MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA D'AYA
Shiri sosai Habeeb da Hameed keyi an gyara gida kamar bashi ba 2 bedroom sai parlour sai kitchen sai d'an tsakar gida.
"Hameed yanzu Ina zaka koma da zama?"
"Karka damu d'an uwana ana gama bikinku zanyi tafiya kuma zan dad'e ban dawo ba."
"Ina zakaje?"
"Idan lokaci ya yi zan gaya maka."B'angaren Nafeesah ma shiri take gadan gadan, ita kad'ai ke hidimar bikinta dan yanzu in da take Mummy bata kallo bare ta saka ran zata mata magana, haka kuma idan ta gaisheta sai ta gadama take amsawa, ita kuma abin bai damunta dan gani take komai zai wuce nan gaba kad'an.
Kwance take kan gado tana waya, murmshi kawai take yi kamar yana ganinta.
"Habibi anyi posting d'ina a nan garin na NYSC."
"Dagaske kike matata?"
"Eh Habibi."
"Amma ya akayi aka ajiye ki nan."Murmushin dake kan fuskanta ta fad'ad'a.
"Nayi relocating ne saboda auren da zamuyi kaga ba zaka ji dad'i ba na tafi wani wuri na barka."Ajiyar zuciya ya yi kamar yana ganinta.
"Amma naji dad'i sosai Matata."Haka dai suka cigaba da firansu cikin so da k'aunar juna.
Malam Ali ne zaune cikin parlour bak'i yana jiran zuwan Mummy, shigowa tayi cikin parlour fuskar ta babu walwala, zama tayi ba tare da ta gaidashi ba, bai damu da rashin gaisuwar ta ba dan yasan abinda yafi haka ma zatayi. Zama ya gyara tare da fad'in.
"Nazo d'aukar Nafeesa ne kin san gobe ake d'aura mata aure, ina san ta koma gidana da an d'aura aure zan kaita gidan mijinta da kaina.""Babu in da zataje, Idan ka d'aura mata auren kazo nan ka d'auke ta amma ba zataje ko ina ba."
Tana gama fad'in haka ta tashi ta barshi nan zaune, murmushi yayi ya mik'e ya bar parlour.
Safiyar Juma'a Malam Ali ya d'aura auren Nafeesah da Habeeb akan sadaki dubu hamsin in da dubban mutane suka shaida d'aurin auren, daka ga ango kasan yana cikin farin ciki.
B'angaren Nafeesah kuwa tun da ta samu sanawar an d'aura auren ta take kuka, sai a yanzu take ganin butulcin da tayi ma mahaifiyarta, kuka take sosai kamar ranta zai fita. D'akin aka kwankwasa, cikin dasashiyar murya tace
"Shigo."Falmata ce ta shigo.
"Anty dama Kawu Ali ne yazo yace ki fito."Gabanta ne ya yanke ya fad'i jin ance Kawu Ali na nemanta. Tashi tayi jiki sanyaye ta d'auki mayafi tayi hanyar fita, parlour ta iske shi zaune, shiga tayi ta zauna tare da gaidashi, amsawa yayi yana fad'in.
"Duk an kwashe kayanki ko?"D'aga mashi kai tayi.
"Je kiyi sallama da mahaifiyarki."
Tashi tayi jiki ba kwari ta nufi d'akin Mummy, tana shiga ta isketa kwance, da gudu ta fad'a jikinta tana kuka. Ture ta Mummy tayi daga jikinta.
"Kiyi hak'uri Mummy ki yafe man, nasan ban kyauta ba amma dan Allah kiyi hak'uri ki yafeman ki daina fushi dani, idan kina fushi dani Allah ma zai yi fushi dani, ki daure ki sama aure na Albarka ko sau d'aya."
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Bí ẩn / Giật gânLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...