BABI NA GOMA

322 22 0
                                    

[7/31, 6:40 PM] Mamanhaneef: FEENAT

BY

MMNAHANEEF

2016

26

***Har cikin dakin sa dake soron gidan su yashigo da kamal, daki ne yalwatacce mai dauke da luntsimemiya katifa sai sif madanar kaya dg gefe sai kujeru guda biyu a gefen lokar dake cike da littafai da takardu sai kayan kallo dake jikin bangon da bandakin sa yake haeda firinji a gefen tv sa, dakin kafet ne a malale mai kalar ruwan labulen dake dakin,dakin sai buga kamshi yake kai bakace dakin gwauro bane.

Cikin mutunta juna suka soma tattaunawa tareda hirar su irin ta abota bayan yq gabatar masa da abin sha,suna cikin hira ne kamal yasako masa mganar Maryama wacce ita ce ginshikin data kawo shi, Ismail shuru yayi yama rasa ta inda xai soma ko da wanne ido zai dubi tsabar idon abokin sa kamal yace masa bayason k'anwar sa?duk da dai inyayi hakan baiyi laifi ba to amma hakan da kunya, kuma yasan kamal bazaiji dadi ba,

jin shurun yayi yawa yasa kamal dafa kafadun sa tareda cewa"Dr Ismail me kake tunani haka? murmushin yak'e yayi kan yace"ina dan nazari akan maganar Maryama ne, da farko dai ni bazan ki maryama ba amma wani hanzari ba gudu ba banida kudirin yin aure a yanzu saina kammala karatun danasa a gaba na nutsu tukun sannan zanyi aure, a zahirin gaskiya kamal ina son suren mace mai ilimin addini kamammiya wacce a matsayin karatu bata wuce sakandare ba,

inamai baka hakuri kuma kaima kabawa Maryama hakuri tayi adduar Allah yazaba mafi alkairi, kasan matar mutum kabarin sa,inda rabon aure a tsakanin mu Allah ya tabbatar mana, Hmm kamal ya sauke numfashi yadube shi tareda cewa"shikenan na fahimce ka Allah yazaba mafi Alkairi,yace"Ameen"nan dai suka cigaba da tattauna sukama canja wata hirar,yafuto yakashi ne sukai kacibus da safiyya tana kokarin shigowa sukuma zasu fita, har kasa ta dirkusa tana gaida kamal ya amsa cikin mamaki yadubi ismail yace"eacece wannan? dama har yanzu akwai irin wayannan matan a wannan zamanin? nisaina cemaka baa taba tsugunnawa haka angaisheni ba sai yau a gsky ta birgeni.

murmushi yy kan yace"yar uwata ce sunan ta safiyya ita kebin murtala, akwai irinsu mana ai baa rasa nono a riga,nandai ya rakashi sukai sallama yatafi abinsa.

Acan b'angaren Maryama kuma tun fitar yayan ta takasa zaune takasa tsaye tana fargabar da wacce amsa zaizo mata?Don mafarkin ta baitaba bata xasuyi aure da Ismail ba, don tasan ko kadan bata gaban sa donduk wani feleke tayishi donta birgeshi amma ko a fuska baitaba nunawa yasan tanai ba,da gudu tazura waje donjin dhigowar motar sa,tunkan yagama futowa dg mota ttasoma zabgo masa tambayoyi, maimakon yabaya amsa saiyaji wani mugun haushi ya rifeshi ganin duk ta daga hankalin ta akan Wanda raayin sa baizo dayama da nata ba balle asako da maganar hali ko dabia,

ganin tadamu dajin amsar da Ismail ya bashi yasa yy tunga a kofar dakin sa don yaga alamun har ciki takeso tabishi,cikin tukewa yace"inma zakiyi hankali kisan Mre kike ciki kiyi Ismail Sam bayada raayin auren mace irinki don haka kibarwq Allah zabi,dakin sa yafada game da banko kofar gam! har saida ta tsorata,take tasoma jin wani daci cikin ranta gaban ta na dukan uku uku, wani irin duhu taji yana kewaye ganin ta ga jikin ta yayi mata nauyi jin tana Neman faduwa yasata dafe bango tasilale ta zauna agurin
[7/31, 8:16 PM] Mamanhaneef: 27.                                     ***Akwance take hannun ta rike da wayar ta tana sada zumunta ta hanyar sadarwa ta wtsp don takwana biyu bata leka ba, aikwa ta tarda tarun sakwanni bata saurari hirar grp ba prvt chtt tasoma dubawa tana kuma mayar da amsoshin a hakanne har tazo kan wata bakuwar lamba,bata fiya duba sakon daba tasan me lambar ba, amma ganin anyi mata cikakkiyar sallama gawata hoton wata kyakyawar yarinya akan dp tashiga ta amsa sallamar da cewa"waalaiki salam"nan take taga anturo da wani sakon kmr jiran ta ake,"Nafeesa ya kike ya kikaje gida?Take tasoma zargin ko arukayyace kanwar Ismail donta amshi lambar ta,"lafiya lau naje gida rukayya"ba rukayya bace yayar tace Salma"Anty salma ce ashe?Anty salma ya Affan?"sunan danta na fari."duk lafiya muke Nafeesa,dama na amshi lambar kine gurin Ismail don Mu kara gaisawa don dazu kunya tahana ki sakewa damu kmr wasu surukan ki"murmushi tayi"laah ba haka bane Anty Salma surukai kawai akejin kunya?ai in zumunci yayi karfi haka nan anajin kunyar mutum"laah Inada ja cikin zancen ki Nafesa munadai fatan zumincin ya dore in Allah ya kaddaro wani Al Amari ya gifta tsakanin Ku"Al Amari Anty?"Eh Al Amari koma nace miki Alaka irin ta soyaiya haka,don a zahirin gaskiya ina zargin akwaita tsakanin ki da Ismail,"Dan aljani mai Alamun mamaki dana kunya ta tura mata,"Anty har kinsa naji kunya Anty yanzu banda lokacin ta da kowa ma,kuma ismail yaya nane Anty mutane dayawa na zargin hakan bansan meyasa ba"kun dace shiyasa muke zargin hakan,amma tunda kince hakan zamu fadawa Allah,takara sa da sigar wasa"itama da wasan tace mata"Anty Ku kyalemu pls"Ai ina zamuyi adduar Allah yajefa soyaiya a zukatan Ku balle ma tunda akwai kauna zata rikide takoma soyaiya"Alamun kunya hadeda dariya ta tura mata batace komai ba"Maganar gaskiya munaiwa Ismail kwadayin samun ki Nafeesa Ina fatan bazaki bamu kunya ba"bazan baki kunya ba inhar ba tallan kanwar ki zakiyi wa Ismail ba",wannan furucin yadan bata dariya kuma yasata tagano wayo irinna nafesa da kuma karawa kanta kima da daraja datayi a yanzu,Anty salma takuma jinjina wa sanin yakama tan da nafesa take dashi"Karki damu kanwata ai nasan kanwata tawuce ayi tallan ta saidai a nemi alfarmar ta"murmushi ta tura mata"Anty kiyi mana adduar zabin Allah wannan muke bukata, a halin yanzu kuma adduar samun nasara muke bukata,      ***Nan dai suka cigaba da hira sai wajen karfe goman dare suka rabu yynda kowacce ta ajye wayar ta.                              ***sai bayan ta kwanta ne baccin yaki zuwa tunanin yai mata sallama ta dinga tunanin abubuwan da suke faruwa tsakanin ta da Ismail Wanda yasa ake zargin su da suna soyaiya a boye ne,                                        duk tayi iya tunanin ta bata gano wata alama ta soyaiya a gurin Ismail ba

FEENAT!!! Место, где живут истории. Откройте их для себя