MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA HUD'U
Da sauri ya mik'e ya bar wurin, kwallan dake zubowa daga idanuwanshi ya share, waya ya zaro daga jikin aljihunshi, kira ya danna ringing biyu aka d'auka.
"Hello Doctor dan Allah kazo gida Husna ba lafiya."
"Okay ganin zuwa Mohammed."Kashe wayan yayi ya koma d'aki in da Husna take kwance, ko da ya shiga, amai ta keyi daga nan kwance, da sauri ya isa in da take.
"Baby Sis amai kuma kike yi?"Da kyar ta d'ago ta kalleshi, murya galabaice take mashi magana.
"Ya Moh ka taimakeni cikina kamar zai fashe, zafi yake man sosai."
"Kiyi hak'uri Baby Sis, na kira Doctor yanzu zai zo."Bai k'arasa maganar da zaiyi ba, wayarshi ta fara ringing, ganin mai kiran yasa bai d'aga ba ya fita da sauri daga d'akin.
Tsaye ya ganshi tsakiyar parlour, suna ganin juna suka yi murmushi, tare da musabaha.
"Moh Baby Sis ba lafiya shine duk ka rud'e haka."Murmushi yayi yana fad'in
"To kasan yanda take a guri na."
"Hakane gaskiya nasani."
"Yanzu dai muje idan ka fara surutu baka san ka tsaya ba."Bugu Doctor ya kai mashi yama fad'in
"Komai ai zaka iya fad'aman kan wannan figaggar sister taka."D'aure fuska Moh yayi.
"Dama zuwa kayi dan ka ciman fuska?"Dariya yayi sosai har yana rik'e ciki.
"Kaga yanzu na rama."Murmushi Moh ya saki, ya ja hanmunshi suka nufi d'akin Husna.
Suna shiga d'akin abinda suka gani ya tasa masu hankali, amai ta keyi amma aman jini, da gudu Mohamed ya k'arasa wajen ta, kafin ya isa ta suma.
Jijjigata ya din gayi yana kiran sunanta.
"Husna! Husna!! Husna!!!"Kallon Doctor yayi hawaye cike da idonshi.
"Ta mutu ko?"K'arasowa Doctor yayi gabanshi ya janye shi.
"Karka damu bata mutu ba, ba kuma zata mutu ba yanzu sai burinka ya cika akanta."
"Dan Allah Doctor kayi wani abu Allah idan ta rasu ba zan gafarta ma kaina ba."
"Ka kwantar da hankalinka ba zata rasu ba In shaa Allah, zanyi iya bakin k'ok'arina in ga ta samu lafiya."Yana gama fad'in haka ya k'arasa gabanta, taimakon gaggawa ya fara bata, da kyar ya samu ta farfad'o, gwaje gwaje ya mata, ya d'aura mata k'arin ruwa, rubuta yayi cikin wata farar takarda, kallon Moh yayi
fuska ba annuri.
"Gaskia Moh banji dad'in halin da na samu Husna ba, a yanda kake ikirarin zaka iya komai a kanta amma gashi tun ba'aje ko ina ba ka gaza, gaskiya idan wani ya ce man zakayi haka bazan yarda ba."
"Doctor miyafaru ne? Dan Allah kaman bayani."
"Husna ta kamu da mummunar ulcer wadda ta na neman tab'a mata yan hanji, kuma idan har aka cigaba da haka to zata iya rasa ranta, saboda yan hanjinta zasu iya rub'ewa."
"Innalillahi wa'inna ilahir raj'un."
Abinda yake fad'a kenan yana dafe kanshi."Tabbas likita na zalunci Husna ban tab'a sanin bata cin abinci ba, ban tab'a tambayarta ba saboda nasan ita ke dafawa na d'auka zataci amma koma miye In shaa Allah zan gyara."
Dafashi Doctor yayi
"Kada ka damu Moh nasan kana iya k'ok'arinka akan Husna kawai nayi mamaki ne yanda Ulcer tayi mata kamu irin haka, amma In shaa Allah zata warware."Hawayen da suka gangaro mashi ya share ya d'aya hannu sama.
"Allah ga baiwar ka nan Husna bata da kowa sai kai Allah ka bata lafiya ka kawo mata d'auki cikin gaggawa, Allah ka da ka kamani akan abinda ban sani ba Allah ka yafeman akan alk'awarin da na d'auka akan zan kula da ita amma tun ba'aje ko ina ba na kasa cika maka alk'awarinka."
"Ka daina fad'in haka Moh, in shaa Allah zata ji sauk'i, yanzu ga wad'annan magangunan kaje ka siyo mata su, ka kawo akwai allura zan mata yanzu."Ba musu ya k'arbi takardan ya nufi hanyar fita. Haraban gidan suka had'u da Muhamud, rab'ashi Moh yayi zai wuce, hannunshi ya jawo.
"Lil Bruh har yanzu fushi kake da big bro ko?"Kallonshi yayi sama da k'asa yace
"Kada ka k'ara kira na da Brother d'inka, saboda idan da kai jinane, da ba ka iya mugunta ba, a yau nayi danasanin fitowa tsatso d'aya dakai, a dalilin munanan halayenku, kun jefa yar uwarku mawuyacin hali wallahi idan Husna ta rasa rayuwarta sai na kwatar mata hakk'inta."Yana gama fad'in haka ya bar wurin ya nufi in da motarshi take ya mata key ya bar haraban gidan da gudu. Bai fahimci maganar Moh ba, tab'e baki yayi ya nufi hanyar shiga cikin gida.
Shigowa yayi da sallama, zaune suke parlour suna fira bai tanka masu ba ya rab'asu ya wuce ya shiga d'akin Husna, rik'e da ledar magani.
"Lallai Husna daban ce a wurinka har ka dawo?"Yak'e yayi.
"Ni dai malam kayi abinda ke gabanka ban san gulma."Karb'ar ledan maganin yayi ya zaro Allura ya mata, yana gamawa yace
"Wannan maganungunan idan ta tashi sai ka bata, kuma idan k'arin ruwan ya k'are sai ka sa mata wani amma dan Allah ka aje hankalinka waje guda ba'a san likita da tsoro, kuma wannan aikin da nayi kai ya kamata kayi shi bani ba."
"Naji amma kasan ba laifina bane ba a yanda na sameta ban san mi zanyi ba."
"Nasani amma ka dinga daurewa, amma in dai Husna ce akace bata da lafiya baka iya komai anya ba ragon Yaya gareta ba?"Dukan wasa ya kai mashi, gocewa yayi yana dariya. Tare suka fito parlour. Gaida Mummy Doctor ya yi, amsawa ta yi cikin sakin fuska. Juyawa yayi su kayi musabaha da Muhamud.
"Moh ka koma daga nan, amma katabbata tasha maganin idan ta farka, kuma akwai allura da za'ayi mata gobe amma kai zaka mata."
Zaro ido yayi yana tambayar shi.
"Saboda mi?"
"Saboda gobe bana nan kaga dole ka aje tsoro ka mata in kuma kafi san ta rasa ranta to shikenan."Ba yanda ya iya, ya zama dole ya aje tsoro ya ceci lafiyar Baby Sis d'inshi.
"Kar ka damu Doctor zanyi komai in dai dan Husna ta samu lafiya."
"Ko kai fa yanzu kayi magana."Musabaha sukayi, fita likita yayi, shi kuma ya koma d'akin Husna, dan ganin lafiyarta.
"Mummy Husna bata lafiya ne?"
Muhamud ke tambayarta.
"Nima ban sani ba"
Ta bashi amsa a tak'aice.Murmushi ya saki ya tashi ya bar parlourn, yana shiga d'akin ya fad'a kan gado, ya saki wani murmushin.
"Dama mutuwa ki kayi da nafi kowa farin ciki, dan na tsani na bud'e idona na ganki cikin gidan nan."Please don't forget to vote comments nd share. Love y'all fisabilillah.
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Mystery / ThrillerLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...