MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA SHA SHIDA
Tuk'i take amma hankalinta baya jikinta, dan tasan Mummy sai ta b'ata mata rai, taya zata fad'a ma Mummy wannan maganar, dan tasan duk duniya babu wanda Mummy ta tsana irin talaka, kuma ace yau talaka wanda bai da ko sisi shine zai zama mijinta uban yaranta, tasan abun nan bamai yuwa bane ba. A haka har ta isa gida, horn tama maigadi da sauri ya tashi ya bud'e mata yana washe baki, kan motarta ta cinna cikin haraban gidan, parking space ta samu tayi parking tare da fitowa.
Maigadi ne ya k'araso gabanta da gudu yana mata sannu da dawowa, hannu ta d'aga mashi ta nufi cikin gida. Mamaki maigadi ya yi dan bata tab'a mashi haka ba.
"Mike damun yar aljanna ne yau?"
Cikin jimami ya yi maganar dan yau ne rana ta farko da ya ganta ba cikin walwala ba, Nafeesah ko bata cikin farin ciki baka tab'a gane mata dan bata barin mutane su gane b'acin ranta. Rashin sanin amsar tambayar da yake ma kanshi yasa ya koma bakin gate dan yin alwalla.Ganin ba kowa parlour yasa ta nufi d'akinta, tana shiga ta wurgan da jikarta kan gado ta nufi toilet dan an kira sallah, alwalla tayi tazo ta kabbara sallah bayan ta sallame ta d'aga hannunta sama tana adua ta dad'e tana adua daga k'arshe ta shafa.
Bisa gado ta koma ta kwanta, juyi ta take yi tana tunani, ganin bata da amsa da zata ba Mummy duk ran da ta tambayi waye zata aura yasa ta tashi ta nufi d'akin Mummy dan bata san ta dawo ba.
Tun da ya koma gida yake cikin nishad'i.
"D'an uwana tun da ka dawo naga wani sabon nishad'i da kake yi ko miye dalili?"Murmushi ya yi yace
"Hameed Aure na ya kusa."
"Auren ka ya kusa?"
Hameed ya tambay tare da zare ido.
"Eh aure na ya kusa."
"Taya auren ka ya kusa har ban sani ba."Dariya yayi sosai yace
"Kabari na mutu ka banne ni mana kabarni na maka bayani."
Baki ya tab'e yace
"Ina jinka."Zama ya yi kusa da Hameed ya kwashe yanda su kayi da Nafeesah ya gaya mashi. Ajiyar zuciya Hameed ya yi yace
"To yanzu yaushe tace zata nemeka?"
"Tace dai na bata lokaci tayi tunani zata nemeni."
"Allah yasa muji alkairi."
"Ameen d'an uwana."
"To yanzu Habeeb sai mu fara shiri ko?"
"Eh inasan ma na fara bincika gidan haya."
"Gidan haya?"
"Eh mana"
"Taya zaka zauna gidan haya, bayan muna da gida, dan haka gidan nan zamu gyara ka zauna babu gidan hayar da zaka kama."Kallon shi ya yi yace
"Kai fa idan ka tashi aure ina zaka zauna?"
Murmushi ya yi yace mashi
"Waya ce maka zanyi aure yanzu, kai dai da kake da niyar yi gaya nan sai ka zauna ni ko zanyi aure ba yanzu ba."Dariya Habeeb ya yi yace
"Kabari idan muka haifa d'iya nida Nafeesah na baka ka aura."Duka ya kai mashi, gocewa ya yi yana dariyar.
Wayarta taji tana k'ara, kafin ta d'auka har ta tsinke, agogo ta kalla ganin sha biyu saura yasa ta tashi da sauri ta nufi toilet dan tayi wanka, fitowa tayi tana goge jikinta da towel, kwankwasa mata akayi.
"Shigo."
Abinda tace kenan tana shafa mai a jikinta, shigowa akayi da sallama, juyawa tayi tana magana.
"Falmata lafiya?""Lafiya lau madam dama Mummy ce tace tana san ganinki."
Gabanta ne ya fad'i jin ance Mummy na nemanta.
"Okay kice mata gani nan zuwa, wanka na fito bari na shirya."
Juyawa tayi ta fita dan isar da sakon Nafeesah, tana gama shafa mai ta feshe jikinta da turaruka. Wardrobe ta bud'e k'ananan kaya ta d'auko riga da wando ta saka jikinta ta feshe da turaren nebras Alishq. Veil ta d'auka ta yane kanta, slippers ta saka ta bar d'akin, babban parlor ta iske Mummy zaune tana shan fruit, sallama tayi ta shiga, bata amsa ba washe baki tayi tana fad'in
"Auta na jiki shiru shine nace a kiraki."Zama tayi tare da fad'in
"Kinsan weekend shiyasa ban tashi da wuri ba."Plate ta d'auka ta zuba abinci, tana ci suna fira cikin shak'uwa.
"Dama albishir zan maki."
Spoon d'in dake hannunta ta ajiye tare da kallon Mummy.
"Albishir d'in mi?"
"Cikin week d'innan yan uwanki zasu zo."Ba k'aramin dad'i taji ba jin ance su Ruk'ayya da Zainab zasu zo.
"Mummy ya kamata Zainab suje saudiya a duba ta akan rashin haihuwar nan da ba tayi."Girgiza kai Mummy tayi tace
"Ni kaina abun na damuna, gashi Ruk'ayya na da wani cikin, kuma maganar zuwa saudiya ai sai dai ayi hak'uri saboda tafiyar nan da sukayi su kaje America ta ga wani kwararren likita ya tabbatar mata da ba zata haihu ba."Cikin jimami Mummy ke maganar, dafa ta Nafeesah tayi tace
"Mummmy mu cigaba da adua In Shaa Allah itama idan tana da rabon ganin jininta zata gani.""Nafeesah kenan ana gaya maki bata haihuwa kina wata magana."
Murmushi tayi tace
"Mummy ai komai na Allah ne ida Allah yaso ta da haihuwa sai ki ga ta haihu a lokacin da muka fitar da rai, kawai abinda zamuyi mata a yanzu shine adu'a.""Gaskiya ne maganarki Nafeesa, a kullum ina alfahari dake da kika zama d'iyata mai tarin ilimi da hangen nesa."
Dariya Nafeesa tayi ta cigaba da cin abincita, tana ci suna fira, sai da ta gama cin abinci tasa aka kwashe kayan.
Zama Mummy ta gyara tace
"Auta inasan magana dake."Gaba d'aya hankalinta ta mik'a ma Mummy dan jin mi zata ce mata.
"Auta yakamata a yanzu ki fitar da mijin da zaki aura final year kike kuma second semester ya kamata ace a yanzu kin fitar da wani a matsayin miji."
Shiru Nafeesah tayi kamar ba da ita Mummy ke magana ba, wasa take yi da ya tsunta
"Nafeesah dake nake, na fitar maki da wani kince baki so, to ina jiran zab'inki kinsan ba zan saka maki ido ba ina kallonki ba tare da kinyi aure ba."K'asa ta k'arayi da kanta tace
"Mummy ina da wanda nake so."Fa'arta Mummy ta fad'ad'a tana fad'in
"To shine kika kasa gaya man Auta ? Waye shi? Waye baban shi a garin nan?"Gabanta ne ya fad'in jin abinda Mummy take fad'a.
"Anya Mummy zata yarda da zab'i na?""Kinyi shiru Auta ina jinki kodai kunyata kike."
"Mummy iyayenshi ba wasu bane ba."Shiru mummy tayi jin abinda Nafeesah ke fad'a.
"Naji iyayenshi ba wasu bane ba amma ai shi wani ne waye shi?""Mummy sunan shi Habeeb, iyayenshi yan marad'i ne zama ya kawosu garin nan kuma duk Allah ya masu rasuwa sakamakon had'arin mota."
"Baki bani amsar tambayar da na maki ba waye shi?"
"Mummy ba wani ba ne ba talaka ne yana da diploma yana teaching a wata private school."Tun Nafeesah bata ida magana ba taji saukar marin da sai da ta dinga ganin stars stars
"Nafeesah Kinsan mi kike fad'a, talaka zaki kawo man cikin gida, ni zaki kalla kice ma zaki auri malamin makaranta, wallahi baki isa ba da ki auri talaka gara ki zauna ba aure."
Dafe kuncinta tayi tana kuka, juyawa tayi ta koma d'aki da gudu tana kuka mai tsuma rai. Wayarta mummy ta jawo, yaranta ta kira ta had'a conference call suna d'auka ta fad'a masu duk abinda ke faruwa, ashar Ruk'ayya ta watso, Zainab kuwa kasa magana tayi. Ruk'ayya ce tace.
"Mummy ki saurare mu gobe muna nan zuwa."Wayar Mummy ta ajiye tare da buga uban tagumi.
"Ko zan rasa komai nawa bazan tab'a bari ki auri talaka ba Nafeesah."
Haka ta dinga sabbatu ita kad'ai cikin parlour.Don't forget to vote and comments. Thank y'all for the love and support
RIJF MOTHER 🙏🏼
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Mystery / ThrillerLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...