BABI NA SHA BIYAR

1.7K 173 11
                                    

MARAICIN 'YA MACE

Rubutawa
Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHA BIYAR

      Da gudu ya fad'a d'akinsu, yana shiga ya fad'a a kan katifa da sauri Hameed ya d'ago shi yana tambayarshi lafiya. D'agowa ya yi yana dariya, ganin yana dariya yasa Hameed ajiyar zuciya.
"Amma kasan ka d'agaman hankali ko?"

Kafad'arshi ya daka yace
"Miye abun tsoro d'an uwana?"
"Taya bazan tsorata ba? Dole in tsorata dan bansan halin da zaka shiga ba."

Dariya ya yi sosai yace
"D'an uwana nasamu karb'uwa fa wajen Nafeesah."
Ihu Hameed yayi yace
"Alhamdulillah"

Hannunshi ya d'aga sama yana godema Allah, a yanda d'an uwanshi ya samu karb'uwa ko bakomai yasan yasamu kwanciyar hankali, ya daina mashi barazanar mutuwa.
"Dan uwana nayi farin cikin samu karb'uwa da kayi wajen Nafeesah."
Zama ya gyara yace
"Bari kaji yanda mukayi da ita"
Tun daga farkon yanda sukayi da ita har k'arshe ya gayama Hameed bai rage mashi komai ba.

Ajiyar zuciya Hameed ya yi bayan ya gama gaya mashi yanda sukayi.
"Yanzu kana ganin bakayi saurin gaya mata ko waye kai ba?"
Tambayar da Hameed ya jefo mashi kenan.

Muskutawa ya yi ya gyara zama.
"Banyi sauri ba d'an uwana, inasan tasan koni waye tun daga farko, inasan tasan ni talakane banda komai sai wadatar zuci, inasan na gina soyayyata akan gaskiya ne."

Kafad'arshi Hameed ya dafa yace
"Tabbas hakane, gara tasan waye tun farko tasan da wa zata zauna tasan baka da komai sai rufin asiri."

Soyayya da shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin Habeeb da Nafeesah, suna soyayyar su cikin tsafta, kullum cikin faranta ran juna suke, duk dare sai yazo wajenta, idan kuma ya koma gida haka zai kirata a waya su dasa wata sabuwar fira.

Kwance take tana waya, gaba d'aya hankalinta baya tare da ita yana kan wayar da take yi. Ta kai minti goma tsaye bisa kanta, ganin bata san da ita ba yasa ta tab'ata juyowa tayi ganin Mummy ba k'aramin mamaki ya bata ba, kashe wayar tayi ta tashi tsaye, rungume Mummy tayi cikin so da k'auna.
"Mummy yaushe kika dawo, taya ma zaki dawo baki fad'aman ba."

Dariya Mummy tayi tace
"Yaza'ayi kisan na dawo ki nan kina waya, kuma dama nace bazan gaya maki ba surprising d'inku zanyi."

Baki ta zumb'ure tace
"Nidai Mummy gaskia banji dad'i ba akanmi zaki kasa fad'aman yau zaki dawo."
"To yi hak'uri Auta nah."

"Auta nah dawa kike waya, kodai an man suruki ban sani ba?"

Jin maganar Mummy cikin kunnenta ba k'aramin tada mata hankali ya yi ba, dan tasan idan Mummy tasan waye take soyayya dashi tasan sai ranta ya b'aci.

"Ya zama dole in b'oye maki Mummy ba yanzu zaki san waye nake tare dashi ba sai nan ga zaki san waye."
A zuciya take wannan maganar, murmushi tayi tana fad'in.
"Ah ah Mummy bafa soyayya nake ba, course mate d'inane, kin san ma ba saurayi ne dani ba."

Kallonta Mummy tayi tsab ta girgiza kai.
"K'arya bata kamace ki ba, dan baki saba da yinta ba."

Ganin Mummy zata gano ta yasa ta ja hannunta sukabar d'akin.

Tun daga wannan rana bata k'ara barin Habeeb yazo gidansu ba, sai dai ya sameta a school, duk yanda ya yi ta gaya mashi dalili, sai tace mashi ba komai gara su dinga had'uwa a school zai fi masu sauk'i.

A haka har sukayi shekara tare suna soyayya ba tare da Mummy ta sani ba. Kwance take tana barci, jin wayarta na ringing yasa ta tashi, tsoki tayi ta nufi in da wayar ke aje, ganin Mon Amor a screen d'inta yasa ta saki dariya, d'auka tayi ta kanga a kunne.
"Hello Habibi"

D'aya b'an garen aka amsa da
"Naam Mieheart."
"In wuni?"
"Lafiya lau."
Ya masa cikin sakin fuska.

