MARAICIN 'YA MACE
Rubutawa
Phirdaucee JeebohNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA TARA
Dakyar yake jan k'afafuwan shi, d'akin shi ya shiga yana shiga ya fad'a bisa gado, tare da sakin kuka sai kace k'aramin yaro. Ba abinda ta mashi ya sa shi kuka ba dan ya cancanci ta mashi fiye da haka, tsananin soyayyarta ne da ta ke neman tarwatsa mashi zuciya.
D'akinta ta shiga, tana shiga ta banko k'ofa k'asa ta zauna ta saka sabon kuka, sai da tayi mai isar ta kana ta tashi ta shiga toilet, wanke fuskar ta tayi ta fito.
Zaune take tana nazarin d'anta wanda gaba d'aya ya fita hayyacin shi, ta kasa gane miye matsalar shi.
"Muhmud wai ba zaka gaya man miye damuwar ka ba, kana da wadda zaka gayama damuwarka sama da ni?"Kanshi ya girgiza ba tare da ya d'ago ba.
"Ina jinka ka fad'a man mike damunka ko da Allah yasa ina da maganin damuwarka."Rinannun idanuwanshi ya d'ago tare da kai duban shi gare ta.
"Mummy kiyi hak'uri ki dai tayani da adua."Yana fad'in haka ya tashi ya bar parlor, dan bai san ta tursasashi dole ya fad'a mata abin da ke damun shi. Tagumi tayi tana tunanin abinda ke damun d'anta amma iya tunaninta ta gaza gano dalilin damuwar shi.
Zaune take farfajiyan makarantar ta tsurama takardun hannunta ido kamar mai nazarinsu, a zahiri kuwa hankalinta baya tare da ita. Ta kai minti biyar tana mata magana amma bata ji ba, dafa ta tayi tare da kiran sunanta, fuskanta ta d'ago ta kai dubanta gare ta.
"Lubabatu ashe kin k'araso."Wadda aka kira da Lubabatu ta d'aure fuska tare da samun wuri ta zauna.
"Yanzu Husna na kai minti biyar ina maki magana amma hankalinki bai tare da ke, tunanin mi kike haka,"Murmushi tayi tare da share hawayen da suka gangaro mata.
"Ni ba kuka na tambayeki ba, idan kuma ba zaki gayaman ba ki barshi."Kallonta tayi tana fad'in
"Ko baki tambayeni ba zan gaya maki, dan kinsan babu abinda nake b'oye maki."
"Hakane ina sauraronki."
"Loubah kinsan duk irin rayuwar da nake yi gidan sister mamana from day one babu abinda baki sani ba."D'aga kanta tayi sama alaman tasani.
"Jiya Ya Muhmud yazo man da magana wai yana sona."
"Yana sanki?"
Ta ambata tare da zaro ido."Eh yana sona "
"Mi kika ce mashi?"
"Nace mashi bana sanshi na gaggaya mashi magana, ni wallahi ban san zan iya gaya mashi magana ba sai jiya."Tsura mata ido tayi har ta kai k'arshen maganar ta.
"Kina da hankali kuwa? Akanmi zaki gaya mashi magana, koda baki sanshi bai kamata ki mashi rashin kunya ba duk da irin azabtar dake da ya yi amma ko ba komai yayanki ne ya cancanci ki bashi girma a matsayinshi na yayanki."
"Loubah Ina tsoron Muhmud Ina gudun yayi amfani da soyayyar da yake man ya cuta man dan muhmud bashi da kirki ko kad'an wallahi.""Ba zai tab'a cutar dake ba a yanda kika ban labarin Muhmud ya kamu da sanki wanda shi kanshi bai san ya kamu da sanki ba sai daga baya, yanzu shawara why not mu kira Ya Moh mu fad'a mashi mike faruwa."
"Ah ah Loubah ba zamu fad'ama Ya Moh ba cz nama Ya Moh alk'awarin ba zan kula kowa ba sai na gama karatu."
"Kina nufin bai san da King Naufal ba?"
"Eh bai san dashi ba."Dafe kanta Loubah tayi tare da sakin guntun tsaki.
"Nikam kai na ya d'aure ban san mizan ce ba."
"Yanzu miye abinyi?"
"Adua kawai zamu cigaba dayi har Allah ya dawo da Ya Moh lafiya."Daga nan babu wadda ta sake magana. Shiru su kayi na kusan minti goma, Loubah ce ta katse shirun tare da kallon agogon hannunta.
