BABI NA TALATIN DA UKU

327 20 9
                                    

MARAICIN 'YA MACE

Rubutawa
Phirdaucee Jeeboh

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA UKU

Karfe uku daidai ya masu a bakin k'ofan gidan su Moh, hon yayi maigadi ya bud'e gate d'in cinna kan motar shi yayi cikin gidan. Sai da ya samu wuri yayi parking kana Moh ya fito daga cikin motan. Kallon haraban gidan yayi babu abinda ya sauya sai dai yan gyaran da akayi mashi.
"Home sweet home"
Abinda ya furta kenan a k'asan leb'enshi.

Da gudu maigadi ya k'araso yana washe baki.
"Ranka ya dad'e sannu da zuwa."

Kallon shi Moh yayi tare da k'ara fad'ad'a fara'anshi.
"Yauwa baba, Ina fatan kuna na nan Lafiya."

Murmushi yayi yana fad'in
"Lafiya lau Alhamdulillah."

"Baba ka kai driver nan d'akin ka kasa a kawo mashi abinci idan ya gama ya huta kaman magana."
"In shaa Allah haka za'ayi."

Da sallama ya shiga kutsa kanshi yayi cikin parlor ganin babu Wanda ya amsa mashi ya samu wuri ya zauna, mai aiki ce tazo wuce wa ta ganshi har ta wuce ta dawo dan bata sanshi na amma tana ganin hoton shi a parlor.
"Ranka ya dad'e ina wuni?"
"Lafiya lau."
"Ina masu gidan?"
"Hajiya ta tafi unguwa, uwar d'akina kuma ta tafi makaranta dan ta fara exams."
Murmushi yayi da yaji an ambaci Husna.

"Yallabai mi za'a kawo maka?"
Muryanta ya juyo tana tambayanshi.
"Kawo man ruwa."

Dasauri taje ta kawo mashi ruwa, karb'a yayi tare da mata godia.
A cikin ranta take yaba halayen Moh, duk da yau ta fara ganin shi amma ta lura yana da halaye masu kyau, kuma tana jin yanda Husna ke yawan ambaton shi, duk yawancin maganarta sai ta ambaci Moh.

Da sallama aka shigo parlor, ganin baba mai gadi ya sa ya mik'e tsaye.
"Ranka ya dad'e ya gama, kuma ina zan kai kayan naka?"
"Nasan d'akina yayi k'ura a kai man su d'akin Husna."
Yana fad'in haka ya saka Kai ya fita daga gidan.
A farfajiyan gidan suka had'u da driver da ya kawo shi.
"Malam Ali sarkin surutu har an gama?"
Dariya yayi yana fad'in.
"Ranka ya dad'e na gama"
Gyada Kai yayi ya fito da kud'i daga cikin aljihun shi bandir guda ne na dubu d'aya ya mik'a mashi. Amsa Malam Ali yayi ya fashe da kuka yanda ka faranta mani Allah ya faranta maka Allah yasa ka gama da duniya Lafiya ya kare ka daga sharin mutum da aljan.
Dafa kafad'anshi Moh yayi yana dariya.
"Karka damu Malam Ali Ai kai yanzu ka zama abokina."
Dariya gaba d'aya su kayi.
"Yakamata kazo ka kama hanya kada dare yayi."
"Yanzu kuwa d'an aljanna."

Raka shi yayi har bakin mota sai da suka sake bankwana kana ya shiga mota.
"Idan ka isa ka kirani."
"In shaa Allah."
Haka sukayi bankwana Malam Ali yaja mota ya fita.
Juyowa yayi kan maigadi.
"Baba maigadi idan masu gidan sun dawo bansan a fad'a masu na dawo, so nake kawai su ganni."
"In shaa Allah yanda kace haka za'ayi."

Murmushi yayi ya fita daga farfajiyan gidan. Tafiya yayi mai d'an nisa kana ya zaro wayan shi ya kira. D'auka akayi.
"Kazo wurin gidan Alh Abubakar ina nan tsaye."

Yana fad'in haka ya kashe wayanshi. Ba'a jima ba wata mota ta tsaya gabanshi, bud'e gaban motan yayi ya shiga.
Yana shiga suka rungume juna tare da fara'a.
"Mutanen America, kaga kyan da kayi?"
Fara'anshi ya fad'ad'a ba tare da yayi magana ba.
"Ina zamuje?"
"Gidan ka mana."

Hanyar gidan shi suka d'auka suna tafe suna fira har suka iso bakin gate, Parkin su kayi waje suka fito suka shiga cikin gidan, wuri ya samu parlor ya zauna tare da fadin
"Wash"
Ruwa mai sanyi ya kawo mashi ya ajiye mashi gaban shi.
"Kaman kasan abinda nake so kenan yanzu."
"Bari in mana order abinci."
"Haba ka barshi ni dai ba wata yunwa nake ji ba."
"Nima ba yunwa nake ji ba dama Saboda Kai ne kawai."

"Ya amanata take?"
"Amanarka lafiya lau."
"Sai dai abubuwa sun cakud'e dan a yanzu tana cikin k'uncin da yafi na da."
"Nasani Saboda Muhmud ya kamu da santa ga kuma tana tare da wani naufal, sanadiyar san da Muhmud ke mata yasa mummy ke gallaza mata."

Da mamaki ya kai duban shi inda Moh yake
"Ya akayi duk kasan wannan?"
"Ya bazan sani ba, ka manta Asmau ce ina nufin husna. Kada kayi mamaki idan na fad'a maka komai akan ta. Ba Kai kad'ai na saka aiki ba har ta maigadin gidanmu yana man aiki kan husna, Tunda na fara jin number Husnah user busy na kasa yarda da irin maganan da yake fada man da course mate d'inta take waya, a nan ne naba maigadi aikin ya binciko man cikin ikon Allah kuwa ya kawo man details d'in Naufal, nayi bincike akan naufal na gane ba mutumin banza bane ba, a da naso in hak'ura da Husna in bata zab'in da take so dan ni nayi kuskure dana kasa fad'a mata tun farko ina santa, sai dai a yanzu Husnah bata da wani miji wanda ya wuce Muhmud."

Da sauri ya kalli Moh.
"Kasan mi kake fad'a kuwa Moh, kasan irin sanda kake ma yarinyar nan taya zaka sadaukar ma wani ita."
"Ni kuwa nasan mi nake fad'a Muhsin, Wallahi zan iya ba Muhmud rayuwata, bama mace ba nasan a da ya tsaneta amma a yanzu daidai yake da ya kashe kanshi akanta saboda irin san da yake mata, A halin da Muhmud yake ciki yanzu nasan ko k'uda ba zai bari ya cutar da husna ba, a yanzu san da yake mata ban mata shi, to akanmi ba zan iya sadaukar ma gudan jini na ba abinda yake so sama dani. Kada ka manta su ka d'ai suka rage mani duniya daga shi sai Mummy tun da mahaifinmu ya rasu suke dawainiya dani miyasa ba zan iya saka mashi ba? Husna bata san ina santa ba dan haka daga yau Wallahi na cire san husna a raina."

Ajiyan zuciya Muhsin yayi
"Tabbas abinda ka fad'a gaskia ne, Amma inda matsalan take Husna bata san Muhmud."
"A wurin mutane take matsala amma a wurina abine mai sauk'i dan kasan zata amince."
"Ya zakayi da Naufal."
"Zai hak'ura idan yaga halin da Muhmud yake ciki."

"Yanzu kai wata zaka nema kenan?"
"Dama Ina da wata ina da Amaal saboda husna yasa nak'i amincewa da soyayyarta."

"Tabbas Muhmud Kai mutum ne Allah ya saka maka da alkairi."
Murmushi yayi
"Muhsin muje ka kaini gida ina san inga family na."

Tashi yayi suka kama hanyar gidansu Muhmud.

RIJF MOTHER🙏🏼

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 15, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MARAICIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now