BABI NA SHA HUD'U

1.8K 188 9
                                    

MARAICIN 'YA MACE

               Rubutawa
                     Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHA HUD'U

Tsaye yake ya k'ura ma gate d'in ido, shi kad'ai yasan tunanin da yake yi. Agogon dake d'aure ga tsintsiyar hannunshi ya kalla, ganin ya b'ata lokaci sosai yasa ya k'arasa bakin gate d'in cike da fad'uwar gaba.
Kwankwasa gate d'in ya keyi cikin kwanciyar hankali , maigadi ne ya lek'o ganin fuskar da ya saba gani ce ya fito yana washe baki, dan baiyi mamakin ganinshi ba dan kusan kullum sai yazo.
"Baba kana lafiya?"
Ya katse shi tare da tambayarshi.
"Lafiya lau yaro, yau dai burin ka ya ciki dan yar Aljanna ta dawo yau, bari na shiga na fad'a mata."
Bai jira mi Habeeb zai fad'a mashi ba ya sa kai ya nufi cikin gida. Hannu Habeeb ya d'aga yana ma Allah godiya da ya fara cika mashi burinshi, sai kuma fatan samun nasara ta amince dashi.

Yana shiga cikin gidan hanyar da zata sadaka da parlour ya had'u da d'aya daga cikin masu aikin gidan.
"Yauwa Falmata da Allah shiga ciki ki cema yar aljanna tayi bak'o."
Amsawa tayi da.
"To"
Ta nufi cikin gidan, d'akin Nafeesah ta nufa, sallama tayi tare da neman izinin shiga, jin ba'a karb'a mata ba yasa ta kutsa kai cikin d'akin, kwance ta tarar da ita da alamu bacci ta keyi, juyawa tayi zata bar d'akin dan ba zata iya tada ta ba tana bacci. Juyawa tayi zata bar d'akin taji muryarta.
"Falmata Lafiya?"
Juyowa tayi tace
"Ranki ya dad'e dama Baba maigadi ne yace kina da bak'o."
"Bak'o?"
Ta tambaya cikin mamaki, dan ita ba tayi da wani zaizo wajenta ba.
"Ki cema maigadi ya kaishi parlour bak'i, ki kai mashi ruwa gani nan zuwa."
"An gama ranki ya dad'e."
Juyawa tayi ta bar d'akin, wajen maigadi ta nufa ta fad'a mashi abinda Nafeesah ta fad'a ta koma cikin gida dan kai ma bak'on lemu.

Tashi tayi cikin mamaki tana tunanin waye yasan ta dawo har yazo nemanta, ita a iya tunaninta batasan wani zai zo nemanta ba, bama mazan take kulawa ba bare a zo nemanta, rashin sanin gamsashiyar amsa yasa ta saka takalminta ta d'auki gyalenta ta yafa ta bar d'akinta.
Wajen mai gadi ta nufa, sallama ta mashi da sauri ya amsa sallamar tare da tashi tsaye.
"Baba maigadi waye yazo nemana?"
"Yar aljanna wallahi wani mutum ne ina ga masu neman taimako ne tun ranan da kikayi tafiya yake zuwa kullum sai yazo har tausayi yake bani, gashi nima takaina nake yi bare na taimaka mashi."
Murmushi tayi tace
"An kaishi parlor bak'i?"
"Eh An kaishi."
Juyawa tayi ta nufi d'akin, ba tayi mamaki ba jin maigadi yace kamar masu neman taimakone dan sun saba zuwa dan ma Mummy bata bari idan ta gani fad'a take yi.

Parlour bak'i ta nufa sallama tayi fuskar ta d'auke da murmsushi wanda ya riga da ya zama jikinta dan ba lallai bane ba kaga Nafeesah ba tare da murmushi a kan kyakyawar fuskar ta ba. Baki ya saki yana kallonta ya kasa furta ko kalma d'aya.
"Malam Lafiya baka amsa sallama?"
Ajiyar zuciya ya yi tare da dawowa daga dogon tunanin da ya tafi, wanda shi kad'ai yasan irin farin cikin da ya shiga sakamakon ganin da yayi mata yau.
"Kiyi hak'uri bansan kin shigo bane ba."
Zama tayi ba tare da tace mashi komai ba, tun da ta zauna ta k'ura mashi ido, du yanda akayi ta sanshi amma ta kasa tuna inda ta san wannan fuskar.

"Da alamun baki gane ni ba."
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa
"Gaskia ban gane ka ba amma nasan na tab'a ganin ka."
"Sunana Habeeb."
Dasauri ta d'ago ta sake kallonshi tabbas shine, shine mutumin da ya taimaketa a school, amma taya ta kasa tunashi."
"Ina fatan yanzu kin ganeni."
Maganar shi taji cikin tsakiyar kanta, ajiyar zuciya ta saki tare da fad'in
"Na ganeka dan Allah kayi hak'uri nasan dai na sanka amma na rasa tuna in da na sanka kasan abubuwan dayawa."
"Karki damu manya ai basu laifi."
Murmshi tayi tare da k'ara sadda kanta k'asa tana wasa da yatsunta.
"Maigadi yace man kana ta zuwa baka sameni ba, dan Allah kayi hak'uri."
"Haba ba komai ai matsayinki ya kai na a zo shiyasa nake zuwa kuma gashi yau Allah ya had'amu.

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now