"Mu wuce gida tun da mun gama lectures yau da wuri."Kafin tayi magana Naufal ya k'araso wurin yana dariya tare da sallama. Sallama suka amsa mashi, duban shi ya kai wurin Husna ido ya tsura mata kamar mai karanta wani abu juyawa yayi in da Loubah ke zaune yana magana
"Madam mike damun mamata?"
"Mi kagani?"
"Baki ga yanayinta ba."
"Babu fa abinda ke damuna."
Cewar Husna. Tsura mata ido ya yi tare da girgiza kai.
"Baby akwai abinda kike b'oye man well ba zan matsa maki ba, ran da kika ga ya dace zaki fad'aman."Dariya tayi
"King babu fa abinda ke damuna trust me."Tab'e baki ya yi ya d'auki hand bag d'inta idan kun gama mu tafi.
"Yanzu kai baka jin kunyar rik'e handbag?"
Cewar Loubah tana dariya.
"Miye ai bun mutum dan ya rike ma matar shi jaka?"
"Babu fa ranka ya dad'e wasa nake."Tafe suke suna fira har suka ajiye Loubah gida, bankwana su kayi ya d'auki hanyar gidan su Husna.
"Baby."
Cikin wata irin murya ya kira sunanta. Bai jira ta amsa ba ya cigaba da magana.
"Yakamata yanzu gidanku a san dani saboda iyayena sun matsa man akan lallai sai na fito da mata."
"Shiru tayi ba tare da tayi magana ba.
"Kinyi shiru."
"Kana ganin baiyi wuri ba?"
"Wani irin wuri Husna?, sai dai idan har ba sona kike ba."Dasauri ta kai dubanta gare shi tare da girgiza mashi kai.
"Bai kamata kace haka ba, kafi kowa sanin ina sanka."
"In dai dagaske kina sona ya kamata ki bari gidanku a san dani."
"Shikenan ka k'araman lokaci lokacin dan Ya Moh ya kusa dawowa kaga komai zai zo da sauki."Shiru ya yi bai ce komai ba dan har ga Allah yaso yan gidansu suje mashi neman aurenta cikin yan kwanakin nan amma babu yanda ya iya dole ya lallab'ata tun da yana santa, daga nan babu wanda ya k'ara cewa komai har ya k'araso gate d'in gidansu, fita tayi daga motan tare da mashi bankwana ta shiga cikin haraban gidan, dan yanzu har bakin gate yake kaita.
A haraban gidan taci karo dashi zai fita, yana ganinta ya washe mata baki, d'aure fuska tayi kamar bata tab'a dariya ba. K'arasawa ya yi wurinta.
"Har kin dawo?"
Rab'ashi tayi zata wuce, hannunta ya rik'o fizgewa tayi tare da wurga mashi harara.
"Kada ka k'ara rik'e man hannu."
"Husna miyasa baki da tausayi miyasa baki da imani baki san halin da kike jefani ba?"Dariya tayi sai da hak'oranta suka fito.
"Ya Muhmud ashe kasan tausayi? Wallahi ko zaka mutu bazan tab'a sanka ba."Duk abinda suke Mummy na jinsu ba tare da sun sani ba. Muryanta suka jiyo cikin fad'a
"Kaban kunya Muhmud, saboda yarinyar nan duk ka fita hayyacinka? To bari kaji in gaya maka wallahi ba zaka tab'a auren taba ba zan tab'a had'a zuri'a da dangin matalauta ba."
Mummy ce ke magana cikin b'acin rai."Ke kuma dan ubanki har kina da bakin da zakice baki sanshi ko da yake kin taimaki kanki dan ba zan bari ayi auren nan ba."
"Mummy wallahi sai na aure idan kin ga ban auri Husna ba mutuwa nayi."
Saukar marin da yaji ne ya sa ya had'iye sauran maganar shi.
"Dan ubanka ni zaka gayama zaka aure ta? To ka aureta mugani."
"Ko da zaki kasheni wallahi ba zan janye k'udiri na ba sai na aure ta kuma idan kika ce zaki hana auren nan wallahi sai na kashe kaina."Yana fad'in haka ya bar wurin yana kuka, kan husna tayi da bugu sai da ta tabbata da tayi laushi kana ta kyaleta, dakyar Husna ta iya jan k'afafuwanta ta wuce d'akinta.
RIJF MOTHER 🙏🏼
YOU ARE READING
MARAICIN 'YA MACE
Misteri / ThrillerLabari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye...