BABI NA 18

281 19 0
                                    

FEENAT!!

BY MMNHANEEF

2016

44.

***ganin wankin hula zai kaishi dare yasa yafuto da mota a cikin daren ya dauko ya kaita wani prvt hospital dake cikin nassarawa nan da nan likitan dake night duty suka shiga aikin su, zarya yake yakasa zaune yakasa tsaye don tashin hankali, bashi yasamu nutsuwa ba saida yaga anfuto da ita ankaita dakin hutu wanda anan likitan ke shaida masa zasu iya tafiya bayan ta huta babu wata matsala bayan ta wuyar da tasha tana bukatar Hutu kwarai d gsky, kiran Assalatun farko suka baro asibitin  don tasamu kilawa yanda ya kamata a gidan ma ba zama yayi ba, yana dawowa dg asibiti ya shiga kicin ya shirya mata nau ikan abincin da likita tabashi shawarar ta dingaji zasu taimaka mata wajen samun kuzari da kara jini dadai sau ransu, kasancewar yasan abubuwan dazai bukata yashiga da kansa ya hada mata Abinci mai rai da lafiya da hakanan yaita kula da ita a yinin ranar, da daddare kuwa? Hajiyansa CE tazo gidan da kanta ta tafi da Nafisa gida don acewar ta tafi samun kulawa sosai.

Satin ta biyu gurin hajiyan sa ta warke kalau da ita har wata yar kiba tayi don kulawa ta musamman hajiya take bata tamkar maiyin jegon gsky. A sati na uku ne takoma gidan ta Cikin koshin lafiya Dr har wani kyau yaga ta karai masa,

Tofa Abangaren Dr komai yadawo normal wanda yaci gaba da more rayuwar sa tareda nunawa matar sa tsabtsar soyaiya itama anata bangaren farin cikin mijin ta shine nata hakanan suka kwashi watanni uku suna cin moriyar kaunar su, a dai dai wannan lokacinne tasoma wani laulayin wanda baikai wancen wahala ba don wannan karan bata amai sai dakaran kwadayi da kasala da zarar ta kwanta sai bacci, wannan ne yaso bakan ta ran Dr don shifa don rayuwa ne duk da yana kawaici saida takai ya furta da bakin sa, tayi kokarin lallamin sa don tasan halin kayan ta amma ina a wannan karon ma saida yayi sanadiyar barewar sa, batare da sanin taba kmr yanda waccen ya kasance.

Hankalin yan uwanta yafara dawowa kan matsalar ta a yayin da tayi bari na uku, suka shiga kokwanto cikin ransu, nan dai ta tabbatar musu da komai yasameta Allah ne ya aiko mata kuma tana adduar Allah ya tsayar mata da na gaba, duk da hakan basuyi sanyaba wajen nema mata magani hatta hajiyan sa haka takawo mata magungunan hausa, Nan dai Dr yatada rigima akan magungunan karshe ma ya sasu ashara tanaji tana kallo batada yanda zatai don ko musu bata taba yarda ya hadasu da Dr ba.

Zaune suke a saman kujerun dake falon su tayi matashi da cinyar sa suna hira wacce rabin hirar tasuce ta maaurata bayan sun natsane ya dagota tareda kiran sunan ta"FEENAT"idon ta lumshe tace"Dr"yaci gaba"wata shawara nakeso muyi, mikewa tayi zaune tana sauraran sa" Me zaihana muje muyi tsarin iyali muhuta da bakar wahalar da kikesha wajen laulayi?Cikin mamakin jin zancen sa ta zaro ido tareda maimaita maganar tasa"tsarin iyali? Dariya maganar tasa tabata wacce batasan sanda ta tuntsire da dariya ba kan tace" Haba Dr na, wacce iriyar magana kakeyi haka? Don kawai ina shan wahalar laulayi sai muyi tsarin iyali sai kace kaina farau? Kuma ma aiba tunkan a haihu ake tsarin iyali ba, sai anyi haihuwa biyu uku wasu ma sama da haka ko kuma masu haihuwa akai akai wanda basa samun taxara, katseta Yy da cewa" bafa canai  bazamu haihu kwata- kwata ba, ganinai da kita samun cikin kina wahala kuma karshe ya zube gwara kin huta kwana biyu in yaso daga baya saimu samu baby kan nanma mahaifar ki ta huta kema, Nidai Dr Sam tsarin iyali baya cikin tsari na Mu hakura kawai naji na yarda duk wahalar da zansha na aminta nasha inhar zan haihun sabida nima bansan wahalar da mahaifiyata tayi kan ta sameni ba,

Ganin Taki Aminta yasa shima ya hakura, amma cikin ransa akwai abubuwan daya dasa,

Hakanan suka cigaba da rayuwa kmr yanda sukeso, Tattali soyaiya kuwa sai abinda Yy gaba ita kanta tana mmkin irin soyaiyar da sukewa junan su, tsaftataciyar soyaiya babu takura balle gundura ko yaushe suna begen junan su tareda faran ta ran junan su.

Suna shekara ta hudu da aure ne Nafisa ta tsinci kanta cikin hali na laulayi wanda zuwa wannan lokaci tuni ta gama karatun ta dake takoma makaran ta harta soma aiki a asibitin koyarwa wanda tasamu dinbin nasara da farin jini sakamakon jajircewar ta da kwarewar ta ta fannin ta,a gefe guda kuma dai dai kun ranaku takan ziyarci kananun asibiti don bada gudun mawarta a game da matsalolin da mata kan fuskata  a matsayin ta na cikakkiyar likitan mata wacce tasan aikin ta kuma take Alfahari dashi.

Wannan karon bata wani laulayi da yanayin data tsinci kanta tasan tanada shigar ciki, koda wasa batayi yunkurin fadawa Dr ba,abinda yabata tsananin mmki hartayi zargi wanda tasata bincike akan mijin ta, tashi daya ta wayi gari babu ciki babu alamun sa cikin jikin ta,  wanda ada tanada tabbacin akwai shigar ciki a jikin ta na satitti ka, a iya tunanin ta batasha komai ba kuma bata shaidawa kowa halin datake ciki ba tasan dai inma akwai cikin to karamine wanda bai wuce sati biyar koma hudu ba, wanda inba itan ba bakowa zaigane alamomin ciki a wannan tsakanin ba,

Wannan dalili ne yasata yiwa mijin ta bincike abinda bata tabai masa ba iya shekarun da suka kwashe tare,  duk iya binciken ta a dakin bataga wani Abu daya shafi abinda take zargi ba, hakanan tagama dube duben ta tagaji tagyara ko ina ranta fes har zuciyar ta ta kwanta da zargin dataso dasa mata na mijin ta,

Harta futa daga dakin nasa kome ta tuna oho?ta koma yafada bandaki tashiga gyaran sa duk wasu turarukan wankan sa da shamfo da sabulai saida ta kwashe su ta gyara musu mazauni haka ma tawul din dake cikin wata lokar ta jikin bango wacce duk nau in adone da aka kayata bandaki dashi,  haka nan tashiga futo da sauran tawul da kananun kayan ciki wanda nan ne mazaunin su, tagama futo dasu kenan taji fadowar Abu kasa, Sam bata kula da kome neneba sai bayan tagama ninke kayan ta maida ta tsugunna ta dauko abinda ya fadin wani kwaline Harta mayar ta rufe lokar kawai saitaji tana son sanin menene, aikuwa ta kuma daukowa tasoma dubawa tana karan ta rubutun dake jikin kwali,

Tunkan tagama gumi yashiga karyo mata hannun ta kuwa tuni ya dauki karkarwa a haka tafuto ta nufi nata dakin hannun ta rike da kwalin.

Kubiyo ni

FEENAT!!! Where stories live. Discover now