"Mieheart Ina san ganinki yau inasan muyi magana."
"Amma kasan yau friday kabari sai monday mana."
"Ah ah Nafeesah ina san magana dake kuma a yau nake san muyi magana, saboda maganar nada muhimmanci."

Ajiyar zuciya tayi tace
"Shikenan mu had'u a School a in da muke had'u wa da k'arfe hud'u."
"Shikenan nagode, sai kin ganni."
Wayar ta kashe tana tunanin wace irin magana ce Habeeb bai iya hak'urin sai monday yake so suyi ta yau, rashin samun gamsashiyar amsa yasa ta tashi ta nufi toilet danyin shirin tafiya.

K'arfe uku da rabi (3: 50pm) ta fito cikin shirinta, abaya ce jikinta Black rolling tayi da bak'in gyale, black slippers ta saka na company Aldo, handbag d'inta ta d'auko bak'a ta saka wallet d'inta da wayarta ta fito. D'akin Mummy ta nufa, da sallama ta shiga d'akin, amsawa tayi, shiga tayi cikin d'akin kwance ta tarar da ita tana latsa waya, ganin Nafeesarh ya sa ta mik'e zaune.

"Auta sai ina?"
"Wallahi Mummy zan d'an fita ne na gaji da zaman gida."

Dariya Mummy tayi sosai tace
"Ya kamata kam Auta, ni kaina banasan zaman da kike gida gara ki d'an fita kisha iska."
"Shiyasa zan fita ai Mummy."
"Waye zai kaiki?"
"Mummy da kaina zan tafi."
"Da kanki kamar ya?"
"Eh ni zanyi driving."
Ba k'aramin dad'i Mummy taji ba, jin Nafeesah tace da kanta zata fita.
"Ki duba side drower d'in can akwai kud'i ki d'auka."
"No mummy Ina da kud'i."
"To shikenan Auta Allah ya maido man dake lafiya."

Sallama tayi ma Mummy ta fita, kai tsaye parking space ta wuce, wata farar mota ta nufa k'irar Mercedes-Benz AMG CLS 63, shiga tayi ta ma motar key, wuta ta mata sosai ribas tayi , horn tama mai gadi, da sauri ya wangale mata gate, fita tayi daga cikin haraban gidan.
"A dawo Lafiya Allah ya tsare mamu ke yar aljanna."

Mai gadi ne ke mata Wannan adu'ar, d'aga mashi hannu tayi fuskar nan tata d'auke da murmushi. Bak'ara ta kunna k'ira'ar sudais, bin k'ira'ar ta keyi cikin gwanancewa, a hankali take tuk'in ta cikin gwanancewa.

Sansayar iskan wuri ke kad'ashi, agogon hannunshi ya duba ganin k'arfe hud'u da minti biyar yasa ya zaro wayarshi, kira ya danna, wayar ta fara ringing yaji ringin d'in wayarta a bayanshi. Juyawa ya yi ganinta ya yi tsaye tana washe mashi baki.
"Mutuwar tsaye ya yi ganin irin kyan da tayi."

Takowa ya yi ya k'araso wajenta fuskarshi d'auke da murmushi.
"Tsarki ya tabbata ga mahalincin da ya yi wannan halitta."

Murmushi tayi ta samu wuri ta zauna, k'arasawa ya yi inda take zaune ya zauna. Shiru sukayi na kusan minti biyar, ganin shirun ba zai k'are ba ya fara magana.
"Nasan zakiyi mamakin nace maki inasan nayi magana dake. A gaskia Nafeesah lokaci ya yi da ya kamata na bayyana ma iyayenki kaina a matasayin mijin da zai aure ki, inasan muyi aure cikin shekarar nan."

D'agowa tayi da saurayi ta kalle shi, k'ura mashi ido tayi tana kallonshi, hannun shi ya kad'a mata.
"Ya dai matata? Ko kina ganin nayi saurin bayyana kaina wajen iyayenki? Amma ina ganina banyi sauri ba dan munfi shekara tare."

Ajiyar zuciya tayi tace
"Shikenan kaban lokaci zanyi tunani, in shaa Allah koma miye zakaji daga baya."

"Shikenan Allah yasa muji alkairi."
"Ameen."

Sun d'an tab'a fira kad'an bankwana su kayi, yaja d'an mashin d'inshi, ita kuma ta shiga motarta, ta wuce gida.

Don't forget to vote and comments, thank you All😍

RIJF MOTHER🙏🏼

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now