BABI NA GOMA

2.4K 288 16
                                    

MARAICIN 'YA MACE

               Rubutawa
                     Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

Innalillahi wa'inna ilaihir raj'un it's exactly 1year since u left us😭 May jannatul Firdausi be ur final Abode🙏🏼 ur Auta loves u so much Maama♥️ I cried endlessly when you died but I promise that I won't tears mar the smiles that you've given me when you were alive. I miss you Maama. By Allah we miss you every second of every day. It's really cold out here Maama💕 buh ur babies will stay strong 💪🏻 just like u taught us, with a heavy heart full of hope I know u're in a better place In shaa Allah and I can't wait to be reunited with you in Jannah in shaa Allah 😇 we missed you so much 💔

BABI NA GOMA

    Da sallama ta shiga gida, zaune ta iske Mummy tana latsa waya, kusa da Mummy ta zauna tana fad'in
"Wash nagaji."

Kanta Mummy ta shafa tana murmushi tace
"Sannu Auta, ai kinga abinda nake maki gudu, ki bari driver ya kai ki ko kuma ki dinga driving da kanki amma kin ce ke dole bus zaki dinga hawa, yanzu waya sha wuya, da gatanki da komai ki dinga mai da kanki d'aya da talakawa."

Jin maganar Mummy ba mai k'arewa bace ba tace
"Mummy bari na shiga d'aki nayi wanka nayi sallah, nazo naci abinci.
Bata jira mi Mummy zata ce ba ta bar parlour'n.

Tana shiga d'aki ta fad'a kan gado, suffar mutumin nan yake mata yawo cikin ido, dasauri ta mik'e ta nufi toilet jin ana kiran sallah magrib, shawa ta sakar ma kanta ta dad'e tana wanka kamar wadda zata canja fata, tana gamawa ta d'aura alwalla, tana fitowa ta kabbara sallah ko da ta sallame bata tashi akan abin sallah ba sai da tayi sallar isha.

Tana idar da sallah ta nufi dressing mirror shafe jikinta tayi da man makari tana gamawa ta feshe jikin ta da turaruka masu tsada, wardrobe ta nufa ta zaro rigan bacci doguwar riga iyakar ta gwiwa sakawa tayi ta kwashi wayoyinta ta nufi parlour.

Tana shiga parlour daining ta wuce, warmers ta bud'e ganin tuwon shinkafa miyar agusi yasa ta saki murmushi.
"Dama nasan yau zakiyi farin ciki, shiyasa yau nace ai maki favorite food dinki, kinsan farin cikin ki shine nawa auta ta."
Mummy ce ke magana cike da k'aunar d'iyarta

Juyowa tayi da murmushi ta rungume Mummy tace.
"Nagode sosai Mummy na Allah ya bani ikon faranta maki yanda kike faranta man."

Dariya Mummy tayi tana k'arajin k'aunar Nafeesah a ranta, yarinyar da tafi k'auna sama da sauran yaranta, dan ma halinta d'aya da ta tsana, idan ta ga tana shigema talaka.

Zama tayi ta fara cin abincinta cikin kwanciyar hankali tana tsakar cin abinci taji muryan Mummy na mata magana.
"Auta ina san magana dake."

Hannunta ta cire daga cikin abinci ta nufi kitchen ta wanke hannunta, dawowa tayi in da mummy ke zaune ta zauna tace.
"Mummy ina jinki."
"Nafeesah kinsan ni na haifeki ko? Kinsan duk cikin yarana babu wanda nake so irin ki, Nafeesah ki daure ki fitar dani kunya nasan zaki iya kuma nasan ke kad'ai zaki man wannan alfarman, kuma yanzu kika gama cewa Allah ya baki iko faranta man, to yanzu gani nazo neman alfarma ki taimaka ki amsa man duk abinda zan gaya maki."

A k'agare take taji mi Mummy zata gaya mata, kallon Mummy tayi tace
"Mummy ban fahimci abinda kike san fad'a ba ya kamata ki fad'aman abinda kike so kefa kika haifeni ba sai kin rok'eni ba kawai ki fad'i abinda kike so Mummy."

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now