne kawai zai iya kwatarta.

Girgiza kai tayi ta wuce d'akin Muhamud, tana shiga taga yanda d'akin ya hargitse ji tayi kamar ta d'aura hannu bisa kai tayi ihu, saboda gaba d'aya kayan wardrobe d'inshi ya watsosu bisa gado ga d'akin yayi muguwar datti kamar ba jiya tayi gyara ba. Amma tasan da gangan ya mata haka, siraran hawayen da suka gangaro mata ta goge ta shiga d'akin, kayan kan gado ta fara ninkewa tana sakasu a wardrobe sai da ta mai dasu, kana ta gyara d'akin tana gamawa ta nufi toilet nan ma kaca-kaca yake. Wanke shi tayi tas kamar bashi bane ba yayi datti, tana gamawa tayi turaren wuta, kusan awa d'aya ta d'auka tana gyaran d'akin. Gajiye lik'is ta fito ba abinda take buk'ata a yanzu sai ta watsa ruwa ta d'an kwanta...

Fitowa wa tayi ta nufi hanyar d'akinta, a parlour ta iskesu su duka uku suna kallo, wucewa tayi ta nufi hanyar d'akinta, takai bakin k'ofa kenan taji muryanshi yana kwala mata kira cikin isgilanci.

"Ke"
Tsayawa tayi cak, dan tasan da ita yake.
"Ba dake nake magana ba?"

Juyawa tayi ta nufi inda yake, duk'awa tayi tace
"Gani"
"Jeki man sakwara dan bazan iya cin tuwon da kikayi ba."

Ji tayi kamar an luma mata mashi a k'irji, duk yanda tayi ta hana hawayen da suka taru idonta zubowa ta kasa sai da suka zuwa.

"Gaskia abinda kukeyi gidan nan bai dacewa ya za'ayi ku maida yarinya yar bautarku karku manta fa jininmu ce ita ma amma Akanmi zaku mai data baiwa?"
Moh ne ke maganar cikin fad'a, kallonshi Mummy tayi tace
"Da ubanwa kake? Niko yayanka? Anya Mohammed kai jinina ne kuwa? Dan idan jininane ba zakayi abinda kake mana ba."

Kallonta yayi yace
"Mummy Karki manta itama d'iyarki ce Akanmi zaki dinga azabtar da ita? Saboda wani dalili naki na daban anya kuwa hakan da kukeyi akwai adalci a cikin abinda kukeyi?

Harara Muhamud ya wurga mashi Yana fad'in
"Wallahi sai tayi idan kuma ka isa ka hana tayi."
"Barni dasu Muhamud duk zanyi maganinsu su duka."
Cewar Mummy tana wurga ma Husna harara.

"Dallah tashi kije kiyi abinda aka saki munafukar banza."
Mummy ce ke mata magana cikin tsawa.

Ba yanda ta iya haka ta mik'e jiki ba kwari ta nufi kitchen, tana shiga ta fashe da kuka mai tsuma rai....

Hello hayaties gani na dawo dai abinda nake bukata shine ku d'an danna tautaroron nan na gefen dama sai kuma ku shiga d'an akwatin nan na u hagu ku aje man ra'ayunku a ko wane layi. Idan ku ka man haka shi zai bani k'arfin guiwan cigaba da maku typing.. thnx y'all I love you y'all♥️

Don't forget to vote nd comment

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now