BABI NA SHA BAKWAI

1.7K 171 17
                                    

MARAICIN 'YA MACE

Rubutawa
Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHA BAKWAI

THIS PAGE IS FOR YOU ANTY MAIJIDDA MUSA (MAMA) THANK YOU SO MUCH FOR THE LOVE, COURAGE AND SUPPORT. I LOVE YOU FISABILILLAH♥️

Tana shiga d'aki ta fad'a kan gado, sabon kuka ta fashe dashi tun da take Mummy bata tab'a dungurinta ba yau gashi ta mareta akan abunda ko wajen Allah bata da laifi, haka ta dinga kuka, tun da ta shigo wayarta ke ruri tana neman agaji, kasa d'agawa tayi duk da tasan waye ke kiran nata, tana cikin kukan ne har bacci ya yi gaba da ita.

Kiran sallar la'asar ne ya ta data tunawa tayi ko azahar ba tayi ba, da sauri ta mik'e ta fad'a toilet ta d'auro Alwalla, zuwa tayi ta kabbara sallah, bayan ta idar ta dad'e tana adua daga k'arshe ta shafa, wayarta ta jawo miss call d'inshi ta gani guda 20 ba tayi mamaki ba dan tasan zaiyi fiye da haka dan duk yau ba suyi waya ba.

Kira ta danna, ringin biyu aka d'auka.
"Hello Mieheart ina kika shige?"

Ajiyar zuciya tayi tana fad'in
"Kayi hak'uri wallahi bacci ya d'aukeni."

"Hankalina ya tashi, har na fara tunanin na taho gidanku naji lafiya."

Gabanta ne ya fad'i jin yana tunanin zuwa gidansu, dole ta hanashi dan nan kusa bata san Mummy ta ganshi dan zata iya komai dan taga ta rabasu.
"Karkadamu lafiya ta lau kuma gidanmu ba sai kazo ba idan ina san ganin ka zan maka magana."
"Mieheart miyasa baki san barina nazo gidanku ne?"
"Babu komai idan lokaci ya yi za kazo."
Fira sukayi sosai ko da wasa bata gwada mashi halin da take ciki ba, sun fi awa suna fira, kowanne yana fallasa sirrin zuciyarshi.
"Hayati na tambayeka mana."
"Ina jinki matata."

"Zaka iya rabuwa dani kuwa, saboda ka tsira da rayuwarka?"

"Nafeesah ko da ta sanadiyarki zai zama a datseman rayuwata wallahi na yarda, zan iya rasa raina akan san da nake maki ina sanki kamar yan da uwa ke san yaranta, ina sanki fiye da yanda nake san kai na, a yanzu burina bai wuce ki zama uwar 'yayana ba, na kiraki da sunan MATATA GIMBIYATA."

Hawayen da suke mak'ale a kwayar idon ta suka gangaro, hannun tasa ta share hawayen.
"Sai kayi hak'uri akan irin abinda zaka gani nan gaba amma kasani ina sanka zan zauna da kai da dad'i da ba dad'i, zan zauna da kai cikin samu ko rashi, bazan tab'a barin ka ba cikin zafi ko sanyi, in shaa Allah zan zama kafad'ar da zaka kwanta kayi kukanka."

"Nasan ba zan tab'a samun ki ba cikin sauk'i, na shirya karb'an kowane irin hukunci in dai zan mallakeki, kuma zaki sameni mai juriya akanki ba zan tab'a gazawa ba akan duk hukuncin da za'a yanke man a kanki ba."

Kukan da yaci k'arfinta ne yasa ta kashe wayar, kuka tayi sosai, tabbas tasan Habeeb na santa amma bata d'auka san da yake mata har ya kai haka ba.

**************
Mafarkin da tayi ne ya tada ta, tsorace ta mik'e side lamp ta kunna, ajiyar zuciya tayi abinda ya faru cikin mafarkin ya dawo mata, kuka ta fashe dashi ganin kukan ba zai mata magani ba yasa ta jawo wayarta, k'arfe uku da rabi na dare, ta shi tayi ta nufi toilet, alwalla tayi ta dawo ta shimfid'a abin sallah, ta dad'e tana kaima Allah kukanta, ta dad'e tana rokon Allah Kada mafarkin da tayi ya zama gaskia, bata bar abin sallah ba sai da akayi asuba, ko da akayi asuba bata tashi daga abin sallah ba sai bakwai, dan dama idan tayi sallah asuba sai tayi azkahar kana take tashi.

Juyawar da cikin ta ya yi ne ya tuna mata rabon ta da abinci tun kalacin jiya, toilet ta nufa tayi brush, tana fitowa ta bud'e d'an k'aramin fridge d'in dake d'akinta fresh milk ta d'auko ta zuba a cup, bismillah tayi ta kaita baki, tun da ta kai cup d'in baki bata ajiye shi ba sai da ta shanye, tana gamawa ta koma bisa gado, bata jima bacci ya d'auke ta.

B'angaren Mummy kuwa hankalinta duk a tashe yake, hankalinta ba k'aramin tashi ya yi ba ganin an kwana an tashi amma Nafeesah bata sauko ba, bata da niyar fitowa ma, tayi niyar zuwa ta dubata amma tuna abinda ya faru jiya yasa ta fasa, nan take tsanar talaka ya k'ara shiga jikinta, dan a ganinta sanadiyar talaka ne ya jefa d'iyar da tafiso sama da kowa cikin halin k'unci.
"Duk hanyar da zanbi sai nabi na rabaki da yaron nan sai na sa an koya mashi hankali sai na nuna mashi tsakanin mai kud'i da talaka akwai tazara sosai."
Haka ta dinga sabbatunta cikin d'aki ita kad'ai.

Bata farka ba sai k'arfe sha d'aya, mik'ewa tayi ta shiga wanka, tana fitowa bata b'ata lokaci ba wajen shafa mai dan duk zuciyarta ba dad'i turare ta fesa ta d'auki doguwar riga ta saka, bisa gado ta koma ta kwanta.

K'ofar d'akin ta aka turo aka shigo tare da sallama, amsawa tayi fuskar nan ba walwala.
"Madam dama Mummy ke kiranki."
"Tana ina?"
"Tana babban parlour."
"Kice gani nan zuwa."

Tashi tayi ta saka takalminta ta nufi babban parlour, tana shiga taga su Ruk'ayya da Zainab zaune, ba tayi mamaki ba dan tasan Mummy ce ta kirasu ta gaya masu, kuma dama tasan hakan zai faru. Baki ta washe tace
"Ah sisters sannunku da zuwa."

Kauda kanta Ruk'ayya tayi, Zainab ce ta karb'a mata ba yabo ba fallasa, wuri ta samu ta zauna, juyawa tayi in da Mummy take zaune ta hard'e k'afa.
"Mummy ina kwana?"
"Lafiya."
Ta amsa a tak'aice, batayi mamaki ba dan tasan komai zasu yi akan tace talaka take so.

Ruk'ayya ce ta fara magana.
"Yanzu Nafeesah abinda kikayi kin kyauta kenan? Ki rasa wanda zaki aura sai talaka malamin primary school? Karki manta fa kina da gata kina da kud'in da zaki saye shi dashi da duk abinda ya mallaka, duk mutanen da ke sanki amma ki rasa wanda zaki so sai talaka marar galihu, mi kika gani jikin talaka zaki ce shi zaki aura, miye abin so a talaka dami zai ciyar dake?, Taya zai iyac iyar dake da abincin da kika sabaci, wallahi babu komai wajen talaka sai bak'in tuwo da miyar kuka ba ko nama."

Kallonta Zainab tayi tace
"Haba Baby Sis miya ja maki soyayya da talaka wallahi duk talakawan nan mayaudara ne so yake ki aure shi ya kwace maki dukiya ya gudu ya barki, dan Allah Nafeesah kiyi hak'uri ki janye maganar auren talakan nan."

Kallon su tayi sama da k'asa, ta juya wajen Mummy
"Mummy ki gafarta man akan abinda ya faru amma wallahi Mummy ki sani bazan tab'a auren wani ba idan ba shi ba shine zab'ina ina ga yaranki babu wanda kika ma auren dole kowa zab'in shi ya kawo dan haka nima nawa zab'in kenan talaka. Ku kuma na dawo kanka karku manta da mai kud'i da talaka duk Allah ne yayi su kuma karku manta a kullum abinda mahaifinmu ke gayamana kada mu kyamaci talaka, yau na tabbata nayi maraici dan da mahaifina yana da rai babu abinda zai hana baiji dad'i na zab'in da nayi ba, kuma ku sani babu wanda nakeso sama da Habeeb babu wanda zan aura sai Habeeb."

Tana gama fad'in haka ta tashi tabar wajen, zagi Mummy ta lailayo ta watsa mata.
"Lallai yarinya dani kike wallahi sai nayi maganinshi sai na sa an mashi abinda ko mai irin sunanki yaji an fad'a sai ya gudu saboda tsoro."

Do comment on every line, vote and share with your family and friends.

RIJF MOTHER 🙏🏼

